Sanata Ali Ndume ya yaba wa dakarun sojin Nijeriya bisa daƙile wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai garin Gwoza a Jihar Borno.
Harin ya faru ne da safiyar Juma’a lokacin da ‘yan ta’addan suka shiga wani ƙauye da ke bayan fadar sarkin Gwoza.
- Marubutan Batsa Ku Ji Tsoron Allah -Emili
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Rahoton Hana Shettima Shiga Villa
Kwana guda kafin harin, Boko Haram sun kashe sojoji biyu da wasu fararen hula a ƙauyen Yamtake.
Sanata Ndume, wanda ya fito daga garin Gwoza, ya gode wa sojojin da sauran jami’an tsaro saboda ƙoƙarin da suka yi wajen fatattakar ‘yan ta’addan ba tare da asarar rai daga ɓangaren sojoji ko fararen hula ba.
Ya ce komai ya koma daidai a garin, inda harkokin kasuwanci da na yau da kullum suka ci gaba kamar yadda aka saba.
Gwoza dai tana daga cikin wuraren da Boko Haram suka mamaye a baya kafin sojoji su ƙwato ta.