Abba Ibrahim Wada" />

Neymar Yana Son Komawa Barcelona – Cewar Mataimakin Shugaban Barcelona

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain, Neymar na son ya sake komawa kungiyar domin ya cigaba da buga wasa in ji mataimakin shugaban kungiyar ta Barcelona sai dai kuma Jordi Cardoner ya ce ba su tuntubi juna ba da Neymar, wanda ya yi kaka hudu a Barcelona.

Dan wasan tawagar Brazil, mai shekara 27, bai samu sakin jiki ba a PSG tun komawarsa Faransa a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya bayan ya koma PSG a shekara ta 2017 kan kudi fam miliyan 200, a matakin wanda aka dauka mafi tsada a fagen kwallon kafa a duniya.

Cardoner ya bayyana hakane a wajen ganawa da ‘yan jarida cewar ana ta rade-radin inda Neymar zai koma da buga wasa a bana idan dan wasan zai bar PSG wadda shugabanta yace a shirye yake daya rabu da Neymar din.

Sai ya kara da cewar akwai yi wu war Neymar na son komawa Barcelona amma Barcelona bata tunanin sake daukar dan wasan ko zama don tattauna batun koda dan kwallon ko kuma da PSG saboda basu shirya sayansa ba a bana.

Neymar ya lashe kofin Ligue 1 na kasar Faransa sau biyu a PSG, inda ya ci kwallo 34 a wasa 36 da ya buga a Faransa sai dai dan kwallon na cin karo da cikas, inda ake rade-radin cewar ana yin fada da shi a dakin sauya kayan ‘yan dwallo karo da dama, da dakatar da shi da aka yi kan dukan dan kallo da cin zarafin alkalan wasa.

Wani rahoto a kasar Spaniya na cewar dan wasan na Brazil ya bukaci a zabtare Yuro miliyan 12 a kudinsa a shekara, domin ya samu damar koma wa Barcelona da buga wasa saboda baya bukatar sake kasancewa da PSG a kakar wasa mai zuwa.

Ana sa ran Antoine Griezmann zai koma Barcelona daga Atletico Madrid kan Yuro miliyan 120, yayin da Frenkie de Jong tuni ya koma kungiyar kan Yuro miliyan 75 daga Ajad sai kuma mai tsaron raga Neto daga Balencia, wanda ya koma Barcelona akan kudi fam miliyan 26.

Exit mobile version