Muhammad Sani Chinade" />

NECAS Na Taka Rawa Wajen Bunkasa Noma A Yankin Arewa-maso-gabas, In Ji Hon. Nuhu Baba

Kungiyar nan da ke kula da bunkasa harkokin noma a yankin jihohin arewa-maso-gabashin kasar nan (NECAS), kungiya ce da ke taimakawa matuka gaya ga manoma ta fuskar samar musu rancen kudade da kayayyakin yin noma, kan ayyukan nata ne SANI GAZAS CHINADE ya samu tattaunawa da shugabanta na Jihar Yobe, HONARABUL NUHU BABA HASSAN. Ya fayyace irin rawar da kungiyar tasu ke takawa wajen bunkasa aikin gona. A sha karatu lafiya…

 

Yallabai ko za ka gabatar da kan ka ga masu karatu…

 

Sunana Hon Nuhu Baba Hassan shugaban kungiyar bunkasa aikin noma (NECAS) na yankin area maso gabas reshen Jihar Yobe.

 

Ko yaushe ne aka kafa wannan kungiya ta NECAS?

 

To ita dai wannan kungiya ta bunkasa aikin gona a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan wato NECAS an kafa ta ne a shekarar 2016 amma bunkasarta a shekarar 2018, kuma an kafa ta ne da manufar bunkasa aikin gona a wannan yankin na mu na arewa maso gabas ganin cewar, yankin ne da al’ummarsa ke fama da rikicin Boko Haram, hakan ta sa Shugabanmu Alhaji Sadik Umar Daware ya yunkura don assasa ta yadda al’ummomin yankin zasu amfana don rage wahalhalun da aka fuskanta, kuma Alhamdulillah.

 

 

Ko wane irin aiki ne wannan kungiya ta ku ta NECAS ta ke yi a wannan yanki?

 

To Alhamdulillah ita dai wannan kungiya ta mu, kungiya ce mai zaman kanta da ta samu sahalewar gwamnatin tarayya don habaka aikin noma a yankin arewa maso gabas yadda al’ummomin yankin za su amfana da shi musamman dake yankin yayi fama da iftila’in Boko Haram, kuma mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari run fil-azal ya amince da kafuwarta tare da hada mu da babban bankin kasa CBN don Samar da kudi ga kungiyar don gudanuwarta da zimmar bada rance ga manoman yankin na  arewa maso gabas wadda in sun girbe da kaka’a su biya wannan ne iron ayyukan kungiyar mu.

 

Yallabai, akwai wasu daga cikin manoman da ake zargin Cesar, in an basu kayayyakin noman maimakon su yi amfani da shi sai su sayar, ko me zaka ce ga ire-iren wadannan manoma?

 

A gaskiya mu a kungiyar mu iya kokarinmu don fadakar da jama’a cewa, wadannan kayayyaki ana ba su ne don gudanar da noma amma ba don Sayarwa ba, kuma mu kan fada musu wadannan kayayyaki ba fa kyauta bane rance ne za kuma su biya zarar kaka’a ta yi shi yasa ma muke aikin tare da wasu jami’an tsaron ‘yàn sanda wadda hakan ne ta sa ake gudanar ayyukan kungiyar cikin hali nagari.

 

Kuma ma ai muma matukar mun san wanda muka bada kaya sayarwa zai yi, to kuwa lalle ba za mu bashi wadannan kayayyaki ba saboda muna bayarwa ne don jama’a su amfana kamar yadda manufar kungiyar ta ke.

 

Ko akwai wani tsari da kuke da shi don bin diddigin kayayyakin da kuka baiwa manoma?

 

Alal hakika muna da wani tsari musamman ma a wannan kungiyar ta mu ta NECAS yadda muke amfani da malaman gona ta hannunsu muke bada wadannan kayayyaki don bayarwa ga manoman kasancewar in ka yi noma su za su rika zagawa don lura da gonar kowa sannan lokacin da amfanin gona yayi za su rika kawo mana rahoto kuma ko da an samu wani iftila’i dangane da yanayin damina, kungiyar da muka yi rijista da ita itace zata biya dukkan asarar da manomi yayi.

 

Bayan ba da rancen kudade ga manoma ko kukan bada rancen kayayyakin noma?

 

Tabbas mukan bada wash kayayyakin noma ga manoma don kara bunkasa shi ciki akwai Takin zamani, magungunan kashe ciyawa da kwari sai injunan ban ruwa da famfon feshi da kuma motocin noma tractors da makamantansu.

 

A sani na wannan kungiya ta Ku ta share akalla shekaru biyu tana gudanar da ayyukanta a jihar Yobe, to ko manoma kimanin nawa ne suka amfana?

 

To lalle a shekarar farko da shigowarmu wato 2018 kenan kimanin manoma 5002 ne suka noma Hekta 11,333 haka kuma a shekarar bara 2019 kimanin manoma 24,400 ne suka noma Hekta 58,380 anan jihar Yobe wato ninkin ba ninki na shekarar 2018 kenan.

 

A bana fa 2020 ko akwai wannan kudiri?

 

A bana ma mun gama dukkan wani shirye-shirye don’t bada irin wannan rance sai katsau iftila’in Cutar nan Cobid-19 ta shigo, shine muka jingine wannan kudiri namu, to amma Insha Allahu a yanzu ganin cewar, abubuwan sun yi sauki muna kokarin sake taso da wannan kudiri namu duk a cewar, a halin a ake ciki tunin damina ta yi nisa to amma duk da haka ba zamu yi kasa a gwiwa ba wejen aiwatar da wannan kudiri namu domin noman rani.

 

Yallabai ana samun korafe-korafe nan da can bisa ga yadda kuke bada rancen yadda wasu ke cewa basu samu, ko me zaka ce kan hakan?

 

To Alhamdulillah, in ka duba muna da ofisoshin mu a dukkannin kananan hukumomin Jihar 17 don haka duk wani mai korafi zai iya zuwa ofishin dake karamar hukumarsa don neman masalaha ko kuma ya zo kai tsaye wajen mu, kuma na hakkake matukar mutum ya cika dukkannin sharuddan bada wannan rance babu dalilin da zai sa a hana shi.

 

Wane kira kake da shi ga al’umma don sanin irin yadda kuke gudanar da ayyukan Ku a wannan kungiya ta Ku ta NECAS?

 

Ina kira ga jama’a da su san yanayin ayyukan mu musamman ma ganin cewar, ayyukanmu kwacakwam sun ta’allaka ne ga bunkasa aikin noma ta kowace fuska. Kuma ina kara jaddada cewar, ya kamata jama’a su sani cewar, mu kan bada rancen kayayyakin noma ne wadda kuma a karshen damina ko kuma da kaka’a mu kan tara rancen da muka bayar.

Kuma zuwan wannan kungiya ta NECAS ta samarwa manoma sauki matuka musamman yadda ta ke samar da kayayyakin gudanar da noma na zamani. Kuma ina Jan hankalin matasa da su rungumi aikin noma wurjanjan kamar yadda mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fada a kullum, haka nan shi ma jajirtaccen gwamnan mu Na Yobe Mai Mala Buni kan ba da.

Exit mobile version