- Za A Bi Qa’idojin Korona
- Kungiyar Marubuta Ta ANA Kano Ta Nuna Jimaminta
A yau Laraba ne za a fara bikin yin bankwana da gawar Shugaban kamfanin Rukunin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, kamar yadda tsare-tsaren gudanar da jana’izarsa ya nuna. Wannan na faru ne a daidai lokacin da a ke cigaba da mika sakon ta’aziyyar rasuwar fitaccen shugaban kafar yada labaran a fadin Tarayyar Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, Mista Nda-Isaiah ya kwanta dama ne a ranar Juma’a, 11 ga Disamba, 2020, bayan gajeriyar rashin lafiya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, iyalin mamacin su ka fitar da jaddawalin yadda jana’izarsa za ta gudana, a inda suka bayyana cewa, tsofaffi shugabannin Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, za su albarkaci jana’izar marigayin, inda a ranar Laraba mai zuwa za a fara gudanar da ayyukan jana’izar, wacce ranar ce da za a gabatar da wani taro na musamman, don sauraron jawabai daga makusanta da ’yan uwan Marigayin.
Sanarwar ta ce, bikin addu’o’in da za a yi a katafaren dakin taro na Duniya da ke Abuja (ICC) da misalin karfe 12:00 na yau, za a gudanar da shi ne ta hanyar hoton bidiyo, amma dukkan tsarin addu’o’in da a ka shirya yi a wajen su na nan yadda su ke babu canji.
Asalin sanarwar dai ta bayyana cewa, ana kuma sa ran Babban Basaraken gargajiya na jihar Neja, Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar zai halarci taron. Nda-Isaiah dai shi ne ke rike da sarautar Kakaki Nupe kafin rasuwar tasa.
Haka zalika, akwai kuma alamu masu karfi da ke nuna cewa a ranar Lahadin, fadar Shugaban kasa da ta gwamnatin Jihar Neja, (inda Marigayin ya fito), za su tura manyan wakilai zuwa wajen taron.
Sanarwar ta Mista Abraham Nda-Isaiah ta kara da cewa, za a fara gudanar da jinjinawa ga marigayin, wanda ya kasance fitaccen ne a harkar yada labarai da karfe 12 na yau. Sannan kuma a gudanar da wakoki na musamman a ranar Lahadi 27 ga Disamba, 2020 a.
Abraham ya ce, “za a gudanar da taron binne marigayin ne a ranar Litinin 28 ga Disamba, 2020, a makabartar Gudu da ke Abuja, Babban Birnin kasar, da misalin karfe 10 na safe, wanda zai zama taro ne na wadanda aka gayyata kawai.”
Sam Nda-Isaiah, wanda ya kasance masanin harhada magunguna, dan kasuwa, mashuhuri a harkar yada labarai, kuma hazikin dan siyasa. Mutuwar sa ta girgiza mutane a duk fadin kasar nan da ma kasashen waje.
Duk da yake mutum ne wanda ya sami horo a fannin sarrafa magunguna, Sam yana fada da farin ciki cewa, ya dauki aikin jarida a matsayin sana’arsa, kuma ya samu nasarori tun bayan da ya kafa tsayayyar Kamfanin Jaridun LEADERSHIP, ‘National Economy’ da LEDERSHIP A YAU, wacce ta kasance jaridar Hausa ta farko mai fitowa kullum a duniya.