Umar A Hunkuyi" />

NDLEA Ta Cafke Dalibin Da Zai Tafi Kasar Cyprus Da Tabar Wiwi

Tabar Wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA sun cafke wani dalibi mai niyyar tafiya kasar Cyprus domin karatu a filin Jiragen sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, (NAIA) da kilo 13.55 na haramtacciyar tabar nan ta Wiwi.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Mista Jonah Achema, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa wacce ya fitar a ranar Talata, a Abuja.

Achema ya ce wanda ake tuhumar mai suna, Sunday Odi, an kama shi ne a dakin masu jiran tashi na filin Jiragen saman a lokacin da yake kokarin shiga Jirgin saman Turkish airline zuwa arewacin kasar ta Cyprus, a bayan ya bi ta Istanbul, ta kasar Turkiya.

A cewarsa, matashin da aka Kaman mai shekaru 23 da haihuwa, dan asalin Jihar Ebonyi ne, wanda ya fito daga karamar hukumar Ezza ta kudu, a Jihar ta Ebonyi, ya kuma sami izinin zuwa yin karatu ne a fannin yawon shakatawa da kula da harkokin Otal-otal a kusa da jami’ar gabashin kasar ta Cyprus.

“A lokacin da ake bincikar kayansa ne sai aka taras da ganyan tabar wanda aka cusa su a cikin kwalaben ruwa sannan aka boye su a cikin wasu kayayyakin abinci sannan aka sanya masu label din ‘Wonder Bitter Root’.

Sai dai Achema ya ce wai Odi ya musanta cewa yana da wata masaniya a kan abin da yake a cikin jakar na shi, sannan ya bayyana cewa wani ne mai suna Emmanuel Ihebekwe, ya nema masa karatu a can jami’ar ta kasar Cyprus.

Achema ya ce Odi ya yi ikirarin cewa wai wancan Ihebekwe din ne ya nemi da ya zo ma shi da wasu kayayyakin abinci da kuma kwayoyin maganin cutar Maleriya da suke a cikin jakunkunan biyu.

Ya ce, “Ihebekwe abokinsa ne tun da jimawa kafin ya yi tafiya zuwa kasar ta Cyprus, ya ce wai ya umurci wani ne da ya zo ma shi da jakunkunan a wajen da yake zaune a Nnewi domin ya je ma shi da su zuwa kasar ta Cyprus.

Ya ce a can Nnewi din ne aka danka ma shi jakunkunan a rufen su rijif, aka kuma shaida masa cewa wai kayayyakin abinci da maganin Maleriya ne a cikinsu.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a filin saukan Jiragen saman na NAIA, Mista Kabir Taskuwa, ya ce hatta yanda aka lullube haramtacciyar tabar shi kanshi abin tambaya ne.

A cewar Taskuwa, muna gane miyagun hanyoyin da masu safarar kwayoyin sukan bi wajen aiwatar da muguwar sana’ar ta su.

“Ya kamata matasanmu su yi hankali da hanyoyin da ake yaudararsu a kai da sunan sama masu aikin yi a kasashen ketare.

“Yawanci ana amfani ne da su wajen yin safarar miyagun kwayoyi daga nan Nijeriya zuwa kasashen ketare din ko kuma in sun isa can din ne ake amfani da su a matsayin dillalan miyagun kwayoyi.

Exit mobile version