NAZARI: Da Hakan Za A Sake Yin Ku?

Daga Idris Aliyu Daudawa

Abin ma da akwai ɗaure kai, to ɗaure kai mana saboda ana hana wane kiwon Akuya, amma shi ne kuma mai cewar ai ƙyalla ma ta haihu. Yanzu kusan dai sauran watanni bakwai suka rage, a cika shekaru uku da wasu waɗanda aka zaɓa a muƙaman siyasa a wannan zubin da ake ciki, ba za a iya cewa ba a taka rawar gani ba, wasu sun ba mara ɗa kunya, wasu kuma waɗanda suka zaɓesu sai cizon yatsa suke ta yi yanzu, na dana sani wadda masu iya magana suka ce ƙeya ce domin a baya take.

Wakilai tun daga na mazaɓar kansila zuwa na majalisar dattawa yanzu lokaci ne wanda, ya kamata su yi ma kansu hisabi tun ma kafin ranar da masu zaɓe, zasu yi masu ƙiri ƙiri, wanda abin bai wuce ‘yan awonni ba, a wannan ranar, kowa zai gane gidansa na gaskiya. Ma’ana ko da a sake zaɓenshi, ko kuma a bar shi da halinsa. Wannan kuma ya dangantane akan ire iren ayyukan da suka yi ma al’ummar mazaɓarsu, ba wai a basu kuɗi ba kawai kamar yadda wasu suka fi son haka, shi yasa dama aka ce idan Ɓera na da sata to Daddawa ma tana da wari, domin  ai sai da  shi Ɓeran ya ji ƙanshinta ne ya ke tsaida shawarar inda zai kai na shi farmakin.

Daga cikin shekaru huɗu an ci shekaru biyu da watanni biyar,  abin da ya rage ke nan shekara ɗaya da kusan watanni bakwai. Idan har da akwai niyya yi ma mazaɓu ayyuka to, ana iya cewar ba a makara ba, za a iya yin abubuwan da zasu kawo ma al’ummar mazaɓunsu cigaban wuraren da suke. Hakan ne kuma zai sa su canza ra’ayinsu daga matakin da suka ɗauka, na ba zasu sake zaɓen wanda bai damu da cigabansu ba.To inda aka yi rashin sa’ar sai ga shi  wasu daga cikinku ba wai son cigaban mazaɓunku kuke ba,  sune kuma waɗanda suka taka muhimmiyar rawa, ta tabbatar da cewar kun kai ga ganin bakin gaci.Wani abu kuma mai ɗaure kai da rikitarwa sai ga  yanzu wasu daga cikin kune, suka juya baya wato bayan an masu Rana sai  su kuma da yake suna da dama sai suka mai da martanin da bai dace ba, suka yi Dare, wannan kuma sam bai ƙyautu ba.

Shekara dai kwana ce abin haka yake domin kuwa yanzu an kusa komawa fagen sake neman wani zaɓen, kamar dai yadda wasu da irin hakan ta faru, yanzu abin ya zama tarihi, na sun taɓa zama ‘yan majalisa, kuma wasu daga cikinku haka zata iya kasancewa gareku. Saboda ai dama duk tafiya irin wannan ai dole ne sai an bar wasu a baya. Kamar yadda ake kiran wasu da sunan tsofaffin ‘yanmajalisa, hakanan watarana kuma haka za a riƙa kiranku da suna watarana, sai kuma ta zo ko dai ana abubuwan da suka dace ko kuma saɓanin haka.

Talakawa sun ji daɗin zaɓen wasu daga cikinku domin wasu sun yi  wakilci mai ƙyau, ko dai a majalisar Ƙaramar Hukuma, a matsayin kansila, a majalisar Jihar ɗan majalisar Jiha, sai kuma majalisun ƙasa, da suka shafi na Wakilai da Dattawa. Gaskiyace wasu daga cikinku sun taka rawar gani, wajen yin ayyukan da zasu kawo cigaban mazaɓunsu, wasu kuma abin ba a cewa komai. Talakawa suna ta cizon yatsa da yin da nasani domin kun basu kunya, maimakon ku yi abin da ya dace, sai kuka tsaya yin wasu abubuwan da basu dace da muƙamin ku ba, na ‘yan majalisa.

Akwai hana ruwa gudu nan muna iya kallowa tun daga Ƙaramar Hukuma wani lokaci wasu daga cikinku ku, kan hana ruwa gudu, musamman ma idan kuka ga kune ke da rinjaye a majalisar. Yana da ƙyau mu yi ɗan waiwaye adon tafiya idan ma muka kalli Jihar Kaduna lokacin jamhuriya ta biyu ai wannan ya isa, lokacin akwai jam’iyyu kamar huɗu zuwa biyar masu girma da ƙarfi, kamar su NPN, PRP, NPP, GNPP, sai kuma UPN. Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa na jam’iyyar PRP ta marigayi Malam Aminu Kano shi ne gwamnan jihar Kaduna, PRP ita ce ta lashe Jihohi biyu Kano wadda marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya yi ma gwamna.

