Connect with us

SIYASA

Neja Za Ta Yi Anfani Da Dokar Hana Bangar Siyasa A Lokacin Zabe

Published

on

Zabe na karo na biyu ya dogara ne a hannun jama’a, domin zuwa wannan majalisar ya ta’allaka ne goyon bayan da na samu daga al’ummar karamar hukumar Chanchaga. Dan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar karamar hukumar kuma shugaban majalisar dokokin, Rt. Hon. Marafa Ahmed Guni ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Dadin Kowa Multipopuse Cooperatibe a ofishin sa da ke harabar majalisar na tunawa da marigayi Haliru Dantoro da ke minna.
Marafa yace batun zaben 2019 abu ne daga Allah, domin amincewar jama’a na irin wakilcin da muka bayar ne zai sake ba mu karfin niyya, in ba hukuncin Allah ba, irin Marafa bai is a ya hau wannan kujerar ba, shekaru da dama an danne talaka, yanzu lokaci da talakawa zasu fito dan damawa da su a harkokin siyasar kasar nan.
Da ya juya kan masu korafi akan ake tafiyar da mulki a kasar nan kuwa, sai yace in har zamu iya jure shekaru sha shida cikin ukuba, ban ga dalilin da ba zamu jurewa shekaru uku zuwa hudu na gyara da ake yi ba yanzu, dan haka idan kun ba mu goyon baya da yardar Allah da mu za a sake fafatawa 2019.
Yace maganar bangar siyasa, lokaci yayi da gwamnatin jiha ta kafa doka kan bangar siyasa, nan gaba kadan duk matashin da ka yiwa maganar bangar siyasa ba za ka yi marmarin maimaita mai wannan kalmar ba.
Da yake karin haske ga kakakin majalisar, kodinetan kungiyar ta jiha, Sani Aliyu PRO, yace kungiyar Dadin Kowa ta sanya dan majalisar akan sikeli kuma ya zagaya mazabu goma sha daya da ke karamar hukumar Chanchaga, ta ga irin ayyukan da dan majalisar ya gudanar wanda ya zama wajibi su kara tashi haikan dan wayar da kan jama’a irin mutanen da ya kamata a zaba a zabe mai zuwa.
Yace aikin na su bai tsaya nan ba, yanzu lokacin da aka kara wa’adin karban katin zabe, kungiyar su ta tashi haikan wajen wayar da kan jama’a muhimmancin katin zaben tare da sanya idanu cibiyoyin da aka ware dan karban katin, kungiyar wadda uwa ce ga wasu kungiyoyi sa kai da suka hada da yarbawa da inyamurai ta sha alwashin marawa dan majalisar baya tare da alkawalin tashi tsaye wajen wayar da kan jama’a muhimmancin dawowarsa kan wannan kujerar wanda a tarihin siyasar jihar karamar hukumar Chanchaga ba ta taba rike kujerar shugabancin majalisar ba sai a wannan lokacin.
Da yake karin haske da neman alfarmar, shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Danlami Sabo ya jawo hankalin dan majalisar da ya tabbatar duk ranar da ya zartar zai kaddamar da kan shi a matsayin dan takara karo biyu a tabbatar an yi shi a unguwar makera wadda ke tsakiya garin minna, shugaban yace su mutanen makera suna godiya da dan majalisar akan samarwa ‘yan asalin yankin gwamnati wadanda su ba kowa ba ne face ‘yayan talakawa.
Hon Marafa ya tabbatar wa kungiyar da cewar ba zai yi kasa a guiwar ba wajen ganin duk wani abu da suke bukata na cigaban kasa musamman karamar hukumar Chanchaga zai tsaya tsayin daka da aljihuna shi da lokacin shi dan ganin abin nan ya samu. Kungiyar dai ta gabatar wa dan majalisar kyautar risho kirar hannu wadda ta ke muradin rabawa matan aure na cikin gida dan saukaka masu a harkokin girke girke, ta kuma jawo hankalin dan majalisar da ya yi anfani da matsayin sa na ganin an samar da dokar da za ta takaita anfani da kudi a lokacin zabe kasancewar sa shugaban kungiyar shugabannin majalisun dokoki a bangaren Arewa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: