Nazarin Tarbiyar Matasan Nijeriya A Yau

Matasan Nijeriya

Duk al’ummar da ta bunkasa ko ta samu ci gaba mai dorewa, to ko shakka babu ta himmatu wajen kafa ingantaccen ginshikin dora al’ummar ta bisa kyakkyawan tunani daidai gwargwadon kima da yanayin ta. Musamman sabbin jini, bangaren al’umma mafi muhimmanci da tasiri wajen gudana da ci gaba da kayatattun manufofin da suka yi imani dasu a godaben matafiyar rayuwa.

Yau zamu yi tsokaci kan muhimmin batu: Me Ya Jawo Sukurkucewar Tarbiyyar Matasa A Yau? Batu ne mai matukar muhimmanci, kasancewar sa ya shafi rayuwar yau da kullum; wanda a bisa dabi’ar dan adam, yana da burin samun nagartaccen mutumin da zai maye-gurbinsa, kuma abin alfahari.

Bugu da kari kuma, batu ne wanda ya dace a dauke shi da muhimmancin gaske, saboda yadda ta hanyar sa ne al’umma za ta hangi inda za ta dora harsashen tubalin gina abinda take son ya dore. Wanda kuma ta rashin sa lamurra kan taru su cukurkude har a rasa bakin zaren warware wasu matsalolin da ke neman shan kan al’umma baki daya.

Mallam Bahaushe ya ce: Al’umma Rahama Ce, kuma idan an duba wannan zancen haka ne (duk da a wani kauli ya ce: Idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Idan mun kalli wannan batu, za mu fahimci cewa akwai bukatar gwamnatoci da iyaye tare da sauran daidaikun al’umma su kalli batun tarbiyyar matasan mu da kyau; shin akwai ci gaba a fannin tarbiyya matasan ko ta sukurkuce? Shin me ya jawo sukurkucewar tarbiyyar, kuma ina mafita?

Ba abu ne mai dadin ji ba, balle ko yin tinkahon lalacewar wani ko wasu ba, face abinda Bahaushe ke cewa: Gyara kayanka, ba ya zama sauke mu raba. Saboda haka, amsar wannan tambaya abu ne mai sauki, ganin yadda lamarin sukurkucewar tarbiyyar matasan mu ta yi kamari, kuma da yadda iyaye ke korafin yadda al’amarin ke neman gagarar kundila.

Sannan akwai kyakkyawar fatar gano bakin zare, idan mutum ya lakanci matsalar sa, sannan abu ne mai wuya mutum ya iya gyara kuskuren da bai san dashi ba. Saboda masu hikimar magana sun ce: Gano cuta rabin magani ce.

Dole kowane sashen wannan al’umma ya san da cewa, makasudin kasancewar jama’a wuri guda; duk da bambance-bambancen harshe da launi, shi ne yin aiki tukuru don cimma manufofin da zasu kai ga gina ingantacciyar rayuwa da kwanciyar hankali da fahimtar juna. Sannan kuma hakki ne ga kowane sashen al’umma wajen kokarin sauke nauyin da ya hau bisa wuyansa.

A duk lokacin da al’umma ta kaucewa hadafi da manufofin zamantakwa, ta dukufa wajen nuna wa juna yatsa, wani lokaci za a wari gari ta fada tarkon ruguza komai nata. Za a wayi gari abinda tafi karfisa zai gagareta kuma za ta yi sallama da duk wani dandanon ci gaba da bunkasar tattalin arziki da walwala- kana da faduwa kasa warwas a fannin gina tunani da tarbiyyar shugabanin gobe.

Saboda za a wayi gari, maimakon hada hannu wuri guda domin aikin ci gaba, da hawa kan kyakkyawar turbar magabata zai yi wuya, sai dai a ci gaba da gadon fada da nuna wariya da bambance-bambancen kabilanci da addini. Kuma duk al’ummar da ta tsinci kanta a wannan yanayin, to kashinta ya bushes kuma ta gama tambadewa- ba ta da hus. Kuma sake gina wannan al’umma abu ne mai matukar wahala; saboda yadda suka gaji gaba da kiyayya.

Kamar yadda masana suka tabbatar, aikin gina tarbiyya da horas da halaye nagari, ba aikin bangare daya na al’umma ba, al’amari ne na dogon lokaci wanda nauyi ne wanda ya hau kan baki dayan kowane bangaren al’umma. Kuma samun gazawar kowane daya bangare yana iya shafar sauran- aiki ne na gwamnatoci, iyaye, da daidaikun jama’a.

