Idris Aliyu Daudawa" />

Nazari A Kan Tabarbarewar Al’amurra A Arewa

Dangane da wannan batu mai take a sama, kashi na biyu kenan na rubutun da nake yi a kan yadda tabarbarewar al’amurra take kasancewar a Arewa, ba domin komai ba sai don saboda kawai gyara kayanka wanda ba zai taba zama sauke mu raba ba, da wani wanda yake son a kawo gyaran su al’amuran yake yin magana akai- akai, sai aka ayi ma shi al’amarin da kallon wata manufa daban.

Kamar maganganun da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, ya kan yi lokaci zuwa lokaci, akan yadda ya dace a tafiyar da al’amurra mulki, musamman ma a bangaren Arewa.
Idan muka duba  yadda wasu matan aure suke kashe mazajensu yanzu abin ya zama kamar ruwan dare gama duniya, daga wadda zaka ji labarin wata  matar ta zubawa mijin nata ruwan batiri, sai wadda zata sa kwalba ta kashe shi ko kuma ta yanke masa al’aurarsa da Reza, sai wadda zata yanke ma shi Hanci da kuma Harshe bayan kuwa lokacin da aka yi auren nan an yi shi cikin soyayya ne da kuma kaunar juna.Wannan abu kuma kusan yanzu yana ma neman ya kasance tamkar wata al’ada ce a tsakanin mata wadanda kuma kafin ka ji an ce Kirista ce ta aikata wannan ta’asar, abin yana da mayukar wuya, domin kuwa daga karshe abin sai ma ja ji labarin  cewar ai musulma ce ta aikata haka nan.Allah wadaran naka ya lalace  lokacin da Rakumin dawa da yaga na gida  har ma an kaiga dora mashi kaya a baya.
Yanzu ku san  wanda yake  aikata ashararanci da kuma Fasiki muddin dai yana da Kudi shine wanda ake ganin Kirkin shi a cikin al’umma, yau komai gaskiyarka da kame kanka idai dai kai baka da kudin kai tamkar banza kake cikin wasu al’ummar yanzu. Kawai ma yanzu al’umma wasu sun dawo daga rakiyar gaskiya an koma wajen karya, muddin dai za a samu abin hannu. Wannan watakila shi yasa wasu yanzu suka canza akalarsu suka daina hawan Jaki mai mangala suka koma wanda ake yi ma shimfidar gararar buhu irin ta da can. Cikin wannan marrar da ake ciki wani ko wasu abubuwan kunya yanzu wasu dasu suke yin ado, wasu cikin al’umma zasu yi ta’asarsu yadda suke so, suyi ta shegantakun su, gani ma suke tamkar sune suka halicci kansu ba Allah bane ya halicce su ba.Babu wata maganar tsoron cewar watarana fa mutum duk yadda ya kai ga yin shegantaka, sai abubuwa biyu sun faru da shi watarana, ko dai wata cuta, ga kuma tsufa sai kuma mutuwa, ga kuma hisabi bayan yadda za ayi kwanciyar ta shi kabari. Amma sai ka ga wasu tamkar ma an yi ma masu wahayi ne na cewar ai su suna nan sune wadanda za a bari su yi gadin duniya. Maganar aure yanzu ba duka Iyaye bane  suke bincikar hali, asalin su ma’auratan, duk dai abinda zaka ga wasu sun fi sa ma idanu shine, da  dai zarar an yi maganar Kudi masu gida rana, koda dai akwai wani abin fada ma tsakanin asalin su ma’auratan, sai kaji an yi shiru ba a maganar wannan al’amarin. Irin hakan ne daga karshe sai tafiya ta fara tafiya daga baya kuma ido ya yi neman raina fata, lokacin ne kuma za a ce a dauki mummunan mataki.
Rashin adalci yanzu shine karara ya yi yawa ba daga wasu Iyaye ba, al’umma, makaranta ko kuma daga karshe Hukuma, ana ta aikata shi, ba tare da kallon baya ba, saboda shi juwa bayan idan da masu yin suna yin tunanin da komai zai iya faruwa a gaba.
