Neymar Da Emery Sun Yi Faɗa

Daga Abba Ibrahim Wada

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, Neymar jr da mai koyar da yan wasan ƙungiyar, Unai Emery sunyi fada a ranar Alhamis a filin ɗaukar horo.

Rahotan ya bayyana cewa mai koyar da yan wasan ƙungiyar ne yace a tashi daga ɗaukar horo da wuri saboda yan wasan ƙungiyar sun gaji sakamakon buga wasan zakarun turai da sukayi.

Sai dai matakin da Emery ɗin ya ɗauka baiyiwa Neymar dadi ba inda ya dauki robar ruwa ya buga ajikin wani bango saboda baiji daɗin abin ba.

Sai dai mai horar da yan wasan ƙungiyar ya nuna rashin jin daɗin da halin da Neymar ɗin ya nuna inda yace yana ƙoƙarin raba masa kan yan wasa.

A kwanakin baya ma dai an samu rashin jituwa tsakanin Neymar ɗin da ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Edinson Caɓani akan bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan da ƙungiyar ta samu Caɓani ya ɗauka zai buga Neymar yace shine yakamata yabuga.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG dai ta siyo Neymar ne daga Barcelona akan kudi fam miliyan 200 kuma zuwa yanzu yaci ƙwallo tara sannan ya taimaka anci ƙwallo bakwai cikin wasanni goma daya buga a ƙungiyar.

Ana tunanin dai ƙungiyar za ta iya rabuwa da mai koyar da yan wasan ƙungiyar bayan da rahotanni suka bayyana cewa ƙungiyar tanason dakko Mourinho daga Manchester united.

Exit mobile version