Abba Ibrahim Wada" />

Neymar Ba Zai Buga Wasan Barcelona Da PSG Ba

Dan wasan gaba na kungiyar kwalon kafa ta Paris Saint German, Neymar, ya samu rauni wanda hakan yasa ba zai fafata wasan cin kofin zakarun turai ba da kungiyar zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a mako mai zuwa.
Neymar yaji ciwo ne a wasan daya buga a gasar rukuni-rukuni na kasar Faransa kuma likitocin kungiyar sun bayyana cewa dan wasan zai iya yin makonni hudu yana jiyya kuma ya fita daga cikin jerin ‘yan wasan da zasu fafata da Barcelona.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka tabbatar da cewa dan wasa Angel Di Maria ya samu ciwo kuma ba zai fafata wasan farko ba da kungiyoyin zasu fafata sai dai ana ganin zai buga wasa na biyu.
Shima dan wasan kungiyar Barcelona Philliph Coutinho ba zai fafata wasannin da kungiyoyin biyu zasu buga ba sakamakon ciwon daya samu a kwanakin baya sai dai daman ya dade yana jiyya kuma Barcelona ta saba buga wasa babu shi sannan shima dan wasa Ansu fati har yanzu babu tabbas din ko zai iya buga wasan.
A kwanakin baya ne tauraron dan wasan ya rattaba hannu kan kara wa’adin zamansa tare da kungiyar da tsawon shekaru hudu, abinda ke nufin sai a shekarar 2026 za su gari musamman idan kungiyar tana kokari.
Kafin matakin na Neymar dai, an sha alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, la’akari da cewar, yayi jinkirin tsawaita wa’adin yarjejeniyar sa da kungiyar ta PSG da ke shirin karewa a shekarar badi ta shekara ta 2022.
Tun bayan sauyin shekarsa zuwa gasar League 1 ta kasar Faransa a shekarar 2017 daga La Liga, Neymar ya taimakawa PSG wajen lashe kofuna 9 a Faransa, ciki har da na gasar ta League 1 guda 3.
A shekarar data gabata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona taso daukar dan wasan sai dai daga baya kuma PSG ta bayyana cewa ba zata sayar da dan wasan ba duk da cewa tana bukatar kudin kashewa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.
Neymar dai yasha bayyana burinsa na barin kungiyar sakamakon gazawar kungiyar wajen lashe gasar cin kofin zakarun turai wanda hakan yasa kungiyar tayi masa alkawarin cewa zata sayo manyan ‘yan wasan da zasu iya lashe mata kofin.
Sabuwar yarjejeniyar da Neymar ya sanya zata sanya manyan ‘yan wasa su koma kungiyar ciki hard a Messi wanda kungiyar take zawarci bugu da kari dan wasa Kylian Mbappe ana zaton zaia mince ya ci gaba da zaman kungiyar.

Exit mobile version