Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Nazari: Wasu Dalilan Da Ke Jefa Maha’inta Cikin Harkokin Tsafe-tsafe Da Sassan Jikin Mutane

by
2 years ago
in NAZARI
4 min read
Nazari: Wasu Dalilan Da Ke Jefa Maha’inta Cikin Harkokin Tsafe-tsafe Da Sassan Jikin Mutane
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

Mai bibiyar wannan rubutu, a fitowa ta da ta gabata, an fara bincina wasu daga dalilan dake sanya marasa tsoron Allah tsunduma cikin sabgar yin tsafi da sassan jikin al’uma ne musamman Kananan Yara. Son kudancewa nan da nan, da son samun wata daukakar da, amfaninta kawai zai gudana ne cikin wannan kukuntacciyar rayuwa ta Duniya, mai kama da kiftawar-ido. Na daga sha’awe-sha’awen dake fizgar jama’a zuwa ga wadancan halaye ne Satar Kananan Yara da masu nakasa, kamar masu Kusumbi, a na kai su garuruwan yammacin wannan Kasa a na badda su daga doron kasa.

“…Such rituals are reportedly motibated by the belief that they can bring power and wealth to an indibidual…”
(Leadership, April 30, 2012 ; Punch, August 10, 2012).
Maganar da za a rika yawan ji a bakin al’uma cewa, a duk sa’adda lokutan Zabuka suka karato cikin wannan Kasa, a kan sami labarin sace mutane musamman Kananan Yara, irin wadanda ‘yan kabilar Ibo ko a ce Inyamurai-Kiristoci suka sami nasarar sacewa daga nan garin Kano, tare da yin safarar su zuwa can garin Onitsha ta jihar Anambra, na neman zama gaskiya, duba da wancan labari da Jaridar Leadership da ta Punch da suka hakaito.
Cikin waccan labari da jaridun suka bayar, an ce;
“…An gabatar da tarin rahotannin dake nuni da cewa, daga ababen dake taimakawa zuwa ga tsunduma cikin sabgogin tsafe-tsafen nan da ake fama da su shi ne, imani da wasu ke da shi na cewa, surkullen, kan taimaka ainun wajen samun MULKI da tarin NAIRORI a rayuwa…”.
Har ila yau;
“… And protect them from business failure, illness, accidents and spiritual attacks…”.
(Daily Trust, June 21, 2010).
Sai dai kawai Allah Ya taimaka Ya kwaci Talaka daga sharrin wadannan Matsafa. Cikin tsinkayen Jaridar Daily Trust da aka gabatar a sama, ita ma tana bayani ne game da karin dalilai na-bata dake sanya Barayin Mutane Matsafa yin la’akari da alfanunsu da za su girba, a cikin rayuwarsu ta nan gidan Duniya.
Daga ababen da wasu fandararrun mutane ke matukar yin imani da su cewa za a amfana, daga wadancan sabgogi na tsafi, da Jaridar Daily Trust ta ruwaito a sama, ga su kamar haka;
“…Matsafan, sun yi imani da cewa (ta hanyar tsafin) harkokinsu na kasuwanci za su bunkasa ainun ba tare da samun wani kazgaro ba, za kuma su sami cikakkiyar kariya daga rashin lafiya, ko hadarin mota, sannan, babu su babu haduwa da farmakin Shaidanu…”.
Idan dai irin wadancan mushen tunani Matsafan ke da shi, babu laifi a ce Talaka na tsaka-mai-wuya, sai dai kawai fatan Allah Ya tsare shi.
Ba wai Kananan Yara ba, a’a, shi ma mai Kusumbi da Ahalinsa, a rika kafa-kafa da shi, kamar yadda aka gabatar cikin fitowa ta 14 cewa, a na kama shi (mai kusumbi) a kashe, a yanke kusumbin da wuka, sannan a yi aiyukan tsafi da shi.
Hakika an farmaki masu Kusumbi a garuruwan Kudanci da na Arewacin wannan Kasa tsawon lokaci babu kakkautawa.
An farmaki masu Kusumbin tare da karkashe su, cikin garuruwa kamar haka;
A Babban Birnin Jihar Ondo, Cikin Shekarar 2012
(Leadership, April 30, 2012).
A Jihar Kogi, Cikin Shekarar 2010
(Daily Independent, February 24, 2010).
A Jihar Osun, Cikin Shekarar 2009
(ThisDay, October 27, 2009). Sannan,
A Cikin Wasu Karin Jihohi Na Kudancin Wannan Kasa
(Sahara Reporters, July 3, 2012).
Cikin wasu rahotannin ma, za a iske cewa, wasu daga cikin Matsafa da Bokaye tare da wadansu fitattun mutane a wannan Kasa, na game-baki ne da masu kula da MAKABARTU, wajen samun sassan jikin MUTANE, don yin TSAFI da su.
