Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar Jnr ya rattava hannu kan kara wa’adin zamansa tare da kungiyar da tsawon shekaru hudu, abinda ke nufin sai a shekarar 2026 za su gari.
Kafin matakin na Neymar dai, an sha alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, la’akari da cewar, yayi jinkirin tsawaita wa’adin yarjejeniyarsa da kungiyar ta PSG da ke shirin karewa a shekarar badi ta shekara ta 2022.
Tun bayan sauyin shekarsa zuwa gasar League 1 ta kasar Faransa a shekarar 2017 daga La Liga, Neymar ya taimakawa PSG wajen lashe kofuna 9 a Faransa, ciki har da na gasar ta League 1 guda 3.
A shekarar data gabata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona taso daukar dan wasan sai dai daga baya kuma PSG ta bayyana cewa ba zata sayar da dan wasan ba duk da cewa tana bukatar kudin kashewa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.
Sabuwar yarjejeniyar da Neymar ya sanya zata sanya manyan ‘yan wasa su koma kungiyar ciki hard a Messi wanda kungiyar take zawarci bugu da kari dan wasa Kylian Mbappe ana zaton zaia mince ya ci gaba da zaman kungiyar.
A satin daya gabata ne dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Leandro Paredes, ya ce kungiyar sa ta soma shirye-shiryen kulla yarjejeniya da kaftin din Barcelona Lionel Messi, mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya guda 6 domin ganin ya koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
A karshen kakar wasa ta bana ne dai yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar wanda har sai da shugaban gudanarwar kungiyar Jose Maria Bartemeu yayi murabus daga kujerarsa sakamakon matsin lamba.
Tun kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron dan wasan domin ganin ta kulla yarjejeniya dashi.