Daga Khalid Idris Doya
Hukumar Yaki Da Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta shaida cewar za ta nemi amincewar gwamnati domin gudanar da gwajin nasabar kayan maye ga sabbin daliban manyan makarantu, sabbin jami’an hukumomin tsaro da kuma jami’an gwamnati da za a dauka mukaman siyasa.
Birgediya Janar Buba Marwa (Mai ritaya), shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi shi ne ya shaida hakan yayin ganawa da Kwamandojin hukumar na jihohi 36 da birnin tarayya Abuja gami da runduna ta musamman a ranar Litinin a Abuja.
Marwa, ya ce nan bada jimawa ba zai gabatar da wannan bukata wa gwamnati domin yin gwaji wa dukkan daliban jami’o’i da za su soma karatu, ya na mai cewar, gwajin zai hada da masu zuwa aikin yiwa kasa hidima, ma’aikata sabbin dauka, jami’an tsaro, hadi da duk wanda za a dauka aiki a kujerun siyasa a cikin gwamnati
Ya ce, “Bazuwar yawan ta’ammali da kayan maye shine ummul-aba’isun wanzuwar ta’addanci kamar su Boko Haram, tashin tashina, satar mutane, kungiyar asiri, hauma-haumar siyasa, iskanci, fyade, da sauran ta’annati na zamanta-kewa da yake gudana yau a kasar nan”.
Shugaban na hukumar NDLEA ya bayar da tabbacin kara himma kan rage ta’ammali da kayan maye, a cikin shirin hukumar na rage aukuwar ta’addanci a kasar nan.
Marwa, don haka ya kalubalanci Kwamandojin hukumar tasa da su kasance masu himmatu wajen yaki da masu safaran kwayoyi a kan tituna da shaguna gami da masu saida miyagun kwayoyi a sirrince.
Ya bayyana kudurinsa na yin aiki kafada da kafada da hukumar kula da magunguna ta kasa (NDCMP), yana mai cewa nan kusa za a samar da layukan kiran kar ta kwana da jama’a za su ke kira kai tsaye domin kai sako ko rahoton masu ta’anmuli da miyagun kwayoyi ga hukumar a lunguna da sakona domin daukan matakan da suka dace cikin gaggawa.
“Aiki wa kasa ne a gabanmu. Miyagun kwayoyi suna ko’ina; ta kowani yanki. Za mu jagoranci yaki da miyagun kwayoyin nan kuma za mu yi nasara. Kada ku kuskura ku yi kuskure kan wannan aikin, aiki da ke rataye a wuyayenmu dukka.
“Haka nan, za mu bada himma sosai wajen rigakafin hana ta’anmuli da miyagun, kula da wadanda cutar ta musu illa, maida hankali kan yadda iyalansu za su kula da su ta yadda ba za su sake komawa ta’anmuli da miyagun kwayoyi ba a cikin al’umominmu, makarantu, za mu kara wayar da kan kungiyoyi rawar da kowa ya dace ya taka.
“A wannan aikin namu za mu jawo sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ‘yan jarida, kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula, jihohi, kananan hukumomi gami da sauran bangarori domin yin aiki tare wajen dakile matsalolin shan miyagun kwayoyi. Sannan za mu gyara cibiyoyin kankare wa masu shan miyagun kwayoyi dabi’ar ta’anmuli da kwayoyin domin tabbatar da suna aikin yadda ya dace tare da yunkurin gina wasu sabbi.
Marwa ya gargadi masu safaran miyagun kwayoyi da masu sha da cewa su gaggauta dainawa domin a karkashin kulawarsa zai fito da matakan da suka dace domin tabbatar da dakile aniyar masu ta’anmuli da kwayoyi miyagu.