Ajin farko su ne gwamnatoci, bangaren da suka yi kane-kane a sha’anin gudanar harkoki da rayuwar al’umma, bangaren da ingantattun manufofi ko gurbatattu da suke samarwa ke shafar al’umma kai tsaye. Kuma wannan sashe yana da rassa daban-daban wajen taka muhimmiyar gudumawa a fannin sauya tunani da tarbiyyar al’umma baki daya.

Akwai babban aiki ga wannan sashe wajen sake tunani ta hanyar daukar kwararan matakin sauke wannan nauyin, wanda idan basu yi ba, su ma abin zai shafe su tare da ya’ya da sauran iyalan su. Sannan kuma uwa uba, idan an koma ranar hisabi.

Gwamnatoci ne suke da karfin dokar samar da ingantattun manufofi da hadafi wajen kyautata rayuwar al’umma, a makarantu, mu’amalar su da wasu kasashe tare da daukar matakan abinda ke kai-komo a ciki da wajen kasar. Saboda bai dace ace abubuwa su rinka tafiya haka sakaka ba, ba tare da daukar mataki ba- ya dace gwamnatoci su samar da tsare-tsare da shirye-shirye masu ma’ana, musamman domin matasa, manyan gobe.

Duk da ba a taru aka zama daya ba, amma yanzu dauki misalin yadda mu’amalar matasa; maza da mata ke gudana, a sarari da a kafafen sada zumunta. Abin akwai fargaba sosai, kuma da yadda abin sai dada tabarbarewa yake. A hannu guda kuma ga ta’amulli da miyagun kwayoyi, wanda ya zama ruwan dare a tsakanin matasa, ga kasala da zaman kashe wando wanda ya yi katutu a gindin matasan mu. Wannan babban abin kaico ne, kuma abu ne da ya dace a hada hannu don yakar sa.

Sabanin yadda abin yake a wasu kasashe, duk da wani lokaci idan mutum ya yi magana, wani yana iya cewa yan Nijeriya ne sun yi yawa; kuma idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, wanda a hasashen da ake yi yawan yan Nijeriya bai wuce 200 ba. Amma mu kalli kasar Chana (Sin), wadda jama’ar ta sun haura miliyan 1000, amma ya take shirya wa rayuwar al’ummar ta; musamman matasa?

Kasar Chana tana daga cikin manyan kasashen duniya, wadanda suka fi kowa karfin tattalin arziki da yawan jama’a (a shekarar 2017 tana da yawan mutane biliyan 1.386), amma a wata kididdiga ta bayyana cewa tun a shekaru 20 da suka gabata, kasar ta kawar da matsalar jahilci ga jama’ar ta. Da tsararren shiri ga matasanta na tsawon shekaru 12 nan gaba a kasa.

Wannan sabon binciken mai dauke da shafuka 24 wanda cibiyar ‘Asia Society’, da ‘Business Roundtable’, Council of Chief State School Officers, suka gudanar a karkashin taken: Tsarin Ilimin China: Yar manuniya ga masana a kasar Amurika.

Tare da bayyana cewa kasar China ta na da wani salon sanya kumaji wajen yi wa sha’anin karatu dibar karan-mahaukaciya tare da sanya son karatu a zukatan dalibanta, su rinka yi a cikin tsawon lokaci ba tare da kosawa ba.

Rahoton ya bayyana cewa, “yan kasar China mutane ne masu matukar kumajin neman ilimi, domin haka ne ya jawo yi wa yaransu takamamen shirin yadda rayuwar su za ta kasance nan gaba. Sannan kuma a shirye muke wajen sadaukarwa ga kasar mu wajen ganin ta bunkasa”.

“A halin yanzu, dalibanmu za su iya fita ayi gogayya dasu zuwa kowace kasa a fadin duniyar nan, saboda nagartar da suka samu. Komai da ruwanka ne, sun kware a aikin tsara manufofi da gudanar da sha’anin ilimi wanda hatta kasar Amurika shaida ce a kan hakan, bisa cikakkiyar kwarewar da suke da ita, kuma sun shirya tunkarar kowane kalubale da yanayin sauyin da duniya ta samu”. In ji Mista Susan Traiman.

Sai kuma bangaren iyaye da daidaikun al’umma, wanda su ma akwai babban nauyi a kan su, wajen bayar da tasu gagarumar gudumawa wajen kafa ginshikin gina tarbiyyar matasan.

Exit mobile version