“Da sannun zamu bayyana masu ayoyinmu a cikin sasanni da kuma kawukansu har sai ta baiyana masu cewa shi gaskiya ne”
“Ina rantsuwa da Sama da taurari masu aukowa da dare. Me ya sanar dakai Taurari masu aukowa da dare? Tauraro ne mai huda (Rami)”
Da akwai dimbin tambayoyi masu yawan gaske a kan lamarin ita wannan tauraron na ‘Black hole’, da amsar su yake bukatar yin wani dan littafi ne wala alla.
A ranar 10/4/2019 masana kimiyar sararain samaniya suka iya samun damar fitar da hoton da suka dauka, hoto na farko na tauraron Black Hole, da suka ce yana a cikin sararin samaniyar Messier 87 (M87). Wannan tauraron yana cikin Taurarin ayarin Masaukan Burujin Birgo (Al azra’) Gwaggwabar bincike akan wannan Tauraron da samun nasarar daukar hoton sa na farko, ya biyo bayan kwashe shekaru 103 daga fara yin nazari akansa da ChidKarl Schwars ya fara a 1916.
Daga sunan sararin samaniyar da manazartan masu buncike suka gano wannan tauraon na Black Hole, (Massier 87) da kuma yanayin dabi’ar Black hole, zamuga kamar ana siffanta mana lamarin Imam Mahdi (A) ne, Saboda karfin ikon sa da zai sanya kowa ya zama a karkashin ikonsa, cikin hikimar Ubangiji, kowa sai ya makale a jikin ikon Imam mahdi (A), Watau duk wanda ya kusance shi sai ya zama nasa, mutum ko aljani ya so hakan ko bai so ba. Kamar yanda yake faruwa a farfajiyar tauraron Black Hole.
Kalmar Messier kalma ce da a larabci ke da ma’anoni biyu, ma’anar farko da dukkan ma’anoninta tana komawa ne ga siffan Imam Mahdi (A) (Aktharu faud ) Sai ma’ana ta biyu da ta ke koma ga ita wannan duniyar tamu da za ta cika da duhun kazanta ( Aktharu kaazarah). Allah ne masani
Me ya sanya Tauraron Black Hole mai ƙusurwoyi 12 ya kansance a cikin ayarin Burujin Birgo, da a ke danganta Burujin da Saiyida Zahra (A) da kuma Maryam (A)? Wannama tambaya ce da take bukatar zaman kanta.
An wallafa bayanai masu yawan gaske a kan wannan tauraron na Black Hole. Daga abin da masana suka fara bayyanar wa dangane da binciken wannan tauraron shi ne; Daga dan abin abinda wannan babban masanin Kimiyyar wato Albert Einstein da kuma “General theory of relatibity” da ya kawo, ya bayyana cewa a ganinsa, babu ta yadda tauraro mai tsananin nauyi zai iya faduwa saboda ya fi karfin “grabity”.
To amma ba a dade ba sai wani bincike ya sauya wannan tunanin na Einstein sauya, inda aka samu tabacin cewa taurari sukan iya faduwa bayan sun rasa karsashi a jikinsu. Wannan faduwar da tauraro yake yi a wani guri shi aka fara kira da “frozen star” (daskararren Tauraro) da farko kafin daga baya a koma kiransa da suna “Black hole” saboda a kan samu taurari da yawa ne kan fada ba lallai guda daya ba. Masana sun baiyana cewa tauraron Black Hole yana da kusurwoyi 12 da ake iya ganin shacin su gaba dayansu. Ba kamar na mu kusurwoyin ba na wannan duniyar da itama take da kusurwoyi 12 amma guda hudu kawai ake iya riskar ganinsu.
Dangane da wannan Tauraron ‘ *Najamus thaƙib (Tauraro mai rami a cikinsa) Tauraro ne mai haske a geffan sassan ƙusrwoyinsa, wanda kuma tsakiyarsa ya ke rami, ramin da ya sabbaba masa duhu. Surar Tarik ta bamu labarin Sararin Sama da kuma taurari masu bayyana da dare, (Tarik) Surar ta gaya mana ko menene kalmar Tarik yake nufi da cewa Tauraro ne mai rami (Thakib).
Abdudda’im Kaheel ya yi fashin baki a kan wannan tauraron na Black hole a bisa fahimtarsa da surar Tarik. Dangane da binciken da aka gudanar akansa a shekarar miladiyar 1967, da kuma sautin da aka samo daga wannan Tauraron na Black Hole. Da suka ce sautin ya yi kama da sautin karaurawa ko kama da sautin karar bugun guduma (Hammer). Hakan ya bamu ma’anar Tarik da Alƙur’ani ya kira Najamus thaƙib (Black hole) da shi, daga kalmar sunan Guduma da larabci.
