NDRC: Sin Na Da Kwarin Gwiwar Wanzar Da Matsayin Tattalin Arzikinta A 2022

Daga CRI Hausa,

Hukumar tsara manufofin sauye sauye da bunkasa ci gaban kasar Sin NDRC, ta ce Sin na fatan wanzar da matsayin ci gaban ta a fannin tattalin arziki a wannan shekara ta bana, ta hanyar kiyaye ginshikan samar da hajoji masu ingiza ci gaba mai karko, da sauran dabarun da za su dawwamar da nasarorin da ta samu cikin tsawon lokaci.

NDRC ta ce Sin na da karfin gwiwar wanzar da matsayin tattalin arzikin ta a shekarar nan ta 2022.

Da yake tsokaci kan hakan, kakakin hukumar ta NDRC Yuan Da, ya shaidawa taron manema labarai cewa, gwamnatin kasar Sin za ta gaggauta fitar da manufofi na hakika, wadanda za su bunkasa bukatun cikin gida, tare da nazartar muhimman matakai na ingiza ayyukan samar da hajoji a masana’antu. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version