NEMA Ta Raba Kayan Abinci Ga ‘Yan Gudun Hijirar Jihar Neja

Daga Mahdi M. Muhammad,

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta fara raba kayayyakin tallafi ga gidaje 24,925 na ‘yan gudun Hijira (IDP) da ‘yan bindiga suka addaba a kananan hukumomi 14 na jihar Neja.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Manzo Ezekiel, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar a ranar Alhamis a Abuja.

Air Vice Marshal Muhammadu Muhammed (mai ritaya), Shugaban NEMA wanda Hajiya Zainab Saidu, Shugabar ofishin Minna na hukumar ta wakilta ta kaddamar da rabon kayayyakin a Kuta, karamar hukumar Shororo.

Sauran kananan hukumomin sun hada da, Rafi, Shiroro, Bosso, Munya, Paikoro, Mariga, Kontagora, Magama, Mashegu, Wushishi, Rijau, Borgu, Lapai da Labun.

A cewarsa, kayayyakin agajin sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Neja da sauran su don samar da agaji ga mutanen da abin ya shafa.

Ya kara da cewa, bayan tantancewar hadin gwiwa da NEMA da gwamnatin jihar suka gudanar kwanan nan, an gano cewa ‘yan gudun hijirar na bukatar tallafin abinci.

“A kan wannan ne aka samu amincewar shugaban kasar da kuma abubuwan da ake bukata wadanda suka hada da buhunan shinkafa buhu 5, 412, kilo 5,412 na wake 10, lita 500 na man kayan gyada, katun 500 na kayan dandano da buhu 500 na gishiri ga masu amfani,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “za a rarraba kayayyakin ne kai tsaye ga mutanen da abin ya shafa a sansanonin da kuma wuraren da ke karbar bakuncin ta hanyar NEMA tare da hadin gwiwar jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja.”

 

Exit mobile version