Abubakar Abba" />

NECA Ta Jinjina Wa Gwamnati Kan Sabunta Tsarin Shigo Da Madara Nijeriya   

Kungiyar tuntuba na ma’aikata NECA ta kasa, ta yabawa Babban Bankin Nijeriya CBN cire wasu kamfanoni shida  daga cikin jeren sunayen kamfanonin da zasu shigo da madara  daga kasar waje zuwa cikin kasar nan.

A cikin sabon tsarin na babban bankin Nijeriya CBN, ya fitar a ranar talatar data gabata, babban bankin na Nijeriya ya haramtawa kamfanonin wasu kamfanonin shida shigo da madara daga kasar waje zuwa cikin kasar nan.

Kamfanonin sune, FrieslandCampina, WAMCO Nigeria, Chi Limited, TG Arla Dairy Products Limited, Promasidor Nigeria, Nestle Nigeria Plc da kuma Integrated Dairies Limited.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta  Timothy Olawale ne ya yi wannan yabon, inda ya ci gaba da cewa matakin na babban bankin Nijeriya CBN, yazo akan gaba kuma wata lamace da ke nuna cewa, Gwamnatin Tarayya a shirye take wajen kara farfado da fannin a kasar nan.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta  Timothy Olawale Olawale ya ci gaba da cewa, muna yabawa babban bankin Nijeriya CBN kan kokarin san a sabunta tsarin wanda a baya fannin na samar da madara ya ke daf da durkushewa a kasar.

Gwamnatin Tarayya a cikin watan Yulin shekarar 2019, ta dakatar da bayar da samar da kudaden musaya na kasar waje don shigo da madara daga kasashen aje zuwa cikin kasar nan, musamman ganin cewar, za’a iya samar da madarra mai dimbin yawa a cikin kasar nan da zata iya taimakawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Bugu da kari, babban bankin na Nijeriya CBN, ya bayyana cewa, shigo da madara daga kasar waje, ya kai daga dala biliyan 1.2 zuwa dala biliyan 1.5 a duk shekasra, inda babban bankin na CBN ya ya nuni da cewa, hakan ba ta taba sabuwa ba.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta Timothy Olawale Olawale Olawale hana kamfanonin shida shigo da madarar daga kasar waje, ya biyo bayan bukatar kungiyoyin kadago dake kasar nan kan yadda suka jima suna nuna damuwar su kan shigo da madarar cikin kasar nan.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta Timothy Olawale Olawale ya kuma yabawa kokarin babban bankin Nijeriya CBN kan yadda ya sanya aka kara yawan madarar da ake samarwa a cikin Nijeriya da kuma rabar da ita.

A cewar Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta  Timothy Olawale Olawale Olawale, akwai kuma bukar Gwamnatin Tarayya data tabbatar da tsari mai dorewa, musamman don a dinga zuba jari wajen yin kiwo, inda hakan zai kara bai wa masu sarrafa madara kwarin gwaiwar kara mayar da hankali a fannin.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta Timothy Olawale Olawale ya yi nuni da cewa, har ila yau, fannin kiwo ya na kuma samar da dimbin ayyukan yi ga alumma da kuma tarawa gwamnatin kudaden shiga.

Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta Timothy Olawale Olawale Olawale ya kuma shawarci Gwamnatin Tarayya data sanya a dinga tattaunawa da masana’antun dake samar da madara da ke a kasar nan da zata kara bunkasa fannin.

A karshe, Darakta Janar na kungiyar ta NECA Dakta Timothy Olawale Olawale yin hadaka zai kuma kara taimakawa wajen wanzar da tsari a fannin na samar da madara a kasar nan.

Exit mobile version