Zuba hannun jari a kiwon Jima, na daya daga cikin damar da ake samu a bangaren kiwon a wannan kasa, domin samun riba mai tarin yawa.
Wannan na faruwa ne, sakamakon yadda ake ci gaba da nuna bukatar kwan na Jimina da gashinta a kasar da kuma fadin duniya baki-daya.
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
- PENGASSAN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Fara
Jimina, ta kasance babbar tsuntsuwa a duniya, sannan wadda take tashi sama, ta kasance kuma ta na yin kwai mai yawan gaske tare da samar da nama mai yawa.
Kazalika, wasu na ganin cewa a kiwon Jimina, an fi samun kudade masu yawa fiye da na kiwon Shanu, musamman duba da cewa; Saniya na haihawa ne sau daya a shekara, kuma sai ta shafe kusan shekara biyu bayan ta girma kafin a kai ta kasuwa a sayar, sabanin Jimina; wadda ke yin dubban kwai a duk shekara guda da kuma tsakanin wata sha hudu, kazalika kuma ‘ya’yan da suka kyankyashe na saurin irin girman da ake bukata, har a kai kasuwa a sayar.
Ga wanda zai fara kiwonta, ana bukatar ya tanadi wadatacen wajen kiwo, inda ko da sun kasance sun mallaki musamman gonar da za su kiwata ko kuma su yi hayar gonar, domin Jimina tsuntsuwa ce da ke da bukatar waje mai girma, ta yadda za ta rika watayawa yadda take bukata.
Haka zalika, ana bukatar mai kiwon ya tabbatar da ya katange wajen kiwata ta duba da cewa, Jimina tsuntsuwa ce da ke da karfin gaske, inda kuma ake bukatar masu son kiwata ta, su tabbatar da sun tanadar mata dakin kwana, domin ba ta kariya daga zafin rana.
Bugu da kari, ana bukatar masu son kiwata ta; su tabbatar da sun dauki hayar leburorin da za su rika ba ta kulawa, sannan kuma dole ne su kasance sun san halayenta da tsarin yadda ake ba ta abinci da kuma da jin dadinta.
A nan, ana bukatar masu kiwonta su yi hayar kwararrun da suka iya sanin yadda ake tafiyar da kiwon manyan tsintsaye.
Haka zalika, ana bukatar masu son kiwon nata su samo ingantacciyar Jiminar da ya kamata a kiwata, musamman wajen sayen ta daga wurin wadanda suka amince da su, kuma Jiminar ba ta dauke da cututtukan da ka iya gagarar yin magani.
Haka nan, kwanta; wanda ba a kyankyashe ba, ya fi saukin saye, wanda hakan ya sanya masu bukatar zuba hannun jari a kiwonta, suka fi bukatar sayen ‘ya’yan Jiminar wadanda ba su wuce wata uku ba, inda suke sayen mace da namiji, domin fara kiwata su a dan karamin wajen kiwo.
Kwanta daya a kasuwar duniya, na kai wa kimanin dala 500, inda kuma ake sayar da Jiminar da ke da rai a kan kimanin dala 5,000.
Naman jimina daya, na kai wa kimanin kilo 1,800, idan aka kwatanta da wanda ake ake samu a Saniya, wanda ya kai kimanin kilo 250.
Sannan kuma, ana bukatar a rika kula da wajen kiwata ta a kowace rana, kamar cire duk wata shara da kuma kawar da duk wani abin da zai iya ji mata ciwo da sauran makamantansu.
Har wa yau, Jimina na yawan shan ruwa a kullum, saboda haka; akwai bukatar a rika tanadar mata ruwa mai yawan gaske, wanda zai iya isar ta.
Ana kuma bukatar masu kiwonta, su samar da wajen da za su rika noman ciyawar da za su rika ciyar da ita, domin samun sauki.
Kazalika, ana samun namanta a manyan shaguna da sauran manyan gidajen sayar da abinci da kuma sauran wurare.
Bugu da kari, fannin kiwon Jimina a kasar nan, na kunshe da wasu manyan kalubale, musamman ga wadanda suke sabbi wajen fara kiwon ta, wanda daga cikinsu; akwai karancin ilimi kan yadda ake gudanar da kaiwon nata da kuma rashin sanin yadda suke yin kwai da samun kwararrun likitocin da ke duba lafiyarta.
Kazalika, zagaye wajen kiwon nata na daya daga cikin manyan kalubale, musamman duba da cewa; zagayen gonar da za a, abu ne da ke bukatar kudade masu tarin yawa tare kuma da kalubalen tanadar abincin da za a rika ciyar da ita.