Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

NEDC Ta Bai Wa Matasa Tallafin Kayan Sana’a A Yobe

by Muhammad
February 19, 2021
in LABARAI
2 min read
NEDC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Maitela,

A kokarin ta na rage wa al’ummar jihar Yobe radadin matsalar tsaro, hukumar farfado da yankin arewa maso gabas (NEDC), ta gabatar da shaidar kammala samun horo ga matasa 134, kayan da za su fara sana’a hadi da naira 20,000 kowanen su- a karkashin shirin ta na horas da matasa na’orar sadarwa a jihar Yobe, ranar Alhamis.

samndaads

 

Bugu da kari kuma, hukumar ta raba wa makarantu a fadin jihar kayayyakin koyarwa hadi da kariya daga cutar korona, kayayyakin noma ga kungiyoyin manoma, tare da bai wa jami’an tsaro a jihar tallafi.

A jawabin sa na bude taron, wanda ya gudana a cibiyar al’adun gargajiya a birnin Damaturu, Manajan Daraktan hukumar NEDC, Mohammed G. Alkali ya bayyana cewa wannan tallafi ne a karkashin tsarin bunkasa hanyoyin sadarwa na zamani (ICT) a tafarkin hacaka ci gaban Nijeriya tare da farfado da tattalin arzikin yan kasa wanda ERGP su ka tsara, a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

“Wanda hukumar ci gaban arewa maso gabas (NEDC) ta kudurta aiwatar dashi tare da burin saukaka hanyoyin sadarwa a arewa maso gabas, saboda mu tafi kafada da kafada da sauran sassan kasar nan, ta wannan fannin.”

 

Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa, hukumar ta yi la’akari da muhimmancin hanyoyin sadarwa wajen samar da ci gaba cikin hanzari a fannin kimiyya da fasaha kana da zaburar da sha’anin ilimi da jawo bunkasar tattalin arziki.

 

“Sannan bisa dunkulalliyar manufa ta gaba daya, dangane da shirin hukumar NEDC wajen girka shirin bunkasa kafar sadarwa, shi ne domin samun saukin ta’ammuli da hanyoyin sadarwar a yankin arewa maso gabas tare da kokari wajen kasancewa hanyar dogaro da kai ga matasa kuma ya rage zaman kashe wando a wannan yanki.”

Haka kuma ya bukaci gwamnatin jihar Yobe a karkashin Gwamna Mai Mala Buni ta basu cikakken goyon baya tare da bai wa wadannan matasan maza da mata kwarin gwiwar samar musu da muhalli na musamman domin fara gudanar da sana’o’in da suka koya.

 

Kayayyakin da hukumar ta raba a matsayin tallafin, sun kunshi kyallen rufe fuska (face mask) na musaman 10,000 domin kananan makarantun gwamnati, karin 5,000 ga makarantu masu zaman kansu tare da wasu 4,000 ga jami’an tsaro daban-daban a jihar.

 

Sauran sun kunshi sinadarin kashe kwayoyin cutar korona (hand sanitizer) 2,000, na’urorin auna zafi, domin gano masu dauke da korona (Thermometer) 100 wanda za a raba su ga makarantun firamare tare da karin wasu kyallayen rufe fuska 5,000 ga kungiyar direbobi ta Nijeriya (NURTW).

 

“Har wala yau, kari dangane da hakan, wannan hukumar ta fadada tallafin a harkokin ilimi a wannan jihar, ta hanyar bayar da tallafin barguna 10,000 ga makarantun kwana na gwamnati, littafan rubutu 60,000 wanda makarantu masu zaman kansu suka samu taafin littafan rubutu 20,000.”

 

A nashi bangaren, babban bako a wajen taron, Gwanna Mai Mala Buni, wanda sakataren gwamnatin jihar Yobe(SSG), Baba Malam Wali ya wakilta, ya bukaci wadanda su ka ci gajiyar tallafin su yi amfani dashi ta hanyar da ta dace, a hannu guda kuma ya yaba da kokarin hukumar NEDC.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Bauchi Ta Rushe Gidan Da Aka Samu Tarin Alburusai 1,000

Next Post

Zaman Lafiyar Nijer Shi Ne Na Nijeriya – Buhari

RelatedPosts

Saura Wata Biyu Buhari Ya Dawo Da Zaman Lafiya –Sanata Lawan

by Muhammad
3 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad...

Sojoji Sun Sake Kwato Garin Marte A Borno

Sojoji Sun Sake Kwato Garin Marte A Borno

by Sulaiman Ibrahim
12 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Sojojin Nijeriya a yammacin yau, da misalin...

Gwamnatin Bauchi Ta Raba Keke-Napep 1,000 Don Bunkasa Zirga-zirga

Masu ‘Adaidaita Sahu’ Sun Janye Yajin Aikin Da Suka Shiga A Kano

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Kungiyar masu 'Adaidaita sahu' ta Kano ta...

Next Post
Zaman Lafiyar

Zaman Lafiyar Nijer Shi Ne Na Nijeriya – Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version