In muka kalli irin bayanan da su masana kimiyar samaniya suka bayar a kan lamarin Black hole. Zamu iya cewa sura ta 81 (Surar Tak’wir) a aya ta 15 zuwa aya ta 19 an warware mana komai dangane da labarin ita wannan taurarauwar ta Black Hole. Da surar Tarik ta kawo labarin da sunansa (Najamus thakib). Duk da cewa aya ta 15 da aya ta 16 sune kai tsaye suke maganar ita tauraron na Black Hole. a mahangar mafasaaran zamaninmu, dangane da mu’ujizar Alƙur’ani
Ga abin da littafin na Allah mai cike da Mu’ujiza ya bamu labarinsa akan Tauraron Black Hole, cikin siffantawa, tun sama da shekara 1400 da suka gabata. A cikin surar Tak’wir. (81. 15-16)
(Fala uƙsimu bil khunnas, Aljawaril kunnas)
Ma’ana:
Ba sai nayi rantsuwa da Khunnas ba. Mai tafiya (jawar) ne kuma Kunnas
Anan ne gizo ke saƙa, menene Khunnas kuma menene Kunnas? Imam Ali (A) ya bamu amsa da fassarawarsa ga kalmar Khunnas da cewa Tauraro ne. A mahanga ta nake ganin wannan jawabin na Imam Ali (A) shine mabuɗi nayin wannan binciken da masana kimiyar samaniya suka gudanar akan wannan tauraruwar Thaƙib, Khunnas, Jawar, Kunnas.(Black hole).
Hakan siffa ce ta Black hole (Najamus thaƙib) da aka gano. Sai kuma ƙarin Sifarsa guda biyu (Jiwar da Kanas) Abin nufi shi tauraron yana yin yawo a cikin falakinsa a lokacin yawon na sa ne yake zama Kunnas. watau wurin da yake sharo duk abin da ya kusance shi zuwa cikinsa. Saboda ƙarfin Jazabarsa (Grabity). Sai su tare a cikin sa.
Sannan Malaman tafsirin sun baiyana cewa shi wannan Tauraron Khunnas yana daga cikin ayarin taurari 5 masu shawagi irin su Saturn (Zuhal), Jupiter (Mushtariy), Mars (Murikh), Benus (Zuhrah) da kuma Mercury (Utaradu).
Amma in muka koma cikin littafin Alkafiy (J,1 sh,341). Bihar j,24 Sh, 78. da Almuhajjah shafi na 24t.
Ummu Hani tace ta gamu da Imam Baƙir (A) sai take tambayarsa fassarar aya ta 15 da aya ta 16 na cikin Surar ta 81 (Tak’wir). Imam Baƙir (A) ya bata amsa da cewa: “Alkhunnas shine Imam mai ɓoyuwa a cikin zamaninsa yayin da aikinsa a cikin mutane ya yanke a shekara ta 260. Sannan zai baiyana kamar Wani tauraro mai haskawa a cikin duhun dare, in kika riski wannan idanuwanki za suyi sanyi. (ko zasu yi baƙo)”.
Menene alaƙar aya ta 3 (Annajamus thaƙib) na cikin sura ta 86 da kuma aya ta 15 (Aljawaril Kunnas) na cikin sura ta 81. Ayar da ke siffanta Tauraro mai rami a ciki sa (Black Hole). Zamuga cewa duk ayoyin suna da Kalmomi biyu ne dukkansu. Sannan kuma an gina su ayoyin biyu ne kowannensu a bisa haruffa 11.
Tazarar shekarun fara nazarin Tauraron Black hole na ChidKarl Schwars daga 1916 zuwa 2019 shekaru 103. Sura ta 103 a cikin Alƙur’ani ita ce surar Asr. Surar da take magana akan zamanin baiyanar Imam Mahdi (A). Ko wannan yana yi mana nuni da cewa ƙarshen aikin aya ta 17 watau yankewar duhun dare na zamanin tsawon fakuwar Imam Mahdi (A) a cikin Mutane, a yanzu ya kawo ƙarshe kenan? Sai fara aikin aya ta 18 da take cewa; (Da asubahi idan ya yi tanaffus) duk dai a cikin surar Tak’wir? kalmar *Tanaffus in muka dora kalmar a bisa lugga da shari’a zamu ga cewa a wannan zamani akwai karin fassara da ma’ana a kan wanda mafssara suka bayar a farko. In muka yi la’akari da badinin fassarar ayoyin da Imam Baƙir (A) ya bayar. Allah ne masani akan komai.
In muka yi la’akari da siyakin aya ta 19 na cikin surar Tak’wir zamu iya danganta lamarin da sura ta 53 (surar Najami), Domin gaskata zancen Manzo mai girma.
Hakika wannan zamani ne na farawar ci gaban ilimi da fadadarsa, da zai cika da baiyanar Imam Mahdi (A). Wanda a yanzu muke ganin farkon farwarsa.
Allah ka taimaki Najamin kasarmu Nijeriya ka sanya muga lokacin da zai yi wa kasar mu hukunci na adalci da izininka ya Rabbah.
Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya
Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...