Nazari Kan Yunkurin Gwamnati Na Haramta Almajiranci A Kasar Nan 

 

mahawayi2013@gmail.com,

Mai karatu yau ma dai cikin ikon Allah mun sake saduwa a wannan shafi da muke yin tsokaci game da abubuwan da ke kaiwa da komowa a wannan kasa ta mu, musamman a nan Arewacin Nijeriya, inda a makon da ya gabata muka fara magana game da shirin da gwamnatin Shugaba Buhari ke da shi na hana bara da almajiranci.

Kamar dai yadda kowa ya sani, wannan batu ya samu harshen damo a tsakanin jama’a, wanda wasu suka yaba wa shirin bisa la’akari da irin bakin jini da tozartar da wannan bara ke jawo wa al’ummar musulmi, yayin da wasu kuma ke ganin ai wannan yunkuri na gwamnati bai yi daidai ba, inda suke ganin tamkar fada ne da addini.

Ko ma dai mene ne, lallai wannan abu yana da matukar muhimmanci a duba shi da idon basira, a yi masa kallo na zahiri. Domin kamar yadda na fada a rubuce-rubucena da suka gabata, musamman wanda na yi a makon da ya gabata, za mu ga cewa ko da wannan almjiranci na da amfani ga yaro, to lallai kam rashin amfaninsa ya fi yawa, bisa la’akari da irin tagayyara da shiga munanan halayen da wannan abu ke jefa yaranmu a ciki.

Domin a gaskiya wannan abu ya zama tamkar wani bala’i ne, inda za ka ga yaro karami yana bara, wanda zai iya yin duk wani aiki na karfi, duk da kuwa a yanayi irin nasa, kamata ya yi a ce yana makaranta don neman ilimin da zai amfane shi duniyarsa da lahirarsa, amma abin takaici babu ko daya, bai tafi makarantar Islamiyyar ba balle ta boko, ta allon din ma ba karatun yake yi ba.

Wasu daga cikin wadannan abubuwa, wadanda kuma zan iya cewa babu wani mai farin ciki da su, shi ne yadda za ka samu kananan yara masu kananan shekaru suna bara a kan tituna, musamman a wasu manyan garuruwan kasar nan, wasu da sunan ’yan makarantar allo, wasu kuma barar kawai suke yi don neman kudi.

Kamar yadda na fada a wani rubutu nawa da na yi cewa magance wadannan abubuwa dole sai Hukumomi, iyaye da sauran al’umma sun tashi tsaye wajen kawo karshensu, domin idan abin ya ci gaba da tafiya a haka, to ba zai haifar wa akibar kasar nan, musamman Arewa da mai ido ba.

Masana da sauran masu lura da al’amuran da ke kaiwa da komowa a kasar nan suna ganin cewa kara samun karuwar kananan yara da ke gararamba a titunan kasar nan da sunan yin bara ko almajiranci, musamman a Arewacin Nijeriya, to lallai akwai babbar barazanar tsaro da sanya fargaba a tsakanin jama’a.

A yunkurin da take yi don ganin an kawo gyara a wannan abu, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dade tana kama almajirai, amma sai ya zama abin kamar ba a yi, domin abubuwan sai kara karuwa suke yi, musamman a Kon din.

Har ma akwai lokacin da shi Babban jami’in sashen yaki da bara na Hukumar ta Hisbah, Shaikh dahiru Nuhu ya ce yanayin da suke ganin kananan yaran da ake kawowa bara a birnin, abin babban tashin hankali ne, wanda a nan gaba zai iya zama babbar masifar da ba a taba gani ba matukar mahukunta ba su dauki mataki ba.

Duk idan ana wannan batu na bara da almajiranci hankula su kan koma ne a birnin Kano, inda nan ne ke zama matattara da ake kawo yara daga sassa daban-daban domin yin bara.

kididdiga ta nuna cewa kananan yara fiye da Miliyan daya ne a Nijeriya ba sa zuwa makarantar boko ko ta addini, kuma akasarinsu na yawon barace-barace ne a tituna, musamman a manyan biranen Arewacin kasar nan.

Bincike ya nuna cewa yawon bara a tsakanin kananan yara na daga cikin manyan kalubale da ke addabar Arewacin Nijeriya, kuma lamarin ya ki jin magani duk da illar hakan a tsakanin al’umma. Wannan ne ya sa a saman wannan rubutu na ke cewa wajibi ne sai kowa ya shigo cikin wannan lamari ne sannan za a sami gyaran da ya dace a ciki, domin ba abu ne da za a barwa gwamnati ita kadai ba, wajibi ne a hada karfi da karfe.

