Neman Tallafi Da Sunan Sojoji: Rundunar Soja Na Neman ‘Brimah’ Ruwa A Jallo

Rundunar Sojin kasar nan ta ce tana yin aiki tare da hukumar ‘yan sandan Duniya domin cigito Dakta Perry Brimah, wani dan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje, wanda ake nemansa a kan kafa wata gidauniya ta Duniya domin samawa Sojoji abinci a yankin arewa maso gabas.
Sanarwar ta ce, “Wani mai aikata laifuka” mai suna Brimah, ya kafa abin da ya kira da”Gidauniyar Duniya domin samawa Sojojin da suke fafatawa da Boko Haram abinci.”
Kakakin rundunar, Birgediya Janar Sani Usman, ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba, inda ya nemi al’umma da su bayar da bayanai a kan duk inda suk tsammanin dan damfarar yake.”
“Dan damfarar yana amfani da wannan shafin ne a wajen ayyukan damfarar na shi https://www.gofundme.com/feed-nigerian-soldiers/info @ ENDS.ng Tel: +1-929-427-5305; Whatsapp: +234-903-420-3031.
“Muna bayyanawa kowa, Sojojin Nijeriya da ke aiki a sashen arewa maso gabas ko ma duk ko’ina, ba su rasa ababen bukatar su ba kamar yanda dan damfarar yake kokarin nunawa.
A cewar sa, babu wani Sojan da ya taba kokawa a kan rashin abinci ga Sojojin da har zai kai su ga shiga matsi na yunwa.
“Duk wanda ya yarda ya fada tarkon wannan macucin, ya yi hakan ne a bisa zabin kansa,” in ji shi.

Exit mobile version