NGF Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-Kashen Filato

Kungiyar Gwamnoni ta Nijeriya wadda aka fi sani Nigeria’s Gobernor’s Forum [NGF]  ta yi Allah wadai da kashe-kashen dimbin mutanen da ba su san hawa bare sauka a rikicin Fulani Makiyaya da ‘yan kabilar Birom a cikin Kananan hukumomin Jos ta Kudu, Riyom da kuma Barakin Ladi da ke cikin Jihar Filato.

Gwamnonin sun yi wannan tir da hakan ne a lokacin da suka kawo wa gwamnan jihar ziyarar jaje bisa dimbin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar shi rikicin.

Gwamnonin wadanda shugabansu Gwamna Abdul Aziz Yari na jihar Zamfara ya jagoranta zuwa gidan gwamnatin jihar [Little- Rayfield Jos], a makon da ya gabata sun tabbatarwa Gwamna Simon Bako Lalong, na jihar samun cikakken goyon bayan su da kuma hadin kansu,  don ya samu kwarin guiwar aiwatar da kyawawan manufofin sa na maido da cikakken zaman lafiya a jihar.

Gwamnonin wadanda suka hada da na Bauchi Nasarawa, Binuwai, Sokoto da Imo, sun ja-jantawa gwamnatin  Filato, Iyalan wadanda suka rasu da  kuma daukacin al’ummar jihar da kasa baki daya bisa ga shi rashin da aka yi.

Da yake magana a madadin Gwamnonin, Gwamna Abdul Aziz Yari,  wanda ya nuna damuwar sa bisa asarar rayukan da aka yi lokacin rikicin yace, Gwamnonin sun kudurin aniyar yin aiki tare da shugabannin rundunar tsaro don gano musabbabin rikicin da wadanda suke assashi, don yin maganin aukuwar su nan gaba.

Shima da yake tofa albarkacin bakin sa Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi  kira ne ga al’ummar kasarnan da su hada kansu da Jami’an tsaro don suyi aiki tare wajen gano irin mutanen da suke haddasa wadannan rikice rikicen don a samu hanyoyin magance su.

Exit mobile version