Inshorar lafiya ta kara (NHIS) ta bayyana cewa, ta samu nasarar dawo da kudade na naira biliyan biyu daga hukumar kula da lafiya (HMO), kudaden kayayyakin kula da lafiya wacce ba ta biya ba. Shugaban NHIS, Mohammad Ghali shi ya bayyana hakan lokacin wani taron kara wa juna sani wanda ya gudana a Jihar Kono. Ghali ya bayyana cewa, sun amsa korafe-korafe dama daga masu gudanarwa a kan rashin biyan kudaden da hukumar HMO da ta yi ba, wanda yarjejeniya ne da aka kulla a tsakanin HMO da masu samar da kayayyakin lafiya, inda hukumar ta kasa biyan su kudadensu har na naira biliyan biyu.
“Sakamakon rashin biyan kudaden, hukumar NHIS ita ce saida a karkashin shugabancin Farfesa Nasiru Sambo, an dai samu korafe-korafe da dama daga hannun masu gudanarwa a harkokin lafiya wadanna suke bin wannan kudade. A wannan korafe-korafe da suke samu wanda ya yi yawa har sai da ya fusata mu a wasu lokuta. A duk lokacin da muka tambaya sai a dunga ba mu amsar cewa, sun gudanar wa HMO ayyuka ne amma ba su biya ba. Wannan abubuwa ne wadanda ba su dace ba.
“Sakamakon haka ne ya sa hukumomi suka dauki matakan da suka dace a kan rashin. Mun bullo da wasu ka’idoji wanda zai ba mu damar tattaunawa wajen amsar dukkanin ba shi a bangaren lafiya tun daga shekarar 2019 har zuwa yau.
“Mun gayyaci HMO a kan su biya basukan da ake bin su a bangaren harkokin lafiya da masu gudanarwa. Ba mu saka bashin da aka yi ba a tsakanin watan Yuni da na watan Yulin shekarar 2020. A cikin watan Satunmbar shekarar 2020, rahoton da muka samu daga jiha cewa, akwai bashin biliyan biyu da HMO ba su biya ba na kayayyakin harkokin lafiya wanda aka kawo musu. Daga baya sun biya bashin wanda aka ba su wasikar wanda ke nuna sun biya ba shin.
Shugaban NHIS, Mohammad Ghali ya bayyana wasu sababbin tsare-tsare da hukumar ke shirin aiwatarwa wadanda suka hada da shirin inshorar lafiya na zamantakewar iyali, wanda zai hada da mutane da dama domin kulawa da kiwon lafiyarsu.