Connect with us

NAZARI

Nazari Kan Rushe Almajiranci Da Gwamnonin Arewacin Nijeriya Suka Yi (2)

Published

on

 

Cigaba daga ranar Alhamis.

 

A rubutun farko mun tsaya ne inda muke cewa muna bayar da shawara musamman ga hukumomi da su tuntubi kwararru da masu ruwa da tsaki kan yadda za a yi gyara (Reforming) ba wai rusau ba dangane da wannan harka ta almajirci ba.

 

Dorawa daga inda na tsaya:

Kafin in kawo hanyoyin da nake ganin za a iya yin gyara (reforming) ta wannan harka ta almajiranci, ya kamata in dan bayar da haske kan yadda tsarin manhajar karatun mu na Tsangaya take, ko kuma in ce lokutan da muke yin karatun Alkur’ani a Tsangaya, don hakan ya bayar da haske kan yadda ya kamata gyaran (reforming) ya zama. Akwai abubuwa da yawa na adabin Tsangaya da mutane basu sani ba, misali banbanci tsakanin makarantar Allo da kuma Tsangaya, wanda duk Tsangaya makarantar Allo ce amma ba duk makarantar Allo ce Tsangaya ba.

Wato kenan ita makarantar Allo tana iya zama wata karamar makaranta wacce yara ‘yan gari suke zuwa su koyi Alkur’ani da safe da kuma yamma ko kuma da daddare, ko kuma da yamma kawai, kuma ba dole ba ne ya zama ita makarantar tana fitar da mahaddata. Amma ita Tsangaya kamar jami’a ce a tsarin karatun boko, kuma ita Tsangaya sha-kundum ce, a nan ake tarbiyyantar kotso da kolo da Titiburi da Gardi da Alaramma da Gwani, a takaice ba a wuce Tsangaya a tsarin almajiranci.

To, a yadda lokutan karatun mu yake (Time Table) a Tsangaya, muna yin karatun Alkur’ani na kwana biyar a sati, kuma a kowacce rana muna yin zallar karatun Alkur’ani na awa 9 ko 10, wannan in ba a lissafa da abin da muke kira da ja-dare da kuma Tashe ba wanda su wannan ja-dare da kuma Tashe su ne za ka iya kiran su da ‘edtra curriculum’ a tsarin boko, sannan ga wadanda sukai Boarding shine abin da za ka iya kira da ‘Prep’. Banda wadanda su ba abin da ke raba su da karatun Alkur’ani sai cin abinci, sallah, da yin bacci dan kadan da wasu uzurori na dole (Buna). Amma duk da haka, duk wanda ya iya samun haddar Alkur’ani mai kyau a shekara shida (6) to ba karamin hazikin gaske bane. Ban da taimako kala-kala na rubutun sha da addu’o’i da ake yi ana sha duk don neman taimakon Allah kan samun saukin yin haddar.

Hanyar farko ta kawo gyara ita ce: Gwamnati ta inganta wadancan makarantun nata na haddar Alkur’ani (Tahfeez, Tsangaya Models) ta hanyar inganta manhajar karatun su ta yadda za a gani a fili cewa makarantun suna fitar da mahaddata Alkur’ani gogaggu. Wanda a wannan dole a yi la’akari da cewa tunda a makarantar Allo ko Tsangaya ana yin karatun Alkur’ani na awa 9 ko 10 a kowacce rana, to yanzu a wannan tsari na zamani wanda ake so a koyar da turanci ko lissafi ko kimiyya misali, awa nawa za a ware musu kuma awa nawa za a baiwa shi Alkur’ani (Time table allocation), wanda ya kamata Alkur’ani kenan ya sami kamar awa 6 ko 7 a kowacce rana. To idan mutane suka ga wadannan makarantun an inganta su kuma ana yin haddar Alkur’anin to da kan su za su dinga kai ‘ya’yansu ba tare da tursasawa ba.

Hanya ta biyu: Samar da bangaren Tajweed a dukkan fadin Arewacin Nijeriya irin wadda aka kafa a Kano a 1985. Wadda ita kanta ta Kano din a iyakar bincike na ba a kara samar da irin ta ba har yau din nan. Wanda da a ce akwai su a jihar Kano da yawa, to da Alarammomin mu da yawa za su shiga kuma tunda karatu ake yi zai yi tasiri kan alarammomin wajen yaran da suke koyarwa ta fuskoki da dama. Ita ba wanda za a dauka sai Alaramma sai ya yi shekara (4) a ba shi takardar Sakandire. Ko haka ya tsaya an ci gaba balle ma zai iyu daga nan ya wuce jami’a.

