Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Masu hikima su na cewa, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba a ke gane ta, amma a rashin kira kuma karen bebe ya ɓata. Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga Mayu, 2015, ne burin mafi yawan ’yan Nijeriya ya cika, inda a ka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban ƙasa bayan ya shafe shekara 12 ya na faɗuwa a takara guda uku da ya yi a bayan kafin wannan.
Haka nan kuma a makon jiya ne ita kanta Nijeriya ta cika shekara 57 da samun ’yancin kai daga wajen Turawan Ingilishi; lamarin da ya sanya masu nazari duƙufa wajen waiwayen baya da kuma bibiyar halin da ta ke ciki a yanzu.
Wannan dalilin ya sanya mun bi sahun ’yan uwa abokan aiki, inda mu ka yi duba izuwa ga alƙawurran da Shugaba Buhari ya yi a ranar rantsar da shi. Idan dai za a iya tunawa, jawabin nasa ya yi matuƙar birge ’yan ƙasar da ma ƙasashen duniya. Yanzu fiye da shekaru biyu kenan da ɗaukar waɗancan alƙaƙurra, inda a wancan lokaci mafi yawan talakawan Nijeriya na kallon shugaban a matsayin mai cetonsu.
“Ni Na Kowa Ne Kuma Babu Wanda Ya Mallake Ni”
A ma’anar abinda Buhari ya furta kan hakan, ya yi alƙawarin cewa, babu wasu tsiraru da za su juya shi a matsayin shugaban ƙasa, domin shi na dukkan al’ummar ƙasa ne. Ta wata sigar za a iya cewa, ya cika alƙawari, domin mun ga yadda hatta matarsa sai da ta yi ƙorafin cewa, mijin nata ba ya tafiya da mutanen su ka wahalta ma sa a lokacin yaƙin neman zaɓe. Bugu da ƙari kuma an ga yadda ya dakatar da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya da sakataren gwamnatinsa bisa zargin aikata ba daidai ba. To, amma ta wata sigar kuma ƙorafi ya yi yawa kan irin rawar da a ke zargin kawunsa, Mamman Daura, ya na takawa fadar shugaban ƙasa, inda a ke ganin ya yi babakere da yawa, ya na hana ruwa gudu.
“Ba Zan Waiwayi Baya Ba”
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, yadda wasu ke fargabar zai yi mu su bi-ta-da-ƙulli, idan ya dawo gadon mulki, to amma a ranar rantsuwa sai ya yi alƙawarin ba zai waiwayi abinda ya riga ya wuce ba. Sai dai kuma duk da cewa, wasu daga cikin manyan ƙasa irin su Janar Babangida da su ka ɗaure shi, bai sake bi ta kansu ba, to amma mun ga yadda ya kama tsohon mai bada shawara kan tsaron ƙasa, Kanar Sambo Dasuki. Kodayake dai wasu za su iya cewa, dukiyar al’umma Buhari ke son ƙwatowa daga hannun Sambon, to amma shi kaɗai ne wanda dukiyar ƙasa ke hannunsa?
“Zan Bada Haɗin Kai Ga Ƙasashen Duniya Kan Tsaro”
Tabbas Shugaba Buhari ya haɗa kai da ƙasashe maƙota da sauran ƙasashen Afrika da na duniya bakiɗaya wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Sahara, musamman ta Boko Haram, wacce ta fi addabar kowa.
Haƙiƙa Nijeriya ta rage matsalolin samun hasken lantarki da na ƙarancin man fetur, to amma dukkansu sun ƙara tsada a zamaninsa.
“Ba Zan Yi Wa Majalisa Da Kotu Katsalandan Ba”
Za a iya cewa ya cika wannan alƙawarin ma, domin tun bayan hawan Shugaba Buhari mulki a ke ganin bekensa kan yadda ya naɗe hannaye a ka samar da shugabancin majalisar da ba zai tafi tare da shi ba, kuma har kawo yanzu ya ƙi ɗaukar irin matakan da wasu daga cikin waɗanda ya gada su ka ɗauka wajen tunɓuke shugabannin majalisar da ba su jituwa da su. To, amma akwai lokutan da a ke ganin gwamnatin ta ƙi yin aiki da umarnin kotuna, kamar yadda kotu ta bayar da belin Dasuki da shugaban ƙungiyar ’yan uwa Musulmi da a ka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, amma a ka ƙi sakin su.
“Zan Sa Ido Kan Asusun Haɗin Gwiwa Na Kuɗaɗen Hukumomi”
Tun bayan Shugaba Buhari ya ɗare karagar mulkin Nijeriya, za a iya cewa, ba-ta-sauya-zani ba, domin har yanzu gwamnoni su na nan su na yin kama-karya kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi da sunan asusun haɗaka.
“Zan Farfaɗo Da Ilimi, Lafiya Da Ayyukan Ƙasa”
Wannan shi ma za a iya cewa, har yanzu ba a cika shi ba, domin nagartar ilimi da lafiya a ƙasar ba su sauya ba, duk da dai za a iya yiwa shugaban uzuri da cewa, ba abu ne da zai yiwu rana guda ba.
“Zan Ƙwato ’Yan Matan Chibok A Raye”
A na kan turba, domin an ƙwato fiye da rabinsu a raye, amma da alama akwai sauran rina a kaba, saboda har yanzu babu ɗuriyar sauran ’yan matan masu yawa.