Rahotanni daga ko’ina a fadin kasar nan na ci gaba da bayyana yadda manyan biranen kasar nan ke ci gaba da fuskantar matsaloli da kalubale da dama wadanda suka shafi cunkoso da rashin tsaro. Sai dai matsalolin babban birnin tarayya Abuja sun fi fitowa karara saboda matsayin da birnin ke da shi a tarihin Nijeriya, wanda ke da babban minista mai gudanarwa.
AL AMIN CIROMA
A duk bangaren nazarin da mutum ya dauka, zai fahimci cewa ministan na babban tarayya Abuja Malam Musa Bello yana da manyan matsalolin da ya kamata ya rika dauka yana fuskanta domin ciyar da wannan birni mai tarihi gaba.
Waiwaye dai, in ji masu magana shi ne adon tafiya. Idan ba a manta ba an rattaba sunan Abuja a matsayin babban birnin tarayya ne a cikin shekarar 1976, lokacin tsohuwar gwamnatin mulkin soja karkashin Marigayi Janar Murtala Mohammed. Sa’ilin da alkalumma suka tabbatar cewa a ranar 12 ga Disamba 1991 ne Tsohon Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya dauko kujerar mulkin kasar daga Birnin Ikko wato Legas zuwa Abuja, domin tabbatar da dokar da ta kafa birnin a matsayin babbar fadar gwamnati.
Wannan nazarin ya nuna cewa birnin na Abuja a yau, ya zama tamkar wata karamar hukuma. Musamman ma idan aka yi la’akari da tsari na birgewa da aka dora birnin a kai tun fil azal.
Nazarin har ila yau sun nuna cewa an dora birnin ne a kan wani kasaitaccen tsari da ya hada da ‘yan tagwayen hukumomi masu cikakken ikon tafiyar da birnin, wato Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA), inda minista ke jagoranta da kuma Hukumar Raya Kasa da Ci Gaban Babban Birnin Tarayya (FCDA), inda babban sakatare mai cikakken iko ke jagoranta. A nan kadai aka samar da irin wadannan manyan hukumomi masu karfi, saboda mahimmancin birnin a matsayin cibiyar Nijeriya. An tsara hakan ne domin Mai Girma shugaban kasa ya rika samun cikakken rahoton birnin daga wajen minista, inda shi kuma minista zai rika samun rahotannin ci gaban birnin daga babban sakataren.
Kan haka ne Abuja ta kasance daya daga cikin birane mafi tsari a nahiyar Afrika ta Kudu – wadanda suka hada da birnin Accra ta kasar Ghana, Abidjan ta kasar Ibory Coast, Dakar ta kasar Senagal, Legas da kuma Abuja a Nijeriya.
Yayin da aka tabbatar da hakan ne ita kuma Abuja ta sami tsari mai inganci, ta yadda aka karkasa birnin daga gunduma-gunduma zuwa shiyya-shiyya, yanki-yanki da unguwanni masu tsari na bai-daya. Babban abin da ya fi bayar da ma’ana a tsarin birnin Abuja shi ne tsarin hanyoyin da suka harhada dukkanin yankuna da shiyya-shiyyar kwaryar birnin. Hakan ke tabbatar da cewa muradin gwamnati na mayar da Abuja cibiyar Nijeriya shi ne yin amfani da tsarin gine-gine don bayyana cikakken hadin kan mazauna garin.
Birnin yana fuskantar kalubalen kwararowar al’umma daga ko’ina a fadin kasar nan har da kasashen waje. Mafi yawan masu yin hijira suna shiga cikin birnin, suna yin hakan ne da zummar neman sanaa’o’i da ayyukan yi don magance harkar tattalin arziki. Wasu kuma sun dauki Abuja a matsayin wata ‘Aljannar’ duniya. Hakan ta sa a ke rige-rige shiga cikin ta don neman matsuguni ko kuma guraben neman ilmin zamani da sauransu.
A wannan nazarin dai, manazarta sun fito da musabbabin samun manyan matsaloli da suka dabaibaye babban birnin na tarayya. Matsalolin sun hada da ambaliyan mutane zuwa cikin birnin, wadanda galibi ‘yan kashe wando, almajirai marasa alkibla, ‘yan bangan siyasa da sauransu. Hakan ce ta haifar da wadannan shingaye bakwai da nazarin ya bayyana a matsayin manyan matsalolin da ya kamata ministan birnin na tarayya ya mayar da hankalinsa a kai. Su ne kamar haka Rashin tsaro, Yawaitar gidajen ba da babu kowa a cikinsu, sakamakon tsadarsu da Toshewar magudanun ruwa da na ba haya sakamakon rashin daidaitacciyar hanyar gine-gine. Sauran matsalolin sun hada da Zamba cikin aminci, Karya dokar tsarin kwalliyar birnin tare da mayar da wuraren kawa da hutawa filayen kwallo da kuma Dumamar yanayi sakamakon cunkoson ababen hawa marasa kyau a cikin kwaryar birnin.
