Hukumar yaki da fataucin muggan kwayoyi ta kasa (NDLEA)ta reshen jihar Kano ta bayyana cewar ta kame wasu mutane 43 da ake zargi da fataucin muggan kwayoyi a cikin watan Janairu da muke ciki.
Dokta Ibrahim Abdul wanda Kwamandan NDLEA na jihar, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wata tattaunawa da manema labarai ranar Juma’a a Kano.
Abdul ya ce an kama su wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar, wannan kuma ya biyo bayan gudanar da wani babban samame da jami’an rundunar suka yi.
Ya bayyana cewar a lokacin da suke gudanar da ayyukansu daban-daban, rundunar ta samu nasarar cafke kilogram 581.702 na wasu daga abubuwan da aka haramta daban-daban a fadin jihar ta Kano.
Ya kara da war “A cikin watan Janairu da muke da muke ciki, mun sami nasarar cafke kilogiram 533.553 na wiwi, kilogiram 48.052 na Psychotropic da kuma kilogiram 0.097 na hodar iblis kamar dai yadda ya bayyana”.
Abdul ya kara da cewar a tsakanin wannan lokaci, rundunar ta samu nasarar yanke hukunci a kan wasu mutane hudu da ake zargi a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.
“A lokacin da ake ciki an tura masu amfani da kwayoyi 76 wadnada aka kai su wurin da zaa rika basu (shawara), sai kuma wasu mutane hudu wadanda aka riga aka saba dasu,saboda yau da kullun, bugu da kari kuma an salami mutane biyu bayan da aka kammala basu shawarar data kamata.
Daga karshe Abdul yace an samu ita nasarar ne sakamakon namijin kokarin da su jami’an na NDLEA suka yi da kuma goyon bayan masu ruwa da tsaki daban-daban akan shi al’amarin na yaki da shan muggan kwayoyi.
Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari akan nadin da yayi wa Birgediya-Janar mai ritaya. Muhammed Buba Marwa a matsayin sabon Shugaban hukumar ta NDLEA, ya kuma kara da cewar ba a dade da fara aikin shi sabon shugaban ba, har kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja
Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...