NECO Za Ta Kasance Amintacciyar Hukuma A Ko Ina Cikin Duniya – Farfesa Wushishi  

NECO

Shugaban hukumar shirya jarrabawa ta NECO, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi ya sha alwashin gyara hukumar NECO ta yadda za ta kasance karbabbiya hukumar shirya jarrabawa a ko’ina a fadin duniya. Farfesa. Wushishi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da yake amsar ragamar gudanarwar hukumar a hukumance daga hannun tsohon mukaddashin shugaban hukumar, Mista Ebikibina John Ogborodi.

 

Haka kuma sabon shugaban hukumar NECO ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki da kowa wajen ganin NECO ta kai mataki na ci gaba a karkashin kulawarsa.

 

“Babban burina shi ne in mayar da hukumar NECO da kasance ta amsu a ko’ina a fadin duniya ta yadda za ta yi kafada da kafada da duk wata hukuma da ke shirya jarrabawa a duniya, wannan shi ne burina ga hukumar NECO”.

 

A cewarsa, “ban zo wannan matsayi ba domin in nuna bambamci ko kadan, na kasance ne a wannan matsayi domin in yi aiki ga kowa da zai taimaka min wajen cika burina na bunkasa hukumar NECO,” in ji shi.

 

Shugaban hukumar ya ci gaba da bayyana cewa a tunaninsa a baya babu wasu matsaloli da zai fuskanta, amma a yanzu ya tabbatar cewa akwai babban kalubala a gabansa tare da neman goyan bayan dukkan jami’an hukumar domin magance matsalolin gaba daya.

 

Bugu da kari, shugaban hukumar ya nemi hadin kan mahukunta da jami’ai da su tallafa masa wajen ganin ya cika burinsa ga hukumar.

 

“Ina mai tabbatar wa daukacin ma’aikatan wannan hukuma cewa zai ba su goyan baya da gwarin gwiwa da suke bukata wajen gudanar da aiki yadda ya kamata, amma ku sani cewa karkashin shugabancina na wannan hukuma za a hukunta duk wani ma’aikaci da aka same shi yana sakaci da aikinsa,” in ji Farfesa Wushishi.

 

Ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammdu Buhari da ya zabe shi a matsayin shugaban NECO, yayin da ya yi alkawarin zai yi aiki kafada da kafada da ma’aikata ilimi ta tarayya da mahukuntan hukumar NECO.

 

Tun da farko dai, tsohon mukaddashin shugaban hukumar, Mista Ebikibina John Ogborodi ya bai wa Farfesa Wushishi cikakken rahoton a kan jarrabawar shekarar 2021 da sauran mahimman bayanai ga hukumar.

 

Idan dai za a iya tunawa, shugaban kasa Muhammdu Buhari ya nada Farfesa Wushishi a matsayin shugaban hukumar NECO a ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2021.

Exit mobile version