NCC Ta Kwace Ayyukan Satar Fasaha Na Kimanin Naira Milyan 926

Daga Sabo Ahmad.

Manajan shiyyar Legas na Hukumar yaki da satar fasaha ta Nijeriya Mista Obi Ezeilo,  ya bayyana Hukumar ta kwace ayyukan satar fasaha da kudinsu ya kai naira milyan 926 a wata takwas a cikin garin Legas. Manajan fadi hakan ne a zantawarsa da Kamfanin dillancin lanarai na Nijeriya a ranar Alhamis din da ta gabata a ofishinsa da ke Legas. Ya ce sun kwace kayan ne a tsakanin watan Janairu da Agusta na wannan shekarar a gurare daban-daban da ke cikin garin Legas.

Sannan sai ya ci gaba da cewa, “Hukumar ta kaddamar da wani babban ofarashin inda ta kama kayayyakin satar fsaha da kudinsu ya kai naira miliyan 926 da aka samu a wadansu kwantena a Apapa da kuma wadansu manya-manyan.

Ya ce “ta fuskar hukunta masu satar fasaha, yanzu an samu canji, da zarar an tabbatar da laifi za a yanke hukunci” Saboda haka ya ce, sun kama mutum12 masu laifi a cikin wata takwas, kuma a halin yanzu akwai mutum 21 wadanda ke zaman jiran shara’a.

Sannan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Hukumar ta kawo karshen kes din wadansu mutum bakwai.

Ezeilo ya ce,  n samu kwantena guda uku da aka kwace a Apapa Terminal da kuma wadansu manyan shaguna guda bakwai a Mushin da Ajegunle da Surulere da Amuwo-Odofin.

Kayan da aka kwace sun hada da  kayan yin fina-finai da CD-CD  da bidiyo CD-CD.

Ya ce, Hukumar za ta samar da wata sabuwar dokar da zata kara yaki da satar fasaha a wannan kasa.“Yanzu a kwai kudirin da ke ofishin babban maishari’a na kasa don sa mata hannu.Muna fatan idan wannan kudirin ya zama doka za ta taimaka wajen dakile ayyukan satar fasaha, sannan kuma ta karfafa gwiwar masu fasaha domin za su samu cin ribar fasaharsu, sannan kuma ta magance matsalar satar fasaha a intanet. Wannan shi ne abin da muke bukata, wanda kuma fatan ya zama sanadiyyar bunkasa fasaha da cin moriyarata a dukkan fadin kasar nan.”In ji shi.

Ezeilo ya ci gaba da cewa, kwananan Hukumar ta kaddamar da yaki da satar fasaha wanda ta yi masa lakabi da “Operation No Mercy” a kasuwar sayar da littafai ta  unguwarYaba da ke garin Legas, wanda ake zargin gurin da cewa, cibiy c eta sayar da kayan satar fasaha.

A karshe, Ezeilo ya yaba rundunar ‘yansanda bisa gudummowar da suke bas u wajen ganin an tabbatar bin doka.

 

Exit mobile version