Daga Sulaiman Ibrahim,
Reshen Hukumar Sadarwar ta Nijeriya (NCC-CSIRT) ta gano wasu sabbin dabarun kutse ga wayoyin hannu guda biyu, sannan ta shawarci masu amfani da wayar hannu a Nijeriya kan matakan da za su dauka don samun kariya daga hare-haren.
CSIRT, a cikin shawarwarin tsaro na farko da ta bayar a watanni uku da kirkirar ta, ta gano hare-haren yanar gizo guda biyu da ake kaiwa masu amfani da wayar sannan ta samar da mafita wadanda za su iya taimakawa wajen afkawa ga kutsen.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Dokta Ikechukwu Adinde ya fitar a jiya, ta ce fasahar kutsen.
Ta farko an bayyana ta da Juice Jacking, wadda za ta iya shiga cikin na’urorin masu amfani da ita a lokacin da ake cajin wayar hannu a wurin cajin wayar na bainar jama’a kamar tashosin jirgin kasa ko na sama.
Na biyun kuma ta hanyar Facebook ce, za a turo maka da neman abokantaka, wannan kuma hari kan Android Operating System ne kawai banda masu shiga shafin Facebook ta Komfuta.