Hanya ta uku: Tunda kuna tausayin yara tare da kokarin kare musu hakkinsu a matsayin su na manyan gobe, sannan kuma tunda gwamnatocin Arewacin Nijeriya bara ce ba sa so ba wai karatun Alkur’ani ba, to su samar da makarantun Alkur’ani na su wadanda za su koyar da Alkur’ani zalla su dauki dalibai ‘yan asalin jihohin su da malamai, sai su kula da su ta hanyar ciyar da su ba tare da sun je bara ba. Idan jama’a musamman almajirai suka ga haka kuma suka lura ana yin haddar Alkur’anin to ba sai ka fada musu cewa kada su kai ‘ya’yansu waccan mai barar ba.

Da kan su za su canja zuwa ga wacce hukumomi suka samar. Musamman da yake duk dan kasa yana da hakkin a ba shi ilimi a matakin farko na shekara 9, to ku yi musu manhaja wacce za ta koyar da su Alkur’ani zalla ku rakaba musu da koya sana’a na shekara 9, (9 Year Basic Education), don haka wanda shi ilimin Alkur’ani ya zaba sama da wanin shi to hakkinsa ne a ba shi.

Hanya ta hudu: Gwamnatocin mu na arewa su kira masu tafiyar da wadannan makarantun ko ta hanyar kungiyoyin su ko manyan malaman su, sai a ba su horo a matsayin taron karawa juna sani, sai a nuna musu illolin bara da yaran mu masu karatun Alkur’ani suke yi, musamman in an kalli girma da darajar littafin, ya kamata a ce mai karanta shi ya zama ya wuce a ce sai ya yi bara zai ci abinci.

To sai gwamnati ta ba su dokoki da ka’idoji na cewa duk wanda yake son ya ci gaba da gudanar da makarantar Allo ko Tsangaya to dole ya bi wadannan dokokin. Misali sai a ce; a) dole ya zama dalibai da za a karba daga garuruwa ya zama kada su yi bara, sai dai iyayensu su dauki nauyin su. b) Dole kafin a karbi yaro ya zama ya kai wasu shekaru (kaza), da dai sauran ka’idoji wadanda kwararru za su bayar da su don inganta harkar.

Hanya ta biyar: Ko gwamnatoci na sane da cewa akwai makarantun Alkur’ani da yawa a yanzu wadanda kwata-kwata yara ba sa zuwa bara? In ba su sani ba to muna sanar da su akwai, in kuma sun sani to ya akai suka rufe su? Ina so ne in ce za a iya amfani da su a matsayin na gwaji, a kira su a tattauna da su sai a ji tsarin da suke tafiya a kan shi ta yadda ya zama yaran su ba sa zuwa bara, sai kawai a yi kokarin fadada shi da kuma taimakon tsarin, amma fa sai in barar ce ba a so za ai hakan.

To, Ina ganin wadannan sune wasu daga cikin hanyoyin kawo gyara a wannan harka. Domin mun ka sa samun nutsuwa kan cewa barar a ka nufa da hanin ba wai shi littafin Allah mai girma ba, musamman lura da cewa ana bara a manyan titunan jihohin da aka hana almajiranci, kuma matasa ne da manyan mutane maza da mata ke yin wannan barar, sannan ana bara a ofisoshin gwamnati ta hanyoyi da dama, yara wadanda ke gaban iyayen su suna zuwa bara a danjoji saboda halin kaka-nakayi da aka sanya iyayansu ciki, ana bara a gidajen Rediyo kan rashin lafiya, daliban manyan makarantu suna bara a gidajen Rediyo don a biya musu kudin makaranta, wanda wasu mata ne ma ke yi, wanda hakan ka iya zama wata sila ta lalacewar tarbiyya.

Amma duk wadannan nau’o’in bara ba a hana ba wacce aka hana ita ce ta yaro karami wanda yake karanta Alkur’ani. Sannan daga cikin dalilan da suka ba mu rashin nutsuwa, akwai makarantun Alkur’ani a Kano da yara ba sa bara amma abin mamaki wannan haramcin bai tsame su ba, yaa ilaahi to me ake nufi kenan?

A ilimin manhaja, akwai abin da a ke cewa ‘Future Curriculum’, shi wani fanni ne da yake kallon abin da ya wuce dangane da manhaja da kuma yanayin da ake ciki yanzu, sai a yi hasashen abin da ka iya faruwa nan gaba akan asasin bincike da ka’idoji. To a kan asasin wannan fannin za mu iya hasashen cewa; in har gwamnati ta iya nasara wajan hana wannan almajirancin da ake magana maimakon gyara shi to zai iyu daga yanzu zuwa shekara 100 masu zuwa a rasa mahaddacin Alkur’ani a Arewacin Nijeriya, ko kuma su zama ‘yan kadan sosai in har an samu.

 

Zan kammala a karo na gaba in sha Allah!

Goni Abdullahi ya rubuta tare da aiko mana daga karamar hukumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano. Za a iya riskarsa a mtabdullahi33@gmail.com +2348039710618. Goni dalibi ne da ke samun kwarewa kan nazarin manhajar karatu da koyo da koyarwa a matakin digiri na uku (Ph.D).
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: