Rabiu Ali Indabawa" />

Netanyahu: Ana Dab Da Kammala Bincike Kan Zargin Cin Hanci

Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na fuskantar bincike na karshe, kafin a cimma matsaya kan ko za’a gurfanar da shi a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Sai dai duk da haka lauyoyinsa za su yi kokarin shawo kan ministan shari’a na kasar kada ya ci gaba da yunkurin samun Firai Ministan da laifin cin hanci da zamba da kuma cin amana har sau uku.

Ana zargin Mista Netanyahu da karbar kyauta daga hannun wani attajiri da kuma yi wa mutane alfarma domin a yabe shi a kafafen yada labarai.

Amma ya musanta yin wani ba daidai ba.

Ana tsammanin ministan shari’ar zai yanke shawara a karshen watan Disamba.

Binciken ya zo ne sama da makonni biyu da kammala babban zaben kasar karo na biyu, a wannan shekarar ba tare da an samu wanda ya yi nasara ba.

Shugaban kasar ya bukaci Mista Netanyahu da ya kafa gwamnatin hadin guiwa, sai dai tattaunawa da jam’iyyar Likud mai ra’ayin rikau da Centrist Blue da kuma White Alliance ta abokin hamayyarsa ta ci tura.

Me zai faru a wajen binciken?

A hukumance wata babbar tawagar lauyoyi 12 ne za su kare Mista Netanyahu kan zarge-zargen cin hancin da ake masa wadanda kuma suka mamaye shekarun da yayi na baya-bayan nan a matsayinsa na Firai Minista.

Za a kwashe tsawon kwanaki hudu ana sauraron bahasi zuwa ranar Litinin mai zuwa.

Haka kuma za a yi zaman binciken ne a ma’aikatar shari’a da ke birnin Kudus a gaban ministan tsaro.

Firai Ministan ba zai halarci zaman binciken ba, amma ya fito karara ya musanta aikata wani ba daidai ba, yana mai cewa abokan adawarsa masu ra’ayin kawo sauyi da kuma kafafen yada labarai ne ke yi masa bi-ta-da-kulli.

“A yau za mu gabatar da duka shaidar da muke da ita wadanda kowa ya sani da ma wasu sabbi,” Amit Hadad, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Netanyahu ya shaida wa ‘yan jarida a wajen ma’aikatar shari’a.

Me zai faru idan aka samu Netanyahu da laifi?

Ana daukar Mista Netanyahu a matsayin wanda bai aikata laifi ba har sai an tabbatar da cewa ya aikata abubuwan da ake zarginsa da su. A don haka babu wani abu da zai hana shi ci gaba da rike mukaminsa, idan har a watan Disamba ministan tsaron ya yanke hukuncin gurfanar da shi a kan tuhume-tuhumen uku.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce mutane da dama ne za su dora ayar tambaya kan cancantarsa na kula da al’amuran kasar a yayin da yake kare kansa a kotu.

Abokin hamayyarsa Mista Gantz, ya yi alkawarin ba zai yi aiki tare da Fira Ministan da ake tuhuma da aikata manyan laifuka ba.

Exit mobile version