Misali, wasu jihohin kasar nan, kamar Kano da Kaduna sun yi dokokin hana bara da suka tanadi kama almajirai, a Kano ma dokar ta tanadar da har da kama Malaman yara masu barar, amma har yanzu matsalar ba ta ragu ba, maimakon haka ma kara gaba-gaba take yi.

Irin matsalolin da wannan bara da watangaririyar kananan yara a tituna ne suka sa gwamnatocin jihohin Kano da Kaduna suka haramta barace-barace, kuma tun bayan fara aikin wannan doka a Kano, an kama dubban almajirai, amma abin bai magantu ba.

Abin da ya sa a saman wannan rubutu na yi bayanin cewa magance wannan matsala ba aiki ne na mutum daya ko gwamnati ita kadai ba, shi ne duk da cewa Hukumomi a jihar Kano sun yi dokar haramta yin barar nan, musamman ta kananan yara, amma a yanzu ana kara samun yawaitar kananan yaran da ke gararamba ne a birnin da sunan yin bara.

Irin wadannan yara sukan bar inda aka kai su domin karatu, su dinga yawo kwararo-kwararo, a wasu lokutan ma sukan kwana a titi ko karkashin gadoji, lamarin da a yanzu ya fara jan hankulan mutane da ke ganin cewar matukar ba a dauki mataki ba, to fa matsalar za ta iya gagarar kowa, har ma takan iya gawurta fiye da inda ba a zata ba.

Baya ga wadannan matsaloli, su kansu yaran sukan fada cikin wata muguwar hanya ta lalacewa, wajen shiga munanan abubuwa na sace-sace, ta’addanci da dai sauran munanan halaye. Kamar yadda a kwanakin baya kafafen yada labarai suka ruwaito cewa an kama wani Malamin irin wadannan makarantu yana yin luwadi da almajiransa. Irin wadannan abubuwa suna nan birjik.

Wani abin dubawa a cikin wannan harka ita ce sau da dama irin wadannan almajiran kan fada cikin ha?urran rayuwa iri daban-daban, kamar yadda na tabbata kowa zai iya kawo misalai a irin wadannan hadurra da wadannan yara kan fada. Wasu su fada hannun matsafa, wasu fada hannun lalata yara, wasu kuma fada hannun masu aikta miyagun halaye daban-daban.

A kwanakin baya sami wani yaro da ya bata a Kano, wanda ya ce an kai shi Kano ne domin almajiranci, ya ce sunan kauyensu Daburam, amma bai san a cikin jihar da yake ba, ya shafe sama da mako daya yana kwana a titi. Har yake cewa a lkacin da ya tafi bara ne ya bata, shi ne yake shinfida leda yana kwana a kai.

To amma duk da munin wannan abu, kamar yadda na fada a makon da ya gabata, su alarammomi da ke ajiye irin wadannan yara suna tura su bara sun fara nuna cewa ba za su yarda da duk wani yunkuri na dakile barar da ake yi ba, suna ganin cewa barar tamkar wani bangare ne na addini, su kuma ba za su yarda da cewa bara ta saba wa addini ba, don haka dole a kyale su su wataya kamar kowa.

Shi ma fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Shaikh dahiru Usman Bauchi ya yi nuni da cewa batun hana bara a Nijeriya ba abu ne da ya dace ba, inda yake cewa kokarin kafa dokar hana barar nan zalumci ne.

Shaihin Malamin ya ce bara tana da asali a tarihin Musulumi, haka nan kuma bara wata hanya ce da marasa shi ke bi domin neman taimako wurin wadanda Allah ya hore ma. Don haka ne ma Shaihin ya yi zargin cewa Nasara ne ke kallon bara da irin wannan mummunar fuska domin hakan bai yi daidai da muradinsu ba.

Ni kuma ina kara jawo hankalin masu karatu cewa yana da kyau a gane cewa, kamar yadda na yi bayani a sama, wannan abu yana da mahangar jama’a daban-daban, kowa da yadda yake kallon abin, kuma kowa da yadda yake ganin yadda za a kawo karshen abin. Don haka kowa ya ba da tasa gudumawar wajen gyaran wannan labari.

Za a iya aiko da shawarwari ta i-mail dinmu na mahawayi2013@gmail.com ko leadershipayaulahadi@gmail.com.

Exit mobile version