Daga Umar Muhsin Ciroma
Kocin Paris St-Germain, Unai Emery ya ce zai shiga tsakanin Neymar da Edison Cabani, idan sun kasa sasanta wa a tsakaninsu kan wanda ya kamata ya buga wa kungiyar fenariti.
‘Yan wasan biyu sun yi takaddama kan wanda ya kamata ya buga wa kungiyar fenariti a karawar da PSG ta ci Lyon 2-0.
Daga baya Neymar ya hakura ya bar wa Cabani, inda shi kuma ya buga amma bai ci kwallon ba.
PSG ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburi ne, bayan da ta ci kwallo biyu da ‘yan wasan Lyon suka ci gida.