Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen filin jirgin saman Legas ta cafke wasu maza uku da ake zargi da hodar Iblis mai nauyin kilogiram 137.8. An kama wadanda ake zargin an kama su ne tare da haramtattun magungunan da suka boye a cikin man shafawa na gashi, kayan dinki, da rigunan da aka hada da carbon da sauran abubuwa masu maiko don kada injunan binciken su gano su.
Jami’an hukumar sun damke wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyin da suka hada da; Okeke Uchenna da Azubuike Jeremiah Emeka, sai kuma a yayin da ake gudanar da binciken jiragen saman Habasha daga Brazil aka kame Abdul Musa wanda ke kokarin safarar hodar Iblis zuwa Indiya ta hanyar rumbun adana kaya na jirgin daukar kaya wato (Cargo), na ‘Skyway Abiation Handling Company, SAHCO a cikin Legas.
A cewar Kwamandan Filin jirgin saman NDLEA, Garba Ahmadu, a wani taron tattaunawa da manema labarai, an cafke wadanda ake zargin da kayan da nauyinsu ya kai kilogiram 13k, da mai nauyin kilogiram 117, duk na miyagun kwayoyi, sai kuma hodar Iblis mai nauyin kilogiram 7.8. Ahmadu ya bayyana cewa Okeke Uchenna ya kasance mai laifi ne har biyu da ma dan gudun hijira ne da Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ke nema saboda ya tsallake beli kan wani laifi da ya shafi miyagun kwayoyi a shekarar 2014, sannan an kara bayar da sammacin kame shi.
Ya bayyana kamun da aka yi a matsayin mai mahimmanci saboda yawan magungunan da aka kama, ya kara da cewa kilogram 13, 7.8 da kuma kilogiram 117, sun kasance masu mahimanci bisa yanayin safarar.
An kama mutane 60 da ake zargi wadanda suka hada da maza 52 da mata 8 kuma dukkansu an gurfanar da su a kotu, sannan 44 an yanke musu hukunci.
“Adadin magungunan da aka kama su ne hodar Iblis kaso 51.404 (1.51 bisa 100), Cannabis satiba kashi 103.84 (3.04 bisa 100), Methamphetamine kashi 19.935 (0.58 bisa 100), Ephedrine kaso 19.811 0.58), Khat ya bar kashi 2,993.350 (87.70 bisa 100), Psychotropic, Tramadol kaso 158.632 da (kashi 4.65), Diazepam 42.0 (kashi 1.32) da Nitrazepam 24.491 (kashi 0.72 cikin 100) wanda ya kawo jimlar magungunan da aka kama zuwa 3,413.463 (100 bisa 100).”
Ahmadu ya lura cewa an cimma nasarorin ne ta hanyar sadaukar da kai da jami’an rundunar suka yi duk da fuskantar hadari da kalubale da suke yi.
“Ina son na gode wa Hukumar Kula da NDLEA saboda jagorantar umarni da kuma kawance da sojojin kan iyaka na Burtaniya, Hukumar Yaki da Laifuka ta Burtaniya wacce ta share fagen kirkirar Hadin Gwiwar JBTF Aikin da ke da alhakin sauya umarnin na NDLEA MMIA zuwa ofishin wanda aka wadata shi da kayan aiki na zamani da kuma horar da jami’ai har zuwa yau daidai da kyakkyawan tsarin aiki na duniya.”