Ga wanda ke biye da wannan rubutu tun farko, ya kwana da sanin a na magana ne game da sace Kananan Yaran al’umar garin Kano ne da wasu Inyamurai-Kiristoci suka yi, tare da canja musu sunaye da addini da sukan yi, a duk sa’adda suka sami nasarar sace sun, bayan danganewa da su zuwa ga jihar Anambra. Akwai wasu rubuce-rubuce da wasu daidaikun mutane gami da wasu Kungiyoyi suka gabatar, suna masu kalubalantar wasu dake bigen nuna kansu a matsayin masu karajin-kare-hakkin al’umaa Najeriya, amma sai suka zama kuramen-karfi-da-yaji, lokacin da jama’ar Kano ke cikin mummunan yanayin alhinin sace musu Yara da Inyamurai-Kiristoci suka yi. Ko me ya sa?
Masu Karajin Kare Hakkin Dan’adam Sun Shamuke
Wani abin ta’ajibi bayan faruwar sace-sacen Yaran Kanawa Hausawa da aka sami ‘yan Kabilar Ibo da shi, a cikin jihar Kano, sai aka nemi jin mabanbantan muryoyin masu ikirarin gwagwarmayar kare hakkin DAN’ADAM aka rasa. Sai suka yi layar-zana. Ko don saboda yawancin ‘yangwagwarmayar a yau, sun fi mayar da hankali ne ga babatun da ake kamfatar Daloli ko Nairori ne a karkashinta?.
Me ke samun Kungiyoyin ‘yangwagwarmaya da daidaikunsu ne a yau cikin wannan Kasa?. Bai dace a ce, a na tunanin irin wadancan ‘yangwagwarmayar na da ilmi da wayewa, amma sai suke yunkurin kabilantar da gwagwarmayar! Eh mana, abubuwan da ba su kai munin sace yaran na Kano ba, sun faru a cikin sassan wannan Kasa, amma nan da nan, sai a fara jin muryoyin wadancan masu kumaji suna ta kai-kawo, amma batun Sace Yaran Kano, sai irin wadancan muryoyi suka yi tsit abinsu.
Ko don sace Yaran na Arewa Musulmi na Kano da aka yi, ba daga Kudu ne suka fito ba? Saboda su ba yaran Kudu ne ba Kiristoci, shikenan an saci banza ke nan?. Akwai zarge-zarge iri-iri da za a ga a na tuhumar Kungiyoyin Kumajin da Daidaikunsu game da wannan batu na sace Yaran Kanawa.
“… We are miffed by the attitude of some members of Cibil Societies and Human Rights Actibists. They raise hell and brimstone when a single Christian is inbolbed in what looks like a denial, but look the other way when thousands of Muslims are depribed. This is selectibe actibism. It is sheer playing to the gallery”.
Muric
Kungiyar MURIC, “Muslim Rights Concern”, wadda ke fafutikar kwato hakkin Musulmi ce ta yi wancan tsokaci na sama. Tsokacin, na yin tir ne da halayyar mursisi da wasu Kungiyoyi suka nuna, na yin burus da sace Yaran Kanawa da Inyamurai suka yi a jihar Kano, ba tare da an ji amonsu ba, kamar yadda aka saba ji, a duk sa’adda wani yanayi ya afku, dake nuna turmushe hakkin Dan’adam karara a fili. Ga fassarar kalaman Kungiyar ta Muric kamar haka;
“… Babu shakka ko kadan ba mu ji dadin halayyar da irin wadancan Kungiyoyi na Al’uma da Kungiyoyin fafutukar kare hakkin Dan’adam suka nuna ba (game da sace Yaran Kano). A fili yake cewa, sukan tashi-kura ainun, a duk lokacin da aka yi kokarin tauye hakkin Mutum Kirista guda daya jal. Amma gashi an tauye hakkin dubban Musulmi amma sun basar ko a jikinsu! Babu shakka, irin wannan gwagwarmaya, cike take da halayyar son-kai da son-zuciya. Irin wadannan Kungiyoyi, na cike ne da farfaganda ta banza a tsakanin al’uma”.
Kungiyar ta cigaba da cewa;
“…Nigerian will recall the hullabaloo that followed the Ese Oruru Saga in March 2016. Where are the adbocates of girl-child rights who nearly bought down the ceilings of heaben ober a mere case of elopement? Where are the human rights lawyers today?”.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Muhimman Harkokin Dake Faruwa Tsakanin Sin da Nijeriya A Shekarar 2019

Next Post

Ire-Iren Fassarar Da Ake Wa Kalaman Kiyayya

Labarai Masu Nasaba

Dariye Da Nyame

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
4 weeks ago
0

...

Bangaranci

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

by Muhammad Maitela
2 months ago
0

...

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

by
3 months ago
0

...

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by
7 months ago
0

...

Next Post
Ire-Iren Fassarar Da Ake Wa Kalaman Kiyayya

Ire-Iren Fassarar Da Ake Wa Kalaman Kiyayya

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: