Muhammad Awwal Umar">

NEWMAP Ta Tallafa Wa Mutum 164 Da Kayan Anfanin Gona

Hukumar kula da zaizayar kasa karkashin ma’aikatar muhalli ta jihar Neja, ta tallafawa al’ummomi 164 daga yankunan kananan hukumomin jihar da tsirrai dan kare muhalli da samar da ayyuka ga jama’a.
Tunda farko da yake bayani ga al’ummomin, kodineta mai kula da ayyukan hukumar, Alhaji Usman Garba Ibeto, yace sun kirkiro wannan shirin ne dan samar da ayyuka ga jama’a musamman ganin yadda zaizayar kasa ke barazana a wasu sassan jihar, da ya zama dole a dauki matakin horar da jama’a muhimmancin dasa itatuwa wanda zai ba su kwarin guiwar kare muhallan su.
Abinda mu ka yi yanzu mun horar da jama’a yadda ake renon tsirrai ta yadda za su samu abin yi, bayan nan mun kafa wuraren musamman da ka baiwa jama’a kwarin guiwa yadda za su iya renon tsirrai ta hanyar ba su tsirrai da gina masu ofisoshi har da gina rijiyuyi da fanfon tuka-tuka ta yadda za su samu kwarin guiwar cigaba da wannan shirin.
Mun ba su damar rainon tsirrai da sayar da shi ga masu bukata dan cigaba da rainon wadannan kananan gidan gonar da muka assasa masu, abinda mu ke bukata bayan sun raini tsirran suna da damar nemo wasu tsirran da suka ga jama’a na bukata dan cigaba da fadada wajen, ta yadda jama’a zasu iya zuwa saye dan shukawa a gidajen su dan anfanin yau da kullun, wanda zai taimaka wajen samun kudaden shigar yau da kullun da kuma baiwa jama’a aikin yi.
Ba mu bar su kara zube ba, mun samar da jami’an da ke sanya ido dan taimaka masu da shawarwari da kuma tabbatar da shirin bai samu koma baya ba, ta yadda za su iya samun kwarin guiwar rike wannan shirin hannu biyu.
Duk wannan aikin na gudana ne a karkashin bankin duniya bisa kulawar ma’aikatar muhalli ta jiha, wannan shirin ya shafi hekta talatin da uku da muka ware a yankunan kananan hukumomin Kontagora, Bida da Lapai, Bosso, Rijau da Magama.
Bayan nan mun zabi makarantun sakandare guda biyu a yankuna uku na jihar da za mu gina masu gidan gona hekta daya a kowace makaranta.
Shirin NEWMAP, shirin babban bakin duniya ne na tsawon shekaru takwas, amma Neja ba ta samu damar shiga shirin kan lokacin da aka fara shi sai bayan shekaru biyar da farawa, amma duk da hakan muna kàn gaba.
Mun gabatar da ayyuka guda shida amma zuwa yanzu aiki daya muka samu na aikin Rafin-gora, wanda yanzu muna sa ran ayyuka guda biyar, biyu a cikin garin Minna, daya a Babban Rami cikin karamar hukumar Mashegu, Lapai da Suleja.
Iraruwan da muka shuka sun kunshi, gwaiba, mangwaro, lemu da ayaba da sauran cimakan yau da kullun.
Da yake bayani, kwamishinan muhalli, Barista Zakari Tanko a ta bakin babban sakataren ma’aikatar, Mista Lucky Barau, yace ma’aikatar za ta cigaba da baiwa hukumar goyon baya domin ayyukanta abin a yaba ne.
Daga cikin ayyukan hukumar da gwamnatin jiha ke alfahari da su da hukumar ta gudanar zuwa yanzu, akwai rijiyoyin da ta gina a kananan gidajen gona ga mutane dari da sittin da hudu, sai fanfon tuka-tuka mai anfani da hasken rana guda bakwai, da lantarki mai anfani da hasken rana guda hudu, sai aikin gada da magudanan ruwa na garin Rafin-gora da zai lashe biliyoyin naira da ke gudana yanzu haka.

Exit mobile version