Connect with us

SIYASA

Ni Ce Mace Ta Farko Da Zan Sauya Tarihin Jihar Bauchi Ta Hanyar Zama Gwamna – Hajiya Baheejah (I)

Published

on

HAJIYA BAHEEJAH MAHMOOD ita ce mace guda daya tilau da ta fito a matsayin ‘yar takara Gwamnan Jihar  Bauchi a karkashin inuwar jam’iyyar ‘Yan Gwagwarmaya mai suna ACD (Action Congress of Democracts). cikin zantawar da ta yi da ‘yan jarida cikin har da Wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ta ce wannan lomacin na matane, tana mai shan alwashin kayar da mazan da suke kan mulki da masu nema, ta yi bayanin yadda take da muradin sabunta jihar Bauchi. Ga yadda hirar ta kasance:

Ga shi  kin yanki katin shiga Jam’iyyar ‘Yan Gwagwarmaya ta ACD ko me ya ba ki sha’awar shiga wannan jam’iyya?

Alhamdulillahi kowa ya san Nijeriya kasa ce mai dimbin jama’a kuma kasarmu cike take da nagartattun mutane, kuma kasar mu cike take da ‘yan siyasa jajirtattu wadanda hakan shi ya kawo mu ga yunkuri na samun dauwamar dimukradiyya a cikin kasarmu. kuma kasar mu mata mafi yawancin lokaci mukan fito ne mu yi zabe bayan an yi zabe an samu nasara sai kuma a barmu a baya. Hakan ta sanya ‘yan uwana mata suka ka ga cancantana da kuma mazaje da yawa da suka yaba da hazakata suka ce in zo in wuce gaba za su rufamini baya in Allah ya taimakemu ya bamu sa’a zan kasance ni ce zan lashe zaben gwamnan jihar Bauchi a 2019.

Dangane da yankan katin wannan jam’iyya ta ACD jam’iyyar masu gwagwarmayar ceto hakkin talaka mai al’amar kambi na shigeta ne, bayan dana yi zuzzurfan bincike, na bi diddigi da tarihi muka kuma yi shawarwari da kungiyoyin mata da sauran ‘yan uwa da aminai mutanen kirki da kuma dimbin magoya bayan mu, muka ga cewa akidodin wannan jam’iyya da manufofionta da tsare-tsarenta sun dace da manufar damu ke da ita yin gwagwarmaya don kwato wa talaka hakkinsa, da kare martanba da mutunci da muradun ‘yan Nijeriya musamman al’ummar jihar Bauchi da a yau suke cikin wani hali na ni-’ya-su, wato mawuyacin hali na rayuwa. Kun ga ita wannan jam’iyya an santa sananniyace da ta shahara wajen yin gwagwarmaya da yaki don ceto talaka da gina tattalin arzikin kasa, dalilina na kasancewa daga cikin wannan jam’iyyar.

 

Ta yaya kike ganin jam’iyyar ACD za ta iya karawa da sauran jam’iyyun adawa har kuma ta kada APC?

Nasara kam ai daga Allah take, kamar yadda na fadi akidodi da manufofin ACD ne suka sanya na shiga cikin jam’iyyar, amma a yau abin da ke gaban mu a kasar nan musamman ma a jihar Bauchi ya wuce batun jam’iyya mai ci ko ta adawa a ceton kai ne, yaya zamu ceci kanmu daga halin kunci, fatara, yunwa tsadar rayuwa, rashin ayyukan yi tsakanin matasa, yaya za mu kyautata ilimi mu samar da kiwon lafiya mai nagarta ta yaya zamu yi su sune a gabanmu. ban dauki kaina zan yi siyasa da gaba ba, kuma ina gani duk mai son ci gaban dimukradiyya ba zai so ya hana wani takara ba haka nima ba zan hana wani yin takara ba, kuma bana fada ko rashin jituwa da kowa a siyasa,  amma na  tabbatar wannan jam’iyya ita ce akidunta suka dace da warware matsalolin tattalin arzikin kasa da ciyar da al’ummarmu a gaba kun ji takenta ma ai ita wannan jam’iyyata ta ACD  Bankwana da Talauci.

 

Al’umma na yi wa wannan sabuwar Jam’iyyar taki kallon kamar baza ta iya fafatawa a tsakanin jam’iyyun PDP. APC da sauransu ba ta yakike da kwarin guiwa cewa za ki yi nasara?

A gaskiya yanzu siyasa fa ta canja ka ga ba kamar yadda da ake cewa sai wane da wane na ciki ba, a’a ai mutane sun waye su na duba in wane da wanen na ciki me suka maka kai talaka wajen kyautata rayuwarka da fitar da kai cikin halin kuncin rayuwa, don haka talaka ya waye zai dubi cancanta ne ya duba mutumin da kuma manufofin jam”iyar da za ta warware masa matsalolin da suka gallabeshi don haka irin wannan jam’iyya sune a kullum ke gwagwarmaya don yaki da zalunci, da rashin gaskiya da fatara da yunwa da cututtuka. Jam’iyya ce da ke neman a shimfida gaskiya da adalci a kyautata rayuwar al’umma na tabbara maka mafi yawan al’ummarmu sun hankalta sun amince damu kuma za su yi jam’iyyarmu.

 

A baya kina jam’iyyyar GPN sai ga shi kuma kin bullo da sabuwar jam’iyya ko me ya ke faruwa ne kam?

Duk cikin neman mafita ne da kuma kokarin da muke yi don mu samo hanyar da zamu ceto jihar mu ta hanyar bin ingantattun manufofi managarta, kuma ka san yawan jama’a, a’lummarmu sun ga cewa manufofin jam’iyyar ACD sune wadanda za su biya bukatun wadanda suke kada mana kuriunsu. Kamar yadda na fadi a 2019 masu zabe na lura da manufofin jam’iyya dana ‘yan takara da kuma cancantar mutum me yayi wa al’umma a baya?

 

To ke me kike tutiyar yi wa al’ummar da za su zabe ki don su?

Alhamdulillahi! Mun yi daidai gwargwado tun kafin Allah ya bamu damar yanda muka yi wa al’ummarmu ayyuka na gari, don tun farko mun samu nagartacciyar tarbiyya na gina alumma, da jin tausayin marasa galihu da mata da yara kuma Allah ya ba ni damar da na yi aiki a hukumar kula da marasa Galihu, ka ga mun yi kokarin samar da hjukuma da kuma hanyar da za a dogara da shi da ba za ta yanke ba a na kula dawa dasu mun samar musu da ilimi mai nagarta da hanyoyin kulawa da lafiya, mun yi musu wurin koyon sana’o’i irin na zamani mun gina musu cibiya kuma a kullum a gidana za ka samu yara marayu da marsa galihu fiye da 200 da suke cin abinci muka isar da taimakon da ya kamata mutsayawa mata wajen kulawa da lafiyarsu da kuma kula da marayunsu da aka rasu aka bar musu mun samawa dubban mata da matasa sana’o’in da za su Dogara da kansu ku san duk fadin jihar Bauchi ba lungu da sako da ayyukan alkhairi da muka yi bai riska ba. shi ya sa jin dadin haka nema ya sa kungiyoyin mata suka jajirce suka zage damtse cewa yanda na rikesu a baya tun da zabe ya zo ga dama ta samu in daure in tsaya  musu zasu zabeni, don in shugabanci Jihar nan domin a samu kyakykyawa kuma nagartacciyar hanyar ciyar da al’umma gaba.

Za mu ci gaba…
Advertisement

labarai