Nasir S Gwangwazo" />

…Ni Ba Dala Ba Ne Ballantana Ka Sa A Aljihu – Gwamna Wike Ga Ganduje

Mai magana da yawun gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, wato Simeon Nwakaudu, ya mayar da zazzafan martani ga gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa aniyarsa ta gurfanar da gwamnan jihar ta Ribas a gaban kuliya kan badakalar rushe masallaci da ya yi a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas kwanakin baya.

Nwakaudu ya bayyana hakan ne a wata kasida da ya aike wa manema labarai a jiya Lahadi, ya na mai cewa, “Gwamna Wike ba takardar Dala ba ne ballantana har idanun Ganduje ya rufe ya jefa shi a aljihu ba.” Wannan martani dai a na ganin cewa, a na ganin cewa, ba zai rasa nasaba da shaguben Ganduje kan badakalar wani hoton bidiyo da a ke zargin an ga gwamnan na Kano ya na amsar takardar kudi ta Dala ya na zurawa a aljihu ba.

“Hankalina ya gushe kan yadda har yanzu Gwamnan Jihar Kano, Abdulahi Umar Ganduje, ya na cigaba da kalaman da ba su dace ba a kan jihar Ribas. Har zuwa wannan lokaci Ganduje ya kasa gane cewa Gwamna Wike ba Dala ba ne ballantana idanunsa ya rufe ya antaya shi a cikin aljihu ba,” in ji Nwakaudu.

Daga nan sai mai magana da yawun Gwamna Wike ya karyata batun cewa an rushe wani masallaci a Fatakwal, ya na mai cewa, siyasa ce kawai ta janyo a ka lakaba wa gwamnan batun, wanda ba shi da tushe balle makama.

Exit mobile version