Nazari A Kan Noman Lemon Zaki
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari A Kan Noman Lemon Zaki

byAbubakar Abba
2 years ago
Lemon Zaki

Ana noman lemon zaki a dukkanin fadin duniya, sannan kuma ya kasance daya daga cikin kayan lambun da za a iya shukawa a dan karamin waje ko a gidan gona, musamman idan yanayin wajen na da kyau.

Har ila yau, lemon zaki na dauke da sinadarin da ke karawa lafiyar jikin dan Adam lafiya, haka nan ana iya shuka shi a kowane yanayi na kakar noma, musamman daga watan Afirilu zuwa Mayu, har zuwa watan Disamba.

  • An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin
  • Mutane Sama Da Miliyan 43 Sun Kalli Bidiyon Dandanon Shirin Talibijin Na Murnar Bikin Bazara Na CMG Ta Kafar CNN

Yana da kyau ga wanda zai rungumi noman lemon zaki, ya tabbata ya samu ilimin shiga fannin, musamman idan har ya na so ya cimma  nasara.

1- Samun Wajen Da Ya  Da Ce Don Shuka Shi: Za a iya farawa da dan kadan, sannan daga bisani a fadada ta hanyar sayen gonar da za ta ci kimanin bishiyar lemon daga 40 zuwa 50.

Ya kamata a tabbatar da kasar noman ta na da kyau tare sinadaren da ya kamata a cikin ta, inda za a iya gane hakan ne, a lokacin da ake gyaran gonar. Haka zalika, ya kamata ka lura cewa; shin abin hawa zai iya shiga gonar cikin sauki, domin dakon lemon da ya nuna zuwa kasuwa, domin sayarwa.

2- Kasar Noman  Da Ta Fi Dacewa A Shuka Lemon Zaki: An fi shuka shi a kasar noman da ruwa zai fi shigar ta sosai cikin sauki, sannan yin gwajin kasar noman na da kyau, don tabbatar da ganin tana da kyau wajen shuka lemon zakin ko kuma a’a?

3- Yanayin Da Ya Dace A Shuka Lemon Zaki: Lemon zaki ya fi saurin nuna a dausayi mai kyau,  sannan ya na jure wa kowane irin yanayi.

4- Nau’ikan Lemon Zaki: Ya na da kyau a zabo nau’in da ya fi dacewa, don shukawa, musamman domin samun riba mai yawa. Haka nan, an fi so a shuka wanda zai fi saurin girma.

5- Yin Ban Ruwa: Kamar dai sauran kayan lambu, shi ma lemon zaki na bukatar a yi masa ban ruwa, domin idan ya na samun ruwa akai-akai, za a fi samun amfani mai yawa, haka kuma ya kan jurewa rashin samun ruwa.

6- Ya Na Da Kyau A San Yadda  Lemo Ke Girma Daga Irinsa: Ya na da kyau a san yadda ya ke girma daga Irinsa, an kuma fi kuma yawan samun hakan ne a lokacin damuna, musamman ganin cewa, a lokacin ne aka fi samun wadataccen ruwan sama. Kazalika, ana kuma so a shuka Irin ya kai tsawon kimanin mita 1. 2, a kuma tabbatar da yana samun wadataccen haske rana tare da rika zuba masa taki a kalla sau daya a sati, domin ya yi saurin nuna.

7- Sanya Takin Zamani: Domin samun amfani mai yawa, ana iya zuba masa takin zamani, musamman don gudun ka da ya lalace bayan an shuka Irinsa.

8- Samar Wa Da Bishiyar Sarari: Ya na da kyau a sama wa bishiyoyinsa sarari, musamman don su dinga samun wadataccen hasken rana; ta yadda za su yi saurin girma, haka nan ana so a tabbatar da  bishiyar tasa ta kai sararin fadin kafa 12 zuwa  25 a tsakanin juna.

9- Yadda Ya Kamata A Kula Da Bishiyar Lemon Zaki: Ya na bukatar a kula da shi yadda ya kamata kamar dai sauran kayan lambu, musamman domin ba shi kariya daga kamuwa da cututtuka ko kwari, sannan za a iya yin hakan ne ta hanyar samar da maganin feshin da ya fi da cewa.

10- Lokacin Da Ya Fi Dacewa A  Girbe Shi: A bisa hakikanin gaskiya, bishiyar lemon zaki na kai wa tsawon shekara daya kafin ya nuna, ana gane hakan ne bayan lemon ya fara faduwa kasa da kansa.

Kazalika, sauran da suka nuna a jikin bishiyar, za a iya cire su. Haka nan, an kiyasata cewa, ana iya cirar kimanin lemon zaki 50 a jikin kowace bishiya daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
matsalar tsaro

'Yansanda Za Su Yaki Matsalar Tsaro Da Fasahar Zamani

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version