NHRC Da HURIDAC Sun Kaddamar Da Binciken Take Hakkin Dan Adam A Zaben 2019

Hukumar kare hakkin dan adam ta, (NHRC) tare da hadin gwiwar hukumar kare hakkin dan adam ta, (HURIDAC), sun kaddamar da rahoto a kan binciken su kan take hakkin dan adam a wannan shekarar ta 2019.
Da yake magana a wajen taron babban Sakataren hukumar, Mista Tony Ojukwu, ya ce, rahoton ya yi bincike ne a kan yanda zabe ya gudana a Nijeriya, sai ya bayar da karin haske a kan matsayin hakkin dan adam kamar yanda dokar Duniya ta nuna.
“Wannan rahoton an shirya shi ne domin ganin an tabbatar da abin da al’umma ke bukata a wajen zabe, kafin a tabbatar da zaben ya gudana ta fuskacin gaskiya da adalci a Nijeriya.
“Rahoton kuma ya yi nuni a kan hadarin da ke cikin rigingimun zabe a zaben Nijeriya na 2019, inda ya mayar da hankali a kan yawaitan kashe-kashe, raunata mutane da kuma lalata dukiyoyin al’umma.
“Hakanan da batun yanda ake siyan kuri’u da makamantan su, rahoton kuma ya bayar da shawarwari ga hukumomi da masu ruwa da tsaki wajen taimakawa matakan zaben domin gujewa hadurran.
A cewar Ojukwu, rahoton ya nuna yawan lalata dukiyoyi ya yi kamari zuwa sama sosai da kashi 37, na jimlar alkalumman zaben, raunuka kashi 25, sa’ilin da mace-macen da ke da dangantaka da siyasa suke kashi na 19.
Ya ce, a cewar rahoton, jimillan rigingimun da suka faru sun yi nu ni da cewa Jihar Kwara ce abin ya fi yawa da kashi 21, saboda yanda aka rika yawan lalata dukiyoyi, sai Jihar Kaduna da ke biye da kashi 14, na yawan kashe-kashen da suke da alaka da siyasa.
A cewar sa, babban birnin tarayya ce ta uku da kashi 12, a sakamakon yawaitan jikkata al’umma daga jami’an ‘yan sanda.
Ya ce, tabbatar da gaskiya a kan sha’anin zabe mahimmin lamari ne, wanda bai kamata a takaita shi a kan yin zabe ta fuskacin gaskiya da adalci ba kadai.
“Abin ya wuce hakanan, ya yi nuni da samar da gaskiya, biyan diyya da bayar da ramako ga duk wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira daga laifukan da aka aikata a lokutan zaben.
A cewar Ojukwu, har sai an kama masu laifi an hukunta su, wanda in ba hakan ba aikata laifukan za su ci gaba ne a lokutan zaben.
Da yake magana a kan hakan, Mista Ayodele Ameen, babban daraktan hukumar ta (HURIDAC), cewa ya yi babbar manufar duk wata hukuma ta kare hakkin dan adam shi ne kare hakkin ‘yan kasa.
A cewar shi, rahoton ya nuna an sami jimillan mace-mace 174 a lokacin zaben 2019, wanda sam hakan bai dace ba.
Daganan sai ya yi kira ga ‘yan siyasa da su karfafa zaman lafiya a tsakanin su, su kuma tabbatar da rigingimu da kashe-kashe ba su lullube duk wani zabe ba.
Ameen ya ce, ya zama tilas a hukunta duk wadanda suka aikata laifuka, saboda a yi maganin irin wadannan kashe-kashen kar su maimaita kansu a 2023.

Exit mobile version