Nda-Isaiah Ya Tafi Lokacin Da Aka Fi Bukatar Shi –Janar Abdulsalami

Janar Abdulsalami

Daga Nasir S. Gwangwazo,

Tsohon Shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa, Shugaban jaridar LEADERSHIP kuma Kakakin Nupe, Marigayi Sam Nda-Isaiah, ya rasu a lokacin da a ka bukatar shi ne.
Janar Abdulsalami ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aike wa iyalin mamacin, wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata da daddare, ta hannun kanin marigayin, Mista Abraham Nda-Isaiah.
A cikin wasikar, wacce tsohon janar din ya santa wa hannu da kansa a jiya Talata, ya ce, “a madadin iyalina da ni kaina, Ina mai mika sakon ta’aziyyata cike da alhini da jimamin rasuwarsa a daidai lokacin da a ka fi bukatar shi.”
Tsohon Shugaban Kasar, bayan ya roki rahamar Allah ga mamacin, sai ya cigaba da cewa, “gibin da ya bari a cikin iyalinsa, jaridar LEADERSHIP da bangaren yada labarai bakidaya, ba zai taba cikuwa ba, amma mun amshi dangana saboda kasancewar zai riski Ubangijinsa ne. Kowane rai mamaci ne.”
Daga na sai Janar Abdulsalami ya kara da cewa, hakika rayuwar marigayin ta yi matukar tasiri ga mutanen da su ka yi aiki da shi a lokacin da ya ke raye. Daga nan sai ya yi fatan samun kyakkyawar rayuwa ga wadanda ya bari a baya.

Exit mobile version