Haka Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya tafiyar da ragamar mulki ya yi watanni yana mulkin jihar ba tare da kwamishinoni ba, saboda ‘yanmajalisa masu rinjaye daga jam’iyyar NPN ce  suke. Mamman Abubakar Ɗanmusa shi ne shugaban majalisar har dai  sai da kai, daga ƙarshe ‘yanmajalisar suka yi amfani da rinjayen da suke da shi, suka tsige gwamna Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa ranar 23  ga Yuni 1981, marigayi Dokta Bala Usman Malami daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria shi ne ya y i ma shi Sakataren gewmnati, tun daga wancan lokacin ne suka kafa tarihi a matsayin jihar  farko da aka fara tsige gwamna a siyasar Nijeriya. Alhaji Abba Musa Rimi wanda shi ne mataimakin gwamna a lokacin, shi aka rantsar a matsayin gwamna, shi kuma lokacin daga ɓangaren Katsina ya ke, kafin a ƙirƙiro jihar Katsina. A Jihar ma musamman ma idan suka ga suna da rinjaye sai su riƙa tuƙin gangancin wajen tafiyar da ita gwamnatin, lokutta da yawa sai a riƙa yi ma gwamna barazanar za a tsige shi daga mulki, idan kuma muka gangaro majalisar ƙasa wadda ta ƙunshi ‘yanmajalisar Wakilai da kuma ‘yanmajalisar Dattawa sai mu tuna da irin wainar da suka toya a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, duk dai ‘yan jam’iyyar PDP ne masu rinjaye, nan ma haka suka yi  ta ƙoƙarin sakar ma shi da hawan jini na barazanar tsige shi.

Nan bada daɗewa ba domin ai ba wani nisa aka yi ba mai tsawon da har mutane zasu ce sun manta, na hanyoyin da su ‘yanmajalisa suka bi suka zaɓi shugabanninsu, a wannan sahun siyasar canji da muke ciki, kowa kuma ya kwana da sani yadda ake ta kiki kaka tsakanin majalisar zartarwa da ‘majalisun ƙasa yadda wasu lokutta suke ma fadar shuagaban ƙasa wani irin kamu kamar yadda cutar Ƙuddumu ke kama kaji lokacin sanyi, ko kuma cutar nan da ke yi masu nan da nan faraɗ ɗaya su sheka barzahu wato wadda ake kira da sunan Fakat.

Lokutta da yawa take taken majalisun biyu waɗanda jam’iyyar APC ke da rinjaye yana ɗaure ma al’ummar ƙasa kai da kuma ban haushi, yadda wani lokaci rijayen nasu sai ya kasance ba wani amfani yake ba wanda zai shafi al’umma, saboda ɗaukar dogon lokacin da ake yi kafin a samu cimma wata matsaya wadda zata amfani mutane, komai ƙyau ɗin da take da shi wannan yana nufin fitar da wani ƙuduri wanda daga ƙarshe zai iya zama doka wadda zata amfani al’umma, wani lokaci sai an mai da al’amarin ya kasance mummuna, daga baya a samu amincewa da shi, wannan kuma sau da yawa sai abin ya kasance ya sallace wato shi al’amarin wani ma ya na ƙoƙarin lalacewa sai an kai ga ƙoƙarin zuwa a zubar a Juji, ko Bola domin yana iya zama shara mai ɗauke da kwayoyin cuta.

Gwamnoni ma da shuagabannin Ƙananan Hukumomi ku ma wasu daga cikinku ku kan yi kutinguila ma tafiyar da wasu majalisu ke yi, ba ma kamar idan kuna daga jam’iyya ɗaya ne, nan da nan a canza shugabanni ba wani abu bane, domin sai bango ya tsage Ƙadangare kan samu kafar shiga, wani lokaci ɓangaren majalisu wato masu dokoki ke nan, da kuma majalisar zartarwa wadda ta ƙunshi shugaban ƙasa da Ministocin shi, kamar suna gwara kan mutane ne, ko an shiga tsakaninsu watarana ana iya jin kunya, domin kamar tsakanin Mata da Miji ne lokacin da wata hatsaniya ta  samu, shiga harkokinsu abu mai wuya ne,  sai an yi taka tsan tsan, idan kuma aka ƙi ji, to ba fa za a ƙi gani ba. Nesa nesa dai wai kallon Kurar Ƙosau.

Koma dai minene ‘yan siyasa ya kamata su gane Talakawa masu zaɓensu , ba wai suna fata bane, idan sun tura mota ta tashi ta barsu da ƙura, ko ta zubar ma wasu daga cikinsu Haƙora, babban abin da suke fata da kuma tsammani da ga ‘yansiyasar,  shine  su tuna , suma fa suna da wuraren da suke son zuwa ya kuma kamata a ɗan riƙa rage masu hanya, ba wai koda yaushe a ce su tura mota ba,bayan kuma su sun san ita motar ba injinta bane ya yi sanyi, sun san so kawai ake a wahalar dasu da kuma yi masu wasa da hankali ,maganar tura mota koda wane lokaci. Ai sun gane cewar yawancin motocin da ake cewa su tura, suna iya  tashi, bugu ɗaya da zarar an sa makulli an ɗan murɗa zata tashi, ana dai son a wahalar dasu ne, domin haka sun gane. Wani rikici ma dake kasancewa tsakanin majalisar dokoki da ta zartarwa, kamar wasa ake yi da hankalin mutane, manufa a ɗan gwara hankalin mutane domin a fahimci, ta yaya za a ɓullo masu, ko kuma dai dai lokutan da waɗannan rigingimun ke faruwa suna sama da ƙasa, a lokacin kallo yana iya komawa sama, kafin har a kai ga ganewa, to al’amari ya kai zuwa wuraren da ba a taɓa tsammani ba.

Exit mobile version