Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Nazari Kan Yadda INEC Ta Gudanar Da Zaben 2019

by
3 years ago
in NAZARI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

Duk da kokarin da Hukumar zabe ta kasa(INEC) ta yi na tabbatar da cewa an gudanar da zabe mai tsafta kuma cikin kwanciayar hankali da luma a zabuka da aka yi na wannan shekara ta 2019, sai dai kokarin na Hukumar zaben ya ci karo da matsala daga wasu bata-garin ‘yan siyasa, wanda hakan ya jefa Hukumar cikin halin tasaka-mai-wuya, SUNDAY ISUWA ne ya rubuta labarin wanda EDITAN LEADERSHIP A YAU ASABAR, SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI ya fassara da Hausa domin amfanin masu karatunmu. Ga kuma yadda fassarar ta kasance:
Tun farko Hukumar zabe ta shirya yin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya ranar 16, ga watan Fabarairu, 2019, sannan kuma na gwamnoni da majalisun dokokin jihohi da na Birnin tarayya ya biyo baya ranar 2, ga watan Maris 2019. Amma sai Hukumar da tsinci kanta a cinkin halin rashin wadataccen kudin da za gudanar da wadannn zabu, wanda hakan ta sa dole Hukumar ta sanar da dage zabukan ana gab da za a fara. Da yawa daga cikin ‘yan siyasa da ‘yan takara da masu ruwa da tsaki da masu sa-ido a harkokin zabe na ciki da wajen kasar nan sun gamsu da dalilan da INEC ta bayar na dage wadannan zabuka, domin sun fahimci cewa, Hukumar ta yi hakan ne domin ta tabbatar da cewa, an gudanar da ingantaccen zabe.
Haka kuma da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya wadanda suka yi fushi lokacin da INEC ta sanar da dage zaben sun huce, yayin da suka fito domin jefa kuri’arsu a sabuwar ranar da Hukumar ta sa, wato ranar 23, ga watan Fabarairu 2019, inda suka zabi shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da kuma ranar 9, Maris inda suka zabi gwamnoni da ‘yan majlisar jihohi da kuma zaben da aka yi a Birnin tarayya Abuja. Jama’a sun fito sosai a dukkan fadin kasar nan a zaben shugaban kasa. Bayan kammala wannan zaben ne sakamako ya nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, shi ne ya samu nasarar lashe zaben da kuri’a 15,191,847, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP day a biyo bayansa da kuri’a 11,262,978. An dan samu wasu matsaloli a wasu wurare wanda ko dai gazawa irin ta dan’adam ta haifar da su, ko kuma an yi su dagangan ne. Saboda inda aka samu irin wadannan matsaloli, sai INEC ta yi amfani da karfin da doka ta ba ta, ta soke zabukan wuraren. Yin hakan sai ta adan takara daga jam’iyyar adawa ta APC da jam’iyyar ta APC suka garzaya kotu suna kalubalantar wannan soke zabe da INEC ta yi. Ranar Asabar 9, ga watan Maris 2019, miliyoyin ‘yan Nijeriya suka fito domin zaben gwamna a jihohi 29, da zaben ‘yan majalisar tarayya 991 a dukkan jihohin da ke fadin kasar nan da ciyamomi 6 da kansiloli 62 da ke Birnin Tarayya Abuja. Duka-duka an zabi ‘yan takara 1,082 a dukkan fadin kasar nan, sai dai a wasu jihohin da mazabu an cim karo da matsaloli wadanda suka sa dole INEC ta bayyana cewa, zaben irin wadannan wurare bai kammala ba.
Ganin yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa, sai ya zama darasi ga INEC, inda ta yi kyakkyawan shiri domin fuskantar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi. Saboda haka an kai dukkan kayan zabe jihohi da Birnin tarayya a kan lokaci, wadanda kuma aka kai su dukkan kananan hukumomin da aka yi wadannan zabuka kan lokaci, saboda kayan zabe sun isa kowace mazaba ba tare da wata matsala ba, wanda ta sa aka bude kowace mazaba tun misalign karfe 8.00ns.Bayan zaben da ka gudanar a mazabu 1,082 da ke fadin kasar nan, INEC ta gudanar da wasu zabukan a gundumomin majalisar dattawa 7 da mazabun ‘yan majalisar tarayya guda 24 da ke jihohi 14. An dagula zabe a irin wadannan wuraren ta hanyar tayar da hankali ko sace akwatu ko kame jami’an zabe ko aringizon kuri’u ko kuma bajirewa dokokin zabe. Yawan kuri’un da aka samu a irin wadannan mazabu sun fi yawan masu zabe. Saboda haka ya zama wajibi a soke zaben irin wadannan wurare a sake wani zaben domin tabbatar da adalci. Saboda haka Hukumar ta yanke shawarar gudanar da irin wadannan zabuka na majalisun tarayya a lokaci daya da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.A zaben gwamnoni Cibiyar bunkasa Dimokaradiyya (CDD), da Cibiyar Nazarin zabe (EAC) sun bayyana wasu jihohi guda tara da suka ce za a yi gumurzu a zaben gawmnonin. CDD ta bayyana Legas da Kano da Kaduna da Imo da Adamawa da Ogun da Filato da Bauchi da kuma Sakkwato a matsayin jihohin da za a yi kare jinni biri jinni a zaben gwamnonin. Daga cikin wadannan jihohin, Kano da Adamawa da Plateau da Bauchi da kuma Sakkwato su ne jihohin da aka ce ba a kammala zabe ba.Kodayake masu fashin baki ba su ambaci jihar Benuwai ba a cikin jihohjin da za fafata ba, amma ita ma tana cikin jihohin da ba a gama zabe ba.
Saboda za a sake zabe a wasu mazabu a wadannan jihohi shida ranar Asabar 23, ga watan Maris 2019. An bayyana zaben da aka yi ranar 9, ga watan Maris 2019 na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da na ciyaman na majalisar Birnin tarayya da kansilolinsa a matsayin zaben da ked a matukar muhimmanci, saboda kusancinsu da jama’a. “ Gwamna na da matukar muhimmanci domin yana da cikakkiyar damar da zai tabbatar da tsaro ko kuma ya yi sakaci a jiharsa,” Dakta. Joe Abah, mai fashin baki ne EAC kuma Darakta a Sahin bunkasa harkokin wajen Tarayyan Turai a Nijeriya ya ce. “Babban kalubalen da ke fuskantar samun kyakkyawan shugabanci a Nijeriya shi ne, da yawa daga cikin gwamnoni na karbar cin-hanci ba sa kula da aikinsu, sannan kuma ba sa zama a jihohinsu ballantana su san matsalolin da ke damun al’ummarsu,” Abah ya ce, ya kamata al’umma su dinga kula da abin da gwamnoninsu ke yi. Koda yake dai an yaba wa INEC bisa magance matsalolin da ta fuskanta a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya, saboda haka matsaloli kadan aka samu wajen gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da na Birnin tarayya. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Aka Yi Tataburza A Zaben Jihar Kaduna

Next Post

Babban Kalubalen Da ke Gaban Sabuwar Majalisar Tarayya

Labarai Masu Nasaba

Dariye Da Nyame

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
4 weeks ago
0

...

Bangaranci

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

by Muhammad Maitela
2 months ago
0

...

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

by
3 months ago
0

...

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by
7 months ago
0

...

Next Post
Majalisa Ga Gwamnati

Babban Kalubalen Da ke Gaban Sabuwar Majalisar Tarayya

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: