Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home MANYAN LABARAI

NAZARI: Kalaman Sarkin Kano A Faifan Nazari

by Tayo Adelaja
July 11, 2017
in MANYAN LABARAI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Hafsat A. M Abdulwahid

Na rubuta wannan takarda ne domim bayar da gudumuwata akan maganganun da ake yi game da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan maganar karin aure ga marasa halin yin hakan. Kafin in yi nisa a bayanin da zan yi, ya kamata mu fara sanin shin mene ne shugabanci a musulunce, wane ne shugaba a musulunce, mene ne muhimmacin shugaba a musulunce, mene ne hakkokin da suka rataya kansa a musulunce.

Shugabanci shi ne baiwa mutum ikon ya jagoranci al’ummarsa a gida, Unguwa, kauye, gari ko Kuma kasa ma gaba daya. Haka nan shugaba shi ne mutumin da aka zaba domin kiyaye hakkokin al’umarsa, rayukansu, mutuncinsu, dukiyoyinsu tare da gyara akan inda ya ga ana kauce wa fadar Allah da Manzonsa, a bisa rashin sani ko akasin haka.

A musulunce kafin a zabi shugaba, ya zama wajibi a tabbatar da halayensa na gaskiya, adalci, rikon amana da jajircewa akan hakkokin da suka rataya a wuyarsa, wato nauyin da ke kansa. Haka nan yana da muhimmanci shugaba ya zama mai ilimi, domin ilimi shi ne jigon tabbatar da hankalinsa, basirarsa, hakurinsa, adalcinsa, natsuwarsa da jajircewa akan abin da yake gaskiya ko da ba zai yi wa wasu dadi ba. Ya kuma zama mutum da ba shi da shinge tsakaninsa da jama’arsa, wannan  kadan ke nan daga cikin abubuwan da suka shafi shugabanci da kuma shugaba a musulunci.

Sayyidina Abubakar ( RA ) a jawabinsa lokacin da aka nada shi Halifa, ya ce. “ya mutane na an ba ni amanar ku, duk da cewa ban fi ku da komai ba. Mafi rauni cikin ku ko kuma mara karfi zai zama mai karfi, sai na tabbatar da hakkokinsu. Mafi karfi cikin ku zan dauke su mafi kasawa, zan tabbatar da sun bada hakkokin su. Kamar kowa nake, idan kun ga na yi daidai ku bi ni, idan kuma kun ga na karkace ku mikar da ni, idan kuma na kuskure ku gyara mani.”

Sayyidina Umar ( RA ) a duk lokacin da ya nada Gwamna bayan dan lokaci kadan zai tambayi ‘yan gari, ko yana kyautata masu? Musamman bayi, ko yana zuwa jana’iza?, ko yana karbar wadanda suka memi ganinsa? Wato bai sa shinge tsakaninsu ba. Idan an ce yana duk abubuwan da aka lissafa, to zai bar shi kan mulki, idan kuma ba ya ko da daya daga cikinsu, to zai sauke shi.

Haka kuma akwai lokacin da Sayyidina Umar (RA) ya tambayi Sahabbansa ya ce, “idan na ba wani shugabanci ko na sauke nauyin da aka dora mani? Sahabbai suka amsa da lalle za ka yi abin da ya dace. Sayyidina Umar ya ce a’a, ba haka ba ne, ya zama lalle ne in tabbatar da ya yi abin da na umurce shi da shi.”

Haka kuma lokacin da aka ci Jerusalem, wato Kasar Isra’ila, mutanenta suka ce ba za su bude kofa ba, har sai shugaban musulmi ya zo sannan za su ba da kai, Sayidina Umar (RA) ya tafi da mutum daya tak, suna cikin tafiya sai ya zauna yana kuka, sai abokin tafiyarsa ya tambaye shi, mene ne dalilin kukansa? Sai ya ce wannan hanyar ba ta da kyau, kuma ko da jaki ne ya yi tuntube sai Allah ya tambaye ni.

Idan muka duba yadda Sahabban Annabi (SAW) suka yi shugabanci za mu tabbatar da maganar da Sarki Muhammadu Sanusi ya yi tana kan hanyar gaskiya, domin ta shafi jama’arsa maza da mata har ma da yara. Domin maganar aure ta shafi maza mata da yara, har ma da masu zuwa nan gaba. Don kuwa addinin musulunci ya zo da ka’idojin aure domin tabbatar da hakkokin kowane ma’auraci mace ko namiji. Sharuddan da idan ba a cika su ba babu aure, har ma akwai inda auren ke haramta.

Misali. Namijin da ba ya iya kusantar iyalinsa, aure ya haramta gare shi. Haka kuma wanda ba zai iya ciyar da iyalansa ba, shi ma aure bai halatta gare shi ba. Sutura ma na daya daga cikin abubuwan da aka wajabta akan ma’auraci.

Kadan ke nan daga cikin ka’idojin aure. Amma sai muka wayi gari mazan da ba su da sana’a, ba su da aikin yi, amma suna aure har ma fiye da daya, su a je mata barkatai ,ba ci, ba sha, ba sutura balle muhallin kirki. Su dinga haihuwar ‘Ya’ya rututu ba tare da kula da hakkokinsu ba, balle tarbiyyar su. Kamar yadda musulunci ya yi umarni da hakan. Sai dai matar da ‘ya’yan su nemi abinci ta hanyar tallah ko aikatau.

Wannan na daya daga cikin dalilan lalacewar ‘ya’ya mata da maza, wadanda ke shiga hanyoyin da Allah ya haramta kamar zina, luwadi, madigo da shaye-shaye (Wa’iyazu Billahi). Allah ka tsare mana ‘ya’yan musulmi, ka kawo mana karshen wadannan masifun.

Sunnar Manzon Allah (SAW) da ya kamata a ce abar alfahari ce, an mayar da ita bala’i, tunda an daina bin ka’idojinta, domin ana barin mata a cikin wahala, kunci, bakin ciki da takaici. Abin haushin ma, ana fakewa da amfani da addinin musulunci ana tafka wadannan abubuwan don son zuciya. Allah (SWT) ya ba mata daraja da daukaka a musulunci fiye da duk wani addini.

A cikin Alkur’ani Mai Girma, a cikin Suratul Bakara aya ta 223 ya kwatanta mace da gona, kuma kowa ya san muhimmancin gona, domim idan ba gona ba abinci, idan ba abinci kuma ba rayuwa. Haka kuma a suratul Bakara aya ta 187 ya kwatanta mace da sutura/tufafi, wanda kuma idan babu su ba mutum, sai dai idan mahaukaci ne.

Dan haka mace na da muhimmanci, domin Allah ya ba ta daraja, amma aka yi watsi da dokarsa ake wulakantata. Idan muka duba a musulunce mace na da darajojin da musulunci ya ba ta. Mace uwa ce, haka kuma mace yaya ce, bugu da kari 3. Mace ‘ya ce kuma mace kanwa ce. Kuma mace abokiyar rayuwa ce. Amma aka manta duk wannan aka yi watsi da duk wannan ake bin son zuciya, aka dauko wasu al’adu marasa ma’ana aka cakuda su da dokokin da Allah ya shimfida na aure, wanda hakan ya jawo lalacewa da tabarbarewar aure a musulunci, har ya zamana ba a daraja shi yadda ubangiji ya umurta.

A duk lokacin da aka kauce wa dokokin Allah, to sai an ga ba daidai ba. A zamanin da ba za ka samu magidancin da bai da aiki ko sana’a ba, balle ka samu mutum ba ya da aikin yi sai tsugunawa kofar gidan wani yana maula.

In muka duba a lokacin aure na da daraja, amma yanzu aure ya wulakanta. Don namiji zai yi aure lokacin da ya ga dama ba tare da daukar nauyin da ya wajaba a kansa ba, ya kuma yi saki lokacin ya ga dama ba tare da shakku ba. Tunda an dora wa iyaye nauyin da musulunci bai dora masu ba. Don wulakanci ma banda kayan daki, har wata al’ada ake ta yin garar kayan abinci in an aurar da yarinya. A gaskiya wannan mummunar al’ada ce, don musulunci cewa ya yi ka sama mata wurin zama da duk kayan da ake bukata a gida.

Ka ciyar da ita, ka shayar da ita ka yi mata sutura, ka kuma ba ta ilimi. Duk wannan gurbacewar aure a musulunci da gudunmuwar wasu daga cikin Malamanmu. Domin musulunci ya wajabta daukar nauyin matarka, idan kuma ba ka da karfin yin auren aka ce ka dinga yin azumi, amma sai wasu Malamai suka fake da wani hadisi na idan ma ba ka da shi ka yi aure, in ba ka samu ba ka sake karawa. Suna cewar wai idan ma talauci ya yi maka yawa ka kara auren, domin Annabi Muhammad (SAW) zai yi alfahari da al’ummarsa ranar gobe kiyama.

