Hukumar NDLEA ta cafke mutun 67, masu safarar miyagun kwayoyi a jihar Edo, tsakani watan Yuli da Agusta na wannan shekarar, bayanin haka ya fito ne daga kwamandan shiyya na hukumar Mista Buba Wakawa a yayin da yake gana wa da ‘yanjarida a Benin, hedikwatar jihar.
Buba Wakawa ya bayyana cewa, wadanda a ka kama sun hada da maza 47 da mata 20, an kuma kama kwayoyi masu nauyin kilogiram 779.572 a hannusu. Haka kuma, hukumar ta kama wasu kwayoyi masu nauyin kilogiram 667.6 da masu shi suka gudu suka bari a lokutan da jami’ansu suka kai samame a wurare daban-daban a cikin jihar,
Ya kuma ci gaba da bayyana cewar, sun kama giram 2 na kwayar ‘Heroin’ da giram 26 na ‘Cocaine’ da kuma gram 170 na kwayar ‘Psychotropic’.
Buba wakawa ya bayyana cewa, noman tabar wiwi na daya daga cikin babbar barazanar da ke fuskantar yaki da harkokin miyagun kwayoyi a jihar, “lamarin na bukatar dauki na gaggawa daga bangarori daban-daban” in ji shi. Ya kara cewa, hukumar majalisar dinki duniya mai kula miyagun laifuka da kwayoyi (UNODC) da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da hadin gwiywar rundunar sojojin sama ta kasa sun gudanar da wani bincike a jihar, inda suka gano girman dazukan da masu noma tabar wiwi ke amfani da su wajen harkokinsu na sarrafa miyagun kwayoyi. Ya ce, filayen noman da ya kamata a noma abu ne da zai taimaka wajen samar da abinci ga al’umma ya fada hannun ‘yan kwaya” a saboda haka ya bukaci gwamnati da ta kafa dokar ta baci a fagen yaki da masu safarar miyagun kwayoyin, domin hukumarmu kadai ba za ta iya fuskantar wannan lamari ba, ganin ba mu da isassun kayan aiki.