Kowanne daga cikin irin wadannan matsalolin, kamar yadda wannan nazari ya tanadar zai iya kawo tarnaki a tsarin gudanar da shi.An wayi gari a yau rashin tsaro ya dabaiye ko’ina a cikin kwaryar birnin. Zai fi kyau babban minista ya sami damar zagaye birnin musamman da almuru ko cikin dare. Kusan ko’ina za a iske mutane na sharholiyarsu, kowa da irin kiwon da karbe shi.
Baya ga wannan kuma nazarin ya kalli matsalar yawaitar manyan gine-ginen gidaje a cikin Abuja, wadanda ke garkame alhali babu kowa a cikin su. Babbar tambaya ita ce, su waye ke da su? Me ya sa ake barinsu a kulle a koda yaushe. Bincike dai ya nuna cewa ana ci gaba da kulle irin wadannan gidajen ne sabili da babu wanda zai iya kama su a matsayin haya saboda tsadarsu. To, idan har haka ne, wane tanadi mahukunta ke dauka wajen rage irin hasarar filaye da irin wadannan maginan ke yi? Maimakon gina gidajen da ba za a iya shigarsu ba, me zai hana gwamnati ta yi tunanin kafa wasu masana’antu a wajen, idan har taswirar birnin ya bada dama? Ta hanyar wannan aikin ne gwamnati za ta iya hana zaman kashe wando.
Babbar illar da mazauna Abuja ke fuskanta ita ce barazanar barkewar wata annobar cuta, sakamakon toshewar magudanun ruwa da na ba-haya. Ganin yadda ake rike cunkushe birnin na Abuja, duk manazarci zai iya tunanin idan har aka ci gaba a hakan, za a iya wayuwar gari wata cuta ta bulla sabili da yadda, a wasu wuraren za ka iske magudanun ruwa sun tumbatsa, suna fito da kazanta sannan jama’a na shaka bisa tilasci. Wasu ma a daidai inda suke sana’arsu ko kofar gida, ko kuma cikin kasuwanni. Hakan babban nakasu ne ga hukumomi na lafiya da kuma na masu gudanar da birnin na Abuja.
A Nijeriya ne kadai za iske mafi akasarinmu ba mu damu da bin doka da oda ba. A nazarin da aka gudanar, Abuja na daya daga cikin manyan biranen da ake yawan samun irin wadannan mutanen. Sabili da yanayin manyan mutane da mahukunta da ke zama a birnin. Duk wanda ka gani a bisa titi za ka samu yana tinkaho da maigidansa, ko mahaifinsa da sauransu. Hakan ke kara sanya wa wasu mutanen girman kai da tunanin sun fi kowa ‘yancin yin abin da suka ga dama, ba tare da an tsangwame su ba.
Irin hakan ce ta haifar da yadda aka birkita tsarin kwalliya da furannin da aka kashe makudan kudin al’umma don shuka su. A yanzu duk inda aka shuka furanni, yawanci sun zama filayen buga kwallo da yamma. Matasan da ke irin wannan danyen aikin, babu ruwansu. Sannan ba wata hukuma da ke tsawatarwa, an kashe milyoyin kudi a banza ba wanda ya damu.
Mafi muni daga cikin matsalolin nan guda bakwai da ke addabar babban birnin tarayya Abuja a yanzu shi ne dumamar yanayi da cunkoson ababen hawa ke haifarwa. Manazarta sun dora alhakin wannan yanayin ga hukumomi masu daidai sahun matuka ababen hawa. Amma saboda rashin matsi daga manyan hukumomin gudanarwa, an wayi gari yawancinsu suna yi wa ayyukansu rikon sakainar kashi. Da ka iske jami’i a kan hanya, babu abin da yake ransa illa dan abin da zai samu daga wajen direbobi da masu ababen hawa a bisa titi.
Manyan tambayoyi suna kan mahukunta wannan birni mai tarihi; shin yaushe za su murkushe miyagun jami’an sintiri da ke cike a kwaryar birnin, don kawo masu kishin kasa, wadanda za su yaki rashin da’a su tabbatar da tsaro a Abuja? Me ya sa hukumar tallar filaye da taswirar birnin ke yin sakaci wajen sayar da filayen da ba su dace a mayar da su matsuguni ba? Yaushe ma’aikatar duba-gari da malaman tsabta za su fara ayyukansu daidai yadda doka ta umurce su? Yaushe hukumomin birnin za su rika fito da tsare-tsaren wayar da kan al’umma game da manyan muradin babban birnin tarayya da kuma uwa uba bin doka da oda?
Manazarta dai suna ganin yana da kyau babban minista ya kara zage dantse, ya jajirce ya fara bin kadin yadda jami’ansa ke gudanar da ayyukansu. Idan ba haka ba, wata rana za a wayi gari darajar babban birnin tarayya ta fadi wanwar a kasa!