NEMA Ta Sake Karbar ‘Yan Nijeriya 116 Daga Libya

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nijeriya wato NEMA, ta ce ta sake karbar ‘yan Nijeriya 116 daga kasar Libya wadanda suka amince su dawo Nijeriya.

Mukaddashin Hukumar na ofishin Legas, Ibrahim Farinloye, shi ne ya karbi ‘yan Nijeriyar a madadin Daraktan NEMA din, Mustapha Maihajja.

Farinloye ya ce ‘yan Nijeriyar sun iso ne ta ‘Cargo Wing’ dake filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas da daren ranar Laraba.

A cewarsa, an dawo da su ne ta jirgin ‘Al Buraq Air Boeing 737’ mai dauke da lamba UZ 188/26 da lambar rijista ta 5A-DMG-MJI.

Ya tabbatar da cewa an yi nasarar dawo da su ne tare da hadin guiwar IOM da AVR da kungiyar tarayyarv Turai da sauran su.

 

Exit mobile version