Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Nda-Isaiah (1962-2020): An Bada Shaidar Zamansa Jakada Nagari

by Khalid Idris Doya
December 22, 2020
in LABARAI
2 min read
Nda-Isaiah (1962-2020)
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

An bayar da shaidar cewa, Shugaban Rukunin Kamfanonin Jaridar LEADERSHIP, Marigayi Sam Nda-Isaiah, ya kasance jakada nagari a lokacin rayuwarsa.

Bayanin hakan ya fito ne daga mataimakin Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke garin Ile-Ife, Farfesa Eyitope Ogunbodede, a jiya Litinin, wanda ya misalta marigayi mawallafin jaridun LEADEESHIP, Mista Sam Ndah-Isaiah, a matsayin wani Jakadan Arziki, dan qwarai kuma amintaccen jakada da ya kasance ga Jami’ar a idon duniya.

samndaads

Fitaccen dan jaridar, Mista Sam Ndah-Isaiah, dai tsohon dalibin Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife ne.

Ogunbodede, wanda ya dauki tsawon lokaci ya na nuna takaici da jimamin mutuwar qwararren masanin ilimin sarrafa maguna a wani taron menema labarai da ya kira kan gargadin jama’a masu kutse cikin filin makarantar, ya misata rashinsa a matsayin wani babban rashi da jami’ar ta yi musamman tsangayar koyar da ilimin harhada magunguna na makarantar.

Sannan, ya gargadi al’umman da ke yankin makarantar da su daina sayen filin a wajen dillalai masu daukar filin gwamnati domin sayar musu, inda yake ce musu filin makarantar mallakin gwamnatin tarayya ne.

“Don haka duk wani ko wata qungiya da ke qoqarin kawo damuwa ko shiga hurumin da ba nasu ba, da su sani an rigaya an sanar da hukumomin tsaro wannan lamarin.”

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta bada umarni daga wajen Ministan ilimi Malam Adamu Adamu kan cewa hukumomin jami’ar OAU su himmatu wajen ilmantar da jama’a tare da fadakar da su kan wannan matakin na shiga filin makarantar ko saye walau bisa rashin sani ko qaqa ta hanyar sanya talluka a gidajen rediyon jihar Osun.

Ya kuma gargadi wadanda aka yaudara har suka sayi filin gwamnatin tarayyar da cewa su fa sani gwamnati ba ta da shirin saida wannan filin, tana shirye da kare wa jami’ar muhallinta.

Da ya ke maida jawabi kan wannan lamarin, mai magana da yawun al’ummar Ife, Cif Bami Ogunbanbi, ya shaida cewar jami’ar tana ta qoqarin kira ga jama’a, sai dai ya shaida cewar sun gaza samar da taswirar da ke tabbatar da iqirarinsu na cewa an mallaka wa jami’ar wani yankin Paraki tun a 1961.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Kara Wa’adin Lambar Rijistar ’Yan Kasa Kafin Toshe Layukan Waya

Next Post

Sakamakon Gwaji: Ban Kamu Da Cutar Korona Ba, Inji Tambuwal

RelatedPosts

Hutun Kirsimeti

Gobarar Sakkwato: Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Tambuwal

by Khalid Idris Doya
8 hours ago
0

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Kakkarfar tawagar Gwamnatin Tarayya ta jajantawa...

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

by Khalid Idris Doya
11 hours ago
0

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami'a mai magana...

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

by Khalid Idris Doya
11 hours ago
0

Yau gwamnonin yammacin Nijeriya ke gudanar da wani taro da...

Next Post
Gwamna

Sakamakon Gwaji: Ban Kamu Da Cutar Korona Ba, Inji Tambuwal

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version