Da koma fara tunanin hakan ba zasu fara ba.Musamman ma idan kana cikin harkar shari’a yau yadda abin kan daure ma wasu kai ganin yadda wani lokacin abin hannun mutum shine ke bashi adalci wajen shari’a ko kuma akasin hakan ga wasu shari’ar da suke kallon masu gida rana. Wasu iyaye yau basu sauke nauyin da Allah ya dora masu ajan tarbiyyar ko kuma biyan hakkokin ‘ya’yan da suka haifa, wasu abinda suka sani shine su haifawa al’umma ‘ya’ya. Dabbobin da suke kiwo ma sai dai su shiga wani gida su rika cin kayayyakin mutane, abu nasu shine ranar da suka so sayar da wata daga cikin dabbar ko kuma Kazar basu ma san inda take kwana ba, sai an nemota, kai kun san inda Kaji na to dabbobi na suke kwana? Don Allah a dubi wannan kalima da idanun basira mana. To haka wasu iyayen suke da ‘ya’yansu basu damu da duk wata dawainiyar su ba wadda shari’a ta dora kansu ba, kamar ciyarwa, shayarwa, ilimi, kula da lafiya, sutura, da dai wani abu mai muhimmanci, sai lokacin da ‘ya’yan nan a suka zama munzalin za a karu dasu lokacin ne za su fara kumfar baki har ma kotu wasu suna iya zuwa cewar ai ‘ya’yan su ne. Haka fa wasu daga cikin iyayen suke yanzu suma sun zama cima – zaunen, inda ma matan nasu sune ke  rika tafiyar da gidan  suke yi, ba abinda ya dame su, wasu sune mazaje ne kawai a baka, amma a zahirance mata neke tafiyar da gidan. Duk da yake ma akwai gidajen da yanzu mata sune ke tafiyar da su, magidanta kuma sun zama mazare ke nan. Kota wanne bangare ma idan dai dan Arewa bai zama na daya ba to ya kasance na biyu wajen mukami duk sai ya yarda tukunna kafi wani ko kuma wasu abubuwa su kasance. Idan dai bai kasance na Shugaba ba a wuri to ya zama mataimaki, to amma dai abin namu wasu har yanzu daga cikin Shugabannin namu basu abin nan da ake kira karatun ta natsu ba, sune dai ta kara girma amma kuma kwana cikin daji suke yi.
Yadda su Shugabannin Arewa suka muke ta lokacin da ake karkashi mulkin Parliamentary wato tsarin mulkin da ake da Shugaban kasa da kuma Firayim Minista sai kuma Firimiyoyi, yadda suka tafiyar da salon mulkin nasu abin akwai ban sha’awa matuka. Wani ban takaici daya shine dole ne ma yanzu abin ya rika daure wa mutane kai yadda sauran sassan da suka hada da sashen Kudu maso yamma, Kudu maso gabas, da Kudu maso Kudu suke tafiyar da al’ummar nasu, abin da akwai ban sha’awa. Duk fa yadda su Shugabannin Arewa suka kafa ginshikin mulkin Arewar ko kuma yadda Shugabannin sassan Nijeriya suka yi ai abin yana nan a rubuce, cikin tsarin mulki yadda aka tafiyar da gwamnatin a wancan lokacin sai dai kawai watakila sun a bangaren Arewa suke ganin ko basu waiwaye ba ai za su iya cin jarabawa, ko kuma ba su son yin amfani da tsare- tsaren nasu bane. Allah ya sa dai su Talakawa su canza halin su tare da kuma su Shugabannin kowa ya rika yin abinda zai taimake shi da kuma ‘yan’uwan shi da kuma wurin daya baro, da ana yin haka, zuwa yanzun ai da ba karamin ci gaba bane za a samu. To amma maimakon hakan abin sai ya kasance an san ga babbar madogarar wanda idan aka bi za a samu wani ci gaba, da kuma so da kuma kaunar juna a Arewa, sai kuma kamar dai wanda Iyayen sa suka yin masa Baki a sa gaba wani tafarkin da daga karshe abin yana iya zama tamkar abin nan da mutane ke kira da suna “Yawon duniyar Kare wanda yake kasancewa aikin banza, domin shi bai dawowa gida ballantana kuma har ace watarana ya kai ga yin tunanin ya yo aike zuwa gida ba”. Kai ma ko kuma na iya yin tsammanin ko a lokacin da suke akan madabun ikon suna makancewa ne sai sun kammala wa’adin nasu suke komawa masu idanu,  ko kuma abin nan da ake kira da sunan “Tazo mu jita” wanda kuma wannan sai an fara fada maku cewar “Gatanan gatanan ku”.

Exit mobile version