Hukumar gudanarwa na hukumar shirya jarrabawar kammala sakandari ta Nijeriya (NECO) ta kaddamar da wani kwamiti mai karfi, wanda zai binciki zarge-zargen magudin jarrabawa da a ke yi kan wasu jami’anta da wata cibiyar zana jarrabawa tare da wasu daliban da su ka zana jarrabarwar kan batun satar amsa da magudin jarrabawa a bisa wani rahoton da wata kafa ta bankadowa.
Kafar talabijin ta Signature ta sake tare da fitar da wani faifan bidiyon da ta dauka a boye da ke nuna yadda a ke karya dokar gudanar da jarrabawa da tafka magudi a daya daga cikin cibiyoyin zana jarrabawar ta Fabian Kings and Kueens International School da ke Kabala ta yamma, a jihar Kaduna da ke da lambar zana jarrabawa ‘0140721’ da ke nuna yadda aka tafka magudin jarrabawa a yayin zana jarrabawar da aka kammala a baya-bayan nan na ‘2020 SSCE’.
A sanarwar manema labarai da jami’in yada labarai na NECO, Azeez Sani ya fitar, ya ce, sun gano makarantar da bidiyon ke nunawa tare da daukan matakan da suka dace kan batun.
A cewar sanarwar: “A bisa matsayar NECO na cewa ba za ta taba lamuntar kowani irin magudi da satar jarrabawa ba, cikin gaggawa ta dauki matakin hanzari kan cibiyar da aka gano tare da killace daliban gami da bincike kan takardun jarrabawar da suka zana,” a cewar Sani.
Ya ce, muddin aka tabbatar da abun da ake zargi to za su dauki matakin soke dukkanin jarrabawar da aka zana a wannan cibiyar nan take, “Dukkanin sakamakon jarawabar za a sokesu da zarar aka tabbatar da wannan zargin, sannan, makarantar za a daina kula da ita, su kuma jami’an da suke da hannu a lamarin za a gurfanar da su kamar yadda ke kunshe cikin sashin dokar zabe 33 na shekarar 1999,”
“Daga bisani, Hukumar NECO ta yaba da kokarin hukumar gudanarwa na gidan talebijin din Signature a bisa himmarsu na tsarkake badalaka a harkar jarrabawa, mu na rokon da fatan masu ruwa da tsaki za su yi koyi da hakan,” inji sanarwar ta NECO.