Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi
Hukumar NDE ta ƙasa ta ƙaddamar da taron bukin haɓaka aikin yi da kuma horas da matasa 18,000 a Jihar Kebbi kan sana’o’in zamani iri daban-daban tsakanin mata da maza duk faɗin jihar ta Kebbi.
Taron ya gudana ne a ɗaukin taro na kwalejin Waziri Umaru da ke Birnin-kebbi a shekaran jiya. Wanda bukin horaswar ya samu halartar manyan shugabanin gwamnatin tarayya da ta jihar kamar ministan kwadago da Aiki Sanata Chris Nwabueze Ngige, Shugaban hukumar Samar da Aikin yi ta ƙasa dakta Nasir Ladan Muhammad Argungu,Mataikin Gwamnan jihar kebbi Alhaji Samaila Yombe Dabai, mataikin shugaban kwamitin kwadago da Samar da aikin yi a majalisar dokoki dakta Manir Baba Dan Agunde, Sanata Muhammad Adamu Aliero.
Sauran sun hada Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar, Sarkin Kabin Argungu Alhaji Samaila Muhammad Mera, Kakakin majalisar dokoki ta jihar kebbi Alhaji Samaila Abdulmuminu Kamba da kuma wakilin ƙaramin ministan kwadago da Aiki .
Har ila yau ministan ya ci gaba da cewa ya yi farin cikin gabatar da jawabi mai mahimmanci a wannan muhimmin taro, na ƙaddamar da horo da horos da kuma karfafawa matasa fiye da 18,000 da hukumar NDE shirya, wanda shine kokarin da za a iya domin biyan bukatun matasa marasa aikin yi ga ‘yan ƙaunatattunmu, musamman ma matasa, don samun damar yin aiki wanda zasu iya dogarowa ga Kansu.
sai dai ya ce shugaban Muhammadu Buhari a kwanan nan, shugaban ya nuna kyakkyawar fatawa ta karfafa matasa ta hanyar tsarin fasaha da kuma tallafawa hukumomin tarayya da ke da nauyin kundin tsarin mulki.
Hakazalika ministan ya nuna jidadin sa kan irin yadda gwamnatin jihar kebbi ke bada goyun bayan ta wurin ganin an Samar wa matasa aikin yi a ƙasar nan.
Daga nan kuma ya ce ya kamata a lura da cewa jihar Kebbi ta sami albarka ga amfamin noma a cikin bangarori masu mahimmanci da kuma ma’adinai wanda ke iya samar da zuba jarurruka da hannun kokarin Gwamna Bagudu wanda ya jagoranci kokarin na yin amfani da wannan damar don ci yarda jihar kebbi da ma ƙasar Nijeriya a gaba ta hanyoyin noma.
Shima da yake nasa jawabi Shugaban hukumar NDE ta ƙasar dakta Nasir Ladan Muhammad Argungu, ya bayyana cewa, manyan baki maza da mata da ke wannan wurin , mun taru a yau don ƙaddamar da horo da horassu wa ta fiye da 18,000 har yanzu marasa aikin yi a cikin rayuwa mai mahimmanci da ma’ana. Za a horar da daruruwan mutane dubu huɗu da ɗari takwas da ashirin (4820) a fannoni daban-daban da suka shafi fasahar gargajiya domin dogaro da Kansu.
Shugaban hukumar ta NDE ya ci gaba da cewa horas suwar ta kunshi fanoni uku ne, wanda horas suwar zata kai kimanin mako biyu ana gudanar da ita , horas suwar ta hada da ilimin kiyon dabbobin da al’umma ke da amfani da su a cikin ƙasar mu Nijeriya. Horas da manoma ilimin yadda zasu jagoranci haɗin kai tare da ci gaba da hulda da bankunan kudi ta hanyar noma. A nan za a ba wa ‘yan makaranta kwaskwarima a kan hankali da tunani don sauya aikin yin aikin gona kamar yadda ya dace da aikin da aka biya.
Sauran sun hada da kashe waɗanda suka shiga za su zama ainihi a cikin gari don rage haɗarin samar da abinci a kasuwa.
Shima da yake gabatar da jawabin sa a wurin taron Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana jindadin sa kan wannan shirin da hukumar NDE ta kawo a jihar kebbi, inda ya yabawa gwamnatin tarayya da kuma shugabanin hukumar ta NDE kan soma ƙaddamar da shirin da matasan jihar kebbi.
Gwamnan Bagudu ya ce “ gwamnatin jihar kebbi zata bada goyon baya ga shirin horas da matasan jihar kebbi sana’o’i hannu na zamani domin su iya dogaro da kawunan su”. Ya ci gaba da cewa” zamu bada tallafin kudi ga shirin Samar da aikin yi ga matasan jihar kebbi kai har da ƙasa baki ɗaya.
Hakazalika Gwamna Bagudu ya yi kira ga matasan jihar ta kebbi da su sadaukar da Kansu wurin ganin cewa su koyi abin da ake son su iya a lokacin karɓar horas suwar, domin samun nasarar abin da suka koya.
Daga nan yana godiya ga duk manyan bakin na gida dana wajen jihar da suka halarci taron bukin ƙaddamar da horas suwar ta matasa domin Samar musu da aikin yi a cikin jihar ta kebbi da kuma ƙasar Nijeriya baki ɗaya.