Khalid Idris Doya" />

NDE Na Horar Da Mata 400 Kan Sana’o’i A Bauchi

Hukumar samar da aiyukan yi ta kasa wato ‘National Directorate of Employment’ (NDE) ta fara koyar da mata dari hudu 400 da suka zakulo daga kananan hukumomi 20 da suke fadin jihar sana’o’i daban-daban na dogaru da kai na tsawon wata uku.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da taron horaswar da aka yi a ofishin NDE da ke Bauchi, Darakta Janar na hukumar NDE ta kasa, Nasiru Muhammad Argungu, ya shaida cewar sun samar da shirin ne domin karfafan mata kan sana’o’i, yana mai fadin cewar duk lokacin da aka baiwa mace horo kan sana’a tamkar an koyar da al’umma gaba daya ne, yana ma fadin muhimmancin da mata ke da shi a cikin al’umma.

Argungu, wanda ya samu wakilcin Ko’odinetan NDE na Bauchi, Ali Lawan Yaya, ya ce, shirin ya fito ne daga tsarin da suka yi na  na zakulo mutane 20 a kowace karamar hukuma da ke fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan domin basu horo kan sana’o’i.

Argungu ya kara da cewa, horaswar tana daga cikin muradin hukumar NDE na samar da aiyukan yi ga wadanda basu da aikin yi, inda yake mai shaida cewar hukumarsa ta kuduri aniyar koyarwa da samar da sana’ar yi ga mata da matasa wadanda ya bayyana su a matsayin shingishikan ci gaba.

Ya ce, za a baiwa mata horo kan sana’o’i daban-daban da suka hada da Dinki, Kayayyakin ado, kayan kwalliya, gyaran gashi na mata da kitso, da sauran sana’o’i daban-daban da suka shafi mata kai tsaye domin tabbatar da sun tsayu da kafafunsu.

Shugaban ya ci gaba da cewa; matan da suke cikin gajiyar horon na tsawon wata uku za su basu naira dubu shida ga kowannensu a matsayin kudin zirga-zirga domin basu damar halartar wuraren daukar darasin sana’o’in a kowace rana.

Ya kuma ce sun yi amfani da hanyoyin zakulo matan da suke bukatar irin wadannan sana’ar daga cikin al’umma, sai ya kara da cewar mata sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar shugaban kasa Muhamamdu Buhari a lokacin zave.

Sai ya kara da cewa, shirin zai tabbatar da rage matsalolin talauci da rage wadanda basu da aiyukan yi a cikin al’umma, a bisa haka ne ya jinjina wa kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa tsare-tsarensa na tabbatar da ya rage yawan mutanen da basu da sana’ar yi a cikin al’umma.

Alhaji Argungun ya kuma taya matan da suka samu kansu cikin horon murna a bisa haka ya jawo hankalinsu da su yi tsayuwar daka su koyi sana’o’in da za a shafe tsawon lokacin ana koyar musu domin amfanun kawukansu da al’ummomin da suke ciki.

A cewar shi, sanar mace zai taimaketa wajen kula da rayuwarta da rayuwar ‘ya’yanta hadi da mai gidanta da ma al’umma baki daya.

Wasu daga cikin matan da suke amfana da shirin, Malama Aisha Musa, Khadija Ibrahim, Hadiza Gambo sun jinjina wa shugaban Buhari da hukumar NDE a bisa samar da shirin, suna masu shan alwashin tsayu da kafafunsu domin koyan ababen da za a koyar musu da kuma tabbatar da yin sana’ar yanda ya dace domin kula da rayukansu.

Exit mobile version