Sai ka ga maigidancin da albashinsa ba ya wadatar da shi da iyalansa yana ta tattalin karo aure, matan kuma na shiga, sai su fara haihuwa, ‘ya’yan da sun fara tasawa, idan mace ce sai a ba Alhajin birni, idan an yi dace ta zauna, idan ba a yi ba, ta gudu, daga nan ta shiga bariki. Ka ga ba a kara zuri’ar Manzon Allah (SAW) ba, amma an kara zuri’ar karuwai, wanda kowa ya san Annabin Rahama ba zai yi alfahari da karuwai ba.

Idan kuma namiji ne, daga fita neman na abinci, ya koyo dabi’un banza na luwadi da shaye – shaye, saboda rashin tarbiyya, da sun samu sabani da mahaifinsa sai uban ya ce bar mun gidana. Ka ga nan ma ba a kara zuri’ar Manzo ba, an kara zuri’ar ’yan shaye-shaye, luwadi da ‘yan fashi da makami. Wadanda Manzon Allah ba zai yi alfahari da su ba.

Dan haka abin da mai Martaba Sarki Sanusi ya fada yake kuma da niyyar yi daidai ne. Domin a matsayinsa na Malami, adali kuma nagartaccen shugaban da ke kokarin jajircewa akan sauke nauyin da al’ummarsa suka dora masa, wanda Allah zai tambaye shi. Haka zalika kula da al’ummar sa gado ya yi daga magabacinsa, Mai Martaba Sarki Abdullahi Bayero.

A da ana zargin Sarakunanmu da rashin kula ko shiga abubuwan da suke faruwa ga al’ummar su, ba sa magana, amma a yanzu Allah ya kawo mana Sarki mai magana, tare da jan hankali akan abubuwan da suka dace, amma wasu na cewa ba daidai ba ne, saboda rashin son gaskiya da son zuciya.

A karshe ya zama wajibi ga duk abin da mutum zai yi, ya yi gaskiya, ya kuma jajirce a kanta. Ya kamata jama’a su natsu, su yi hattara akan zargin da suke yi wa Mai Martaba Sarki Sanusi, saboda jajircewa da fitowa ya fadi gaskiya.

Domin abubuwan da ya fada tunatarwa da gyara ya yi akan bin doka da Shari’a, ita gaskiya daci gareta, amma idan aka natsu aka yi nazari da kakkaifan tunani, sai masu hankali su yi kokarin gyarawa. Dama a duk lokacin da muka bar hanyar Allah, to kuwa dole za mu rinka karo da masifu kala-kala.

Don Allah (SWT) ya fada a kur’ani cewa, “a duk lokacin da kuka bar ni, to ni ma zan bar ka.” Haka zalika na tabbata a duk maganganun Sarki, idan aka tambaye shi, zai bada hujjojin da ya sa ya fadi abin da ya fada. Kuma a ganina Mai Martaba Sarki Sanusi adali ne da ke kokarin ganin ya sauke nauyin da ya rataya a wuyarsa.

 

  • Hafsat (A. M) Abdulwahid fitacciyar marubuciyar litaffan Hausa, ta rubuto daga Abuja.
SendShareTweetShare
Previous Post

RAHOTO: Rikicin Makarantar Kangere: Ba Mu Yarda Da Kalaman Kakakin ‘Yan Sanda Ba —NANS

Next Post

RAHOTO: Biyafara: Hadin Kai Muke Bukata, Ba Rabuwa Ba —Sanata Jibril

RelatedPosts

Sufeton

Jan Aikin Da Ke Gaban Sabon Babban Sufeton ‘Yan Sanda

by Muhammad
5 days ago
0

Waiwaye Game Da Manyan Sufetocin Da Aka Taba Nadawa A...

Malaman

Yajin Aiki: Malaman Jami’o’i Sun Ratse, Na Kwalejojin Fasaha Sun Tsunduma  

by Muhammad
5 days ago
0

Malaman jami’o’i a karkashin kungiyarsu ta ASUU sun ratse daga...

Gada

Gina Gadojin Sama: Ko Gasa Gwamnonin Jihohin Arewa Ke Yi?  

by Muhammad
6 days ago
0

Ra’ayoyin Kanawa Game Da Gadar Buhari Me Ya Sa Tambuwal...

Next Post

RAHOTO: Biyafara: Hadin Kai Muke Bukata, Ba Rabuwa Ba —Sanata Jibril

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version