Daga Jafaar Jafaar
A dauri can, zamanin da duniya ke kwance, kudin Naira kudi ne mai matukar daraja a kasashen Turai, Asiya, da ma Daular Larabawa, wanda hakan ya sanya ma’abota tu’ammuli da Nairar suka ribace ta a huldar cinikayya dama kasuwancin kasa da kasa.
A irin wancan lokaci, darajar Nairar sama take da kudaden Amurka da na Saudiya, al’umai da dama na haba-haba da ita. Amma abin mamaki, waccan Nairar da ada din ta yi wancan tashe, ita ce yau aka wayi gari kimarta ta fadi da har ta kai ko a kasuwar Agadas ake ma kallon hadarin-kaji. Kai hatta a cikin kasar Nijeriyar, Naira ba ta da wani mutunci a idanun ‘yan kasar. Kila hakan bai rasa nasaba da watsi da kananan kudaden Nairar, kamar su Sulallan Naira Guda da takardun Naira Biyar da Goma da ‘yan kasar suka yi.
An yi ta korafe-korafe tun bayan da gwamnatin Nijeriya ta sanar da farashin Hajjin bana, wanda bisa al’ada, kimanin jihohi ashirin da daya na musulmi ne da birnin Tarayya Abuja kan lazimta a kasar Saudiya karkashin kulawar Hukumar kula da aikin Hajjin Musulmai ta kasa, wato NAHCON.
A bara, sa’ad da muke jimamin faduwar darajar Naira, wasu ‘yan Nijeriya nan-da-nan suka yi ta ganin baiken masu kokawa kan lalacewar Nairar, har suke gwabin wai “Da tashin Bam gwamma tashin Naira”, wanda kuwa a zahiri, lalacewar tattalin arziki ka iya haifar da rikicin dama tsadar rayuwa.
A yanzu haka dai, maniyyatan aikin hajjin na bana, na ta ‘yan dabarun ganin sun gagganda sun nemi cikon kudin da za su cikata kudin kujera kan dadin da aka samu. To amma abin tambayar a nan shi ne: Me ya sa Alhazan Nijeriya za su biya kddi sama dana maniyyatan sauran kasashe?
Haka dai za ka yi ta ji; wannan ya ce kaza, wancan ya ce kaza, kowa kuma da abin da za ka ji yana fadi. Amma dai cikin wadanda suka yi tsokaci kan wannan lamari, akwai bayanan shugaban kamfanin jigilar jiragen sama na Med-biew, Alhaji Munnir Bankole, wanda a iya cewa jawabinsa ya ba da haske sosai kan wasu batutuwa da suka shige wa maniyyata duhu.
Matsayinsa na guda cikin masu ruwa da tsaki a sha’anin jigilar Alhazai, kasancewarsa da ya shafe sama da shekaru Talatin a harkar zurga-zurgar jiragen sama, Alhaji Munnir shi ma dai ya bayyana cewa tashin farashin chanjin dai shi ne ummul-aba’isin tsadar da ake ganin kudin kujerar na bana ta yi.
A bayanin nasa, ya nuna cewa a tsarin jigilar Alhazai, a duk lokacin da jirgi ya kwashi maniyyata ya kai su kasar Saudiyya, to idan ya tashi dawowa zai dawo ne tsura, ba tare da Fasinja ko da guda ba, wanda hakan kadai wani babban dalili ne da ko ba a gaya wa kowa ba, ka san cewa sha’nin jigilar Alhazai ya bambanta da na jigilar Fassinjoji zuwa wata kasar.
Sannan Munnir Bankole ya ce yayin da aka gama jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya, to doka ce cewar jiragen jigilar Alhazai ba za su zauna a kasar ba, sai dai kowane jirgi ya koma kasarsa, har sai ranar da aka tsara za a fara kwaso Alhazai a maido su gida. Ka ga ke nan haka jiragen saman za su dawo Nijeriya tsurarsu bada kowa ba, sannan idan lokacin fara dawo da Alhazan ma ya yi, su koma kasar Saudiyar tsura ba tare da Fasinja ba.
Har ilau dai, a kowane zuwa, duk kamfanin jirgi sai an caje shi Dalar Amurka Dala Dubu Shida (sama da Naira Miliyan Biyu), matsayin harajin ketarawa ta sararin samaniyar kasahen Chadi da Sudan, da jiragen Nijeriya kan ratsa kafin su je kasar Saudiya.
