Neymar Zai Iya Komawa Real Madrid ­– Marcelo

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Marcelo JR, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar zai iya komawa Real Madrid nan gaba kuma zai buga abin azo agani idan yakoma kungiyar.

Marcelo, ya bayyana hakane a hir

arsa da manema labarai a shirye-shiryen da kungiyarsa takeyi na kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German wadda Neymar din yake bugawa wasa a Ranar Laraba a filin wasan na Santiago dake birnin Madrid.

Tun bayan da dan wasan yakoma kungiyar ta PSG rahotanni suka bayyana cewa dan wasan yafara takun saka da wasu daga cikin yan wasan kungiyar ciki har da dan wasa Edinson Cabani da mai koyar da yan wasan kungiyar, Unai Emery.

Marcelo yace Neymar kwararren dan wasa ne kuma gogagge wanda kowacce kungiya zataso ace yana buga mata kwallo sai dai abune mai wahala samun irin wannan dan wasa sakamakon idan aka sakashi a kasuwa kowacce kungiya mai karfin tattalin arziki zata taya dan wasan.

Sai sai yace yanayin buga kwallon sa zata dace data Real Madrid wanda hakanne yasa yake ganin idan yakoma kungiyar zaiji dadin buga wasa da ragowar yan wasan kungiyar.

Neymar dai yakoma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German daga kungiyar Barcelona akan kudi fam miliyan 200 wanda hakan yasa yafi kowanne dan wasa tsada a duniya kuma tafi kowanne dan wasa karbar albashi a duniya.

Real Madrid da PSG dai zasu buga wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris din wata mai kamawa bayan buga wasan farko da zasu fafata a ranar Laraba.

Exit mobile version