To me ya sa kuma Alhazan da suka biya a jirgin yawo, wato Intanashinal, suka fi samun rangwamen farashi da na Alhazan da suka biya ta wajen Hukuma, wadanda ake kira da ‘Piligirims?’ Ba wani dalili bane illa adadin kwanakin da Alhazan ‘Piligrims’ ke yi a kasar Saudiyya ya nunka adadin kwanakin da Alhazan jirgin yawo ke yi a kasar. Domin a yayin da Alhazan ‘Piligirims’ ke yin kwanaki Arba’in a Saudiyar, su Alhazan jirgin yawo bai fi su yi kwanaki Goma sha Bakwai ba. Duka wannan kuma, ba ya da wasu ‘yan hidindumu da Hukuma ke wa Alhazan ‘Piligirims’ din wadanda babu ga ‘yan ‘Intanashina.’
A shekarar bara, duk da cewar farashin canjin ya kasance ne a Naira Dari da Casa’in da Bakwai kan kowace Dala, amma gwamnatin Nijeriya sai da ta sanya tallafin kimanin Naira Milyan Dubu Sittin da Takwas matsayin daunin kudin Hajjin bara.
Mun sani cewar kasafin Nijeriya na bana an girke shi ne akan Naira Dari Uku da Biyar kan kowace Dala guda. Don haka idan ka lissafa Naira Dari Uku da Biyar din sau Dala Dubu Hudu da Dari Takwas da Biyar, matsayin kudin kujerar kowane maniyyaci, za ka iske ya yi daidai da Naira Miliyan guda da rabi.
To, amma wani abu da ba mu gane ba shi ne, hatta a wannan farashi fa, gwamnatin tarayya sai da ta sanya tallafi a kudaden aikin Hajjin na bana. Wani kusa a gwamnatin tarayyar ya shaida min cewar a banan, sai da gwamnati ta biya Naira Dubu Dari Uku da Biyu akan kowane maniyyaci don a saisaita tsefewar farashin canjin Dalar ga Alhazai. Wanda ka ga idan ka lissafa wancan kudi sau Dubu Saba’in da Biyar adadin yawan maniyyatan bana, za ka iske akalla ba akasara ba, gwamnatin Nijeriyar sai ta yi cikon sama da Naira milyan Dubu Asirin da Biyu daga aljihunta.
A wannan yanayi Nijeriyar ke fama da lalurar shagidadden tattalin arziki; yunwa da fatara a ko’ina a kasar, ina ga babu hikima idan aka yi watsi da irin wadancan matsalolin rayuwa da ‘yan Nijeriyan ke kokawa a kai, aka kwashi kudaden kasa aka antaya a aikin Hajji kawai saboda a samar da kudin kujerar kasa da yadda aka yanka. Na tabbata ladan ciyar da ‘yan kasa da ke da bukata ya dara ladan bada tallafin aikin Hajji, tunda batu ne na rai da ibada.
Zan yi matukar takaici a ce gwamnatin da ba ta iya samar da tallafin man fetur, ko gari, ko shinkafa ga talakawanta ba, amma ta buge da samar da tallafin aikin Hajji ga masu akwai. Mamaki na ma shi ne yadda talakan da sai kullum ya fita sannan yake samun na hatsi, amma shi ne za ka ji shi yana neman wai gwamnatin ta debi kudi ta antaya a rangwamen kujerar Hajji.
A tafsirinsa kan Sura ta 3 Aya ta 97 a cikin Alkur’ani mai girma, cewar Allah madaukaki: “Kuma mun sanya Ziyartar Dakin Kaba’a matsayin rukunan ibada ga mutane ga wanda ya samu iko.”
Malam Bilal Philips ya ce an ruwaito daga Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare Shi yana cewa: “Iko a nan ana nufin isasshen guzuri da karfin tafiya. Don haka, dole musulmi ya zamanto ya wadatu da abin da zai ci da wanda zai bari idan ya yi niyyar zuwa Hajji. Idan har sai ya yi rance sannan zai samu damar ziyartar dakin Allah, to aikin Hajji bai